JODAH

26

by @sadisakhna


______👑 *JODA* 👑_____

             

Na 

*Sadi-sakhna*

Ƴar mutan Jama'are

THE TRIO OF TALES 
(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey) 


@sadisakhna on Arewapen
@SAKHNA03 On Wattpad
*** on Whatsapp


LITTAFI NA 1


👑*Warƙa ta (26)*👑


Amma bari nashiga na dubata tukunna,sannan ki cigaba da ɗoramin halinda ƴata take ciki.

Nidai kaina a sunkuye ina jinjina lamarin,kai lamarin Masu mulkinnan sai a barsu kawai. 

Itama Sunkia Madina shuru tayi tana kallonta,ta rasa da wanne baki zatayi mata magana kuma.

Tashi tayi fuuu tashiga inda gimbiya Asmah take bayan kaman daƙiƙa goma sai gata ta fito,kallon Sunkia madina tayi idonta yana tara hawaye.

"Yanzu madina haka ƴata ta koma,ko iya motsa jikinta batayi sai an motsata,ballantana kayi magana ta amsa maka,wanne irin ciwone kuka bari haka ya sameta"

"Haba Abidah miyasa bazakiyi tawakkali bane,na shaida miki abinda yafaru da ita,jininta ne ya hau kwanaki muka kaita akayi mata magani,bayan mundawo lafiya take tafiyar da lamarin ta ko kwana huɗu da suka wuce lafiyarta ƙalau. Haihuwar ce tazo da zubar jini wanda kinsan matsalace dake iya shafan kowa. Sannan da kike zancen Masu magani babu wanda baizo ya dubata ba yagagara tsaida jinin,kowa cewa yake bakin mahaifar ne ya buɗe,indai ba jaririn cikinta ne ya fita ba to bazai daina xuba ba,kuma anyi duk abinda za'a iya amma haihuwa taƙi tashi. Tun munayi mata Faten Hanta tanaci da ruwan itatuwa har yazamto ta gagara karba. Bani na haifi Asmah ba amma nima tamkar ƴa take a wajena abinda nayi mata ko ke idan zaki mata sai haka"

Da alama maganganun Sunkia madina sun fara tasiri akanta,hakan yasa tayi shuru da magana saidai har sannnan ruwan hawaye bai daina zuba a idanuwanta ba.

"Shikenan yanzu ke mai kike ganin zaki iya yimata na ceton rayuwarta,idan bakida abinda zaki iya inaso na ɗauki ƴata a yau mu juya Daular Ghana basai Gobe ba"

"Ranki ya daɗe akwai abinda zan jarraba idan an bani dama,
Bazata iya haihuwa da kanta ba,dan haka dole sai an taimaka mata, domin yin hakan kuma tana buƙatar Jini tuni na aika da samo mutum uku da zasu iya taimakawa dashi."

"Ke Joda dafari ni nayarda da maganinki amma wai mai kikecewa ne,jini ake buƙata daga wajen wani sai kace harka ta mayu?"

"Dakata sunkia Madina ke yarinya,indai har nemo masu bada jinin zai zama silar samun lafiyarta sai a nemo ai,Lafiyarta da haihuwar abinda yake cikinta ai yafi rayuwar Bayi guda uku"

"Ehh to hakane,ke Joda kina ganin in an zuƙi jinin bayi ukun zaisa tasamu lafiya?"

Mamaki furucinnnasu nayi wai wannan mutanen anya kuwa sunada ɗanɗanon tausayi akan mutanen dake karƙashinsu.

"Ahah ranku ya daɗe abin ba harkar maita bace kokuma cutarwa,sannan daga wajen mutum ɗaya ma ya isa,kawai zan gwadane nakalli wanda zai dace da nata jinin,idan an samu sai bada kaɗan ne wanda zai taimaka kada takara rasa jinin a yayin haihuwa hakan yayi sanadin ajalinta"

Dukkansu shuru sukayi kafin suce wani abu saiga Ungozama ta dawo da bayi uku maza a bayanta,ɗaya na riƙeda kaskon ruwan zafin danace a kawomin.

Ina ganin sun shigo na shiga ɗakin na ɗauko akwatina.Sannan na ɗebi jinin gimbiya Asmah kaɗan,wacce akayiwa wanka kaman yanda na faɗa,dakyar na samuma saboda yanda jinin jikinta ya ƙare.

"Inna kada ki gaji dani ina buƙatar ƙoƙo ƙanana guda uku kowanne ɗauke da amma na sanyi"

Zuwa akayi aka kawomin na buɗe,kitse ne na jikin ɗan adam aka narka shi ,sannan kwalbar tana riƙe ɗumi na daidai jikin ɗan adam, bayan anyi mana darasinne wanda mukayi a cikin littafin Al'tasrif na Alzahrawi wanda yake ƙunshe da ilimi na fiɗa da kuma Haihuwa,to anan na zaga na ɗauko nima naboye saboda mararin yin amfani dashi watarana. kowa yayi shuru a wajen ana jira aga mai zanyi. Allura na ɗauka na caka a yatsan Mutum na farko ,jini ya ɗiga a cikin ƙoƙo na farko haka na biyu harna uku. Sannnan na buɗe kwalbar dana ɗebo nata nabi kowanne ƙoƙo na ɗiga a gefen jinin. Bayan kaman daƙiƙa biyu na garwaya a hankali da wani tsinke,tamkar abin al'ajabi biyu daga cikin ƙoƙon jinin cikinsu ya haɗe waje ɗaya tamkar dama jini ɗaya aka ɗiga kawai,ɗayan kuma kowanne ya ware gefe guda duk da an garwayasu tare. 

Kallonsa nayi kafin nace masa.

"Kai zaka iya tafiya jininka bayyi daidai da nata ba,mungode da haɗin kanka,ku kuma sauran biyun idan bazaku damu ba inaso nasan ko akwai wata cuta da kuka tabayi mai tsanani?"

Wanda na sallama yatashi aka nuna masa hanya ya tafi,ɗaya daga cikinsu Yace yana fama da tari,sannan yanada ciwo a ƙafa wanda yaji a fagen yaƙi har yau bai warke ba. Ɗayan kuma mai suna Omar shine ya tabbatar mana Banda ciwuka irinna jiki bashida rashin lafiyar komai,saidai zafin jiki dayakeyi idan lokacinsa yazo sai kuma ya warke. Ajiyar zuciya na sauke kana na sallami na biyun shima na bar iya Omar.

Buɗe akwatin nawa nayi na fiddo wani zare dogo,an naɗeshi a cikin wata takarda,da ruwan jikin bishiya idan an sarrafashi ake haɗawa,in an tsoma zare a cikin ruwan daya bushe sai a zare zaren daga ciki. Hakan yana bada ƙofa a siririya gwargwadon kaurin zaren. Sannan akwai ɗan tsini na allura mai ƙofa a bakin. Ana amfani dashi domin cire ruwa a wanda suke fama da Kumburin ciki mai tara ruwa ko kuma zanye jini.
Saidai ni abinda zanyi amfani dashi akai shine jawo jini daga jikin wani na tara a kwalba,na kallah a littafin dana karanta wanda Guru almahdi yabani. A zahiri a nutse nakeyin komai amma cikin zuciyata a razane nake da cewar zan yi gwajin a ɗan adam mai rai hakanma kuma Sarauniyar Gobe ta babbar masarauta irin wannan. Idan aka samu matsala shin ya zanyi?.

A haka ina ƙiran sunan Allah a zuciyata na Soka bakin allurar a jijiyar dake kan gabar hannunsa na dama taciki. Jan iska nayi kaɗan ta bakin igiyar kafin na saka bakin ta ƙofar dake kan murfin kwalbar,ajiyar zuciya na sake dana kalli jinin yana taruwa a cikin kwalbar sannu a hankali, kowa sai fadin albarkacin bakinsa yakeyi da al'ajabin daya kalli yana faruwa a gabansa,inajin wata baiwa tana cewa wai tsafine,nidai bance komai ba dan ko kwana zanyi ina cewa kimiyya ce babu wanda zai yarda dani.

Samun waje nayi na zauna ina maida haki saboda gajiyar danayi da kuma yunwa da take addabata,an gaza wanda zai bani koda ƙwayar abinci tunda nazo,sudai burinsu na ceci rayuwar ƴar su babu ruwansu da nima ina buƙatar wani abun kaman sun samu dutse.

Ganin bazasu bani komai nasaka a cikina ba yasa na kalli Sunkia Madina wacce fuskarta take ɗauke da fara'ah,ganin nasara tana samuwa.....Haɗa ido mukayi da ita na nuna mata bakina ina kaiwa hannuna ciki.

"Yunwa nakeji ku taimakeni da wani abu naci,kafin jinin ya taru yanda zai isa,idan ba hakaba bazan iya yi mata taimakon daya dace ba"

"Au yi haƙuri ashe tunda taxo bamu bata komai ba,munata rayuwar Gimbiya,maza aje a kawo mata abinci mai kyau taci kaman yanda ta buƙata da sauri.
Nidai kallonsu nakeyi,zuwa lokacin babu wanda ya fita yayi sallah gashi magrib ya kawo kai,idan naci abincin ma sainayi sallah da ake bina dukka tukunna,halakar ta isa haka,kada na salwantar da lahirata akan ta ceton wacce batasan darajata.

Bayan naji abincin zuwa lokacin jinin ya isa yanda akeso saina zare sannan nace masa yatafi an gode,kuma na kara masa na Sauran abincin danaci,hadda nama a ciki nasan zai taimaka masa sosai,sai godiya yakeyi domin yanace dukka jininsa za'a kwashe rayuwarsa taxo ƙarshe,sai yaga sabanin haka ashe har harkokin rayuwarsa zai iya cigaba dayi.

Dabara nayi akan nafara gwada saka mata jinin,idan yana shiga sai nayi sallah. Gabana yana ɗar ɗar na isa inda take kwance baccin wuya ya ɗauketa kafin Ciwon yasake murɗo mata. Bakin allurar jikin igiyar na cire na saka wata dana ɗakko a cikin Kwalbar da suke cikin ruwa. 

Daidai kan babbar jijiyar hannunta na soka bakin igiyar mai ɗauke da allurar,da wani yana kusada ni sosai to da zaiji bugun da zuciyata takeyi,amma ko kaɗan hakan bai nuna a fuskata ba,saidai a zuciyata kam na ambaci sunan Allah sunfi dubu. 

Ɗaure bakin kwalbar nayi sosai na ɗaga sama tana kallon ƙasa sannan na bawa wata baiwa ta riƙe,to ya zasuyi aikinmu kenan. Zare nasaka na ɗaure hannunta da igiyar saboda karya goce danaji Jikin jijiyar hannunta ya nuna jinin yana shiga jikinta a hankali.

Tashi nayi tsaye ina kallonta tareda sauƙe doguwar ajiyar zuciya,tun kafin nayi magana suka jefomin tambayoyi a tare.

"Yaya yana shiga jikin ta,kenan jinin data rasa zai dawo jikinta ta haka"......Mahaifiyar ta ta ƙara da cewar.

"Ƴar nan ince dai bazata zama namiji ba kamarsa koh?"

"Ahah Babu abinda zai samu jinsinta,kawai matsalar shine kar da akwai cuta a cikin jininsa itama ya shafeta,amma yace bashida wata rashin lafiya muna fatan yakasance hakan Insha'allahu"

"Ameen amma indai har jininnan yashige jikinta kuma ya zauna daram harta tashi to lallai ƴar nan kin tashi ruwan kaina da fasaharki sannan da zurfin iliminki"

"To dukk ba wannan ba aiki yana gaba shine fitar da abinda ke cikinta, dalilin kenan da nayi kasadar saka mata jini,saboda bamu san in mun tabata mai zai faru ba,kafin jinin yabi jikinta inason na sauƙe sallolin da suke kaina"

"Amma idan kika barta kika tafi ba za'a samu matsala ba,ku gama mana sai a kaiki masauƙi ki huta"

"Ahah babu abinda zai faru,kafin mu fara aiki dole sai Jinin yabi jikinta,shikuma ba kaman ɗiba ba so ake yashiga da kaɗan kaɗan,dan haka har zan iya sauke haƙkin ubangijj dayake kaina,a wajensa muke neman nasara idan bamu gyara tsakanin mu dashi ba taya abinda mukeso zai samu"

Da haka na ɗinke bakinsu suka kaini wani ɗakin sannan suka bani ruwan da zanyi alwala.
Sallolin da suke kaina nayi Na kara da ƴan addu'o'i kafin na shafa a gurguje na fito. Duk abinda nakeyi Hammar yana raina,nasan idan nakoma akwai chakwakiya tsakanina dashi,ni kaina banyi tunanin abun har yakai haka ba. 

Tashi nayi Zan koma ɗakin da gimbiya Asmah take,wanda yana gefen na Sunkia madina. Turuss nayi a Harabar daxai kaini wajen ganin manyan mutane a tsatstssye,wasu matane guda biyu suka ƙaru bayan Sunkia madina da Mahaifiyar Asmah. Ɗayar tana kama da Gimbiya Meerah inaga mahaifiyartace,(Sunkia Haleema) sai kuma wata wacce tafi mai kama da gimbiya meeran amma kuma batakai Sunkia madina ba. (Sunkia Saleema) Durƙusawa nayi na gaishesu suka amsa,sai magana ake a wajen kan yadda naja jini a jikin wani na saka wa Gimbiya Asmah,ina jin Ɗaya matar mai kama da gimbiya Meerah tana cewa Kaskancine ace jinin bawa yana zagayawa a jikin Matar yarima mai jiran gado na daular Songhay guda. Daga yanda take magana da alama tafisu izza jiji dakai da kuma gadara,kuma nakula kamar dukka wajen Shakkarta sukeyi duk da ba itace babba ba. Sarauniya Abida ce tabada martanin cewar idan aka ce Ɗan masu ƴanci yabada jinin zai bada ne? ..Nidai ganin abinnnasu bamai ƙarewa bane yasa na tashi na nufi ɗakin. Dukkansu suka biyoni a baya,inaso nace musu su dakata amma banida wannan ikon,suɗin mutanene da saidai su bada umarni amma ba dai a basu ba koda kuwa basun shine abinda yadace. 

Neman taimakon Ungozamar nayi wanda xuwa yanzu komai nace da rawar jikinta takeyi,domin abubuwan danayi ba ƙaramin tafiya da tunanin ta yayi ba.

Sai kuma wata wacce na kula Baiwarta ce ta kusada ita. 

Tsayawa nayi akanta ina ƙallonta cikeda nazari,jinin ya kusa karewa a jikinta,Lafiyar fatarta har ya fara dawowa babu wannan ɗashewar. Ta farka idonta biyu tana rarrabashi,sannan har nishi takeyi mai ƙarfi dayake nuna mahaifarta yafara taimaka mata,yanzune muma lokacin dazamu taimaka mata. Danna min kan cikinta sukeyi itama tana nishin a tare,Askar na ɗauka na tsaga gefe da gefen ƙofar da Jinjirin zai fito,wata ƙara ta saka jini yafara fita daga wajen,da sauri na saka hannuna a gefe da gefen na jawo kan jaririn waje,na juya kafaɗarsa na jawoshi dukka ya fito duniya. Wata ajiyar Zuciya tasaki tana sake jikinta lokacin da tayi nishin ƙarshe mabiyyyar ta biyo baya itama. Babu alamar motsi a tattare da yarinyar amma bata ita nakeyi ba,Don miƙata nayi ga ungozama wacce mamakin yasakata daskarewa,ko kaɗan bata taba zaton abin da sauri za'a aiwatarshi haka ba,ni kuma nayi hakanne saboda kar mujata da nisa jini yazuba dayawa akoma gidan jiya. Kafafunta na buɗe ina kallon yankan danayi mata,danƙari yanzu ɗinkinsune abu na gaba,nasha ɗinke ciwo amma ban taba ɗinke nan wajen ba. Haka na saka farin tsumma mai kyau na goge jinin dayake zuba a wajen, Kuka ta saka na ciwon dataji,ɗa ya fita kenan tafara jin daɗin jikinta. Ido muka haɗa da ita tanamin kallon razani da biɗar son jin mai zanyi mata.

"Kiyi haƙuri domin na cire miki yarinyar na yankaki ta ƙasan,to yanzu dole za'a ɗinkene"

"Mee ɗinkewa kaman wata zani,waye yace ki yankani toh"

"Bazaki iya haihuwa da kanki ba,kokuma idan aka barki jini zai cigaba da zuba kuma zaki iya rasa karfin da kika samu yanzun,shiyasa na zabi hanyar datafi sauri domin ceton rayuwarku gaba ɗaya,duk da tanada wahala na zafin ɗinki da kuma na lokacin warkewa."

"Har kika tsaya kina mata bayani,idan babu matsala ɗinke mata mana ƴar nan har sai an bata haƙuri,da aka cire mata wannan lalurin cikinnata ai tayi samm barka tunda gashi harta samu bakin yin magana."

Haka kuwa akayi gardawan bayi mata masu karfi aka ƙira suka riƙeta na dinke wajen tass kaman na samu zani,saida na gama na shafa mata maganin dafin ƙarfe da kuma Farin kwalli saboda zubar jini,danaga jinin ya tsaya da zuba kamar yanda muke ɗinke masu raunika in suka dawo daga yaƙi kafin nayi ajiyar zuciya ta karshe. 

Tana ihun ba lallai tajini ba,dan haka Mahaifiyar ta nayiwa bayanin cewar ta dunga wanke wajen da ruwan dumi da gishiri akai akai. Matar da takemin kallon banza sai gashi ta dawo yimin godiya. Waini yau Joda a matsayin baiwa Sarauniyar daula guda takemin Godiya Allah mai bawa ɗaukaka ga wanda yaso. 


Sadi-sakhna ce ✍🏼

Comment 
Like 
Share 
Follow