Chapter 15
Tun da abin nan ya faru Ma'u ta dawo shiru, gabaɗaya ta daina neman magana da tsokanar da take yi, ko a makaranta ta daina shiga harkar kowa. Idan tana gida sai dai ta shige ɗaki ta tsurawa guri ɗaya ido, abin har ya fara damun Inna, ta same ta a ɗaki ta yi shiru kamar yadda ta saba. Zama ta yi a kusa da ita tana bin ta da kallo. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta ce "Ma'u".
Ɗago da kai ta yi ta kalli Inna, kafin ta ce "Na'am".
Cikin damuwa ta ce "Wai me yake damunki ne? Ina lura da dake tun da abin nan ya faru gabaɗaya yanayinki ya canza, kin kasa kwantar da hankalinki. Idan akwai wani abu ne ki sanar da ni ka da ki ɓoye mini Ma'u".
Idonta ne ya ciko da ƙwalla, jiki a sanyaye take kallon Inna, ta ce "Babu abin da yake damuna face yadda naga ana yi wa mutane kisan gilla a gabana. Inna a kan idona suka kashe Baba Saminu, sai kuma...." Ta kasa ƙarasa maganar sakamakon kukan da ya ƙwace mata. Inna ta ce "Sai kuma me? Ki ƙarasa maganar ina jinki". "Sai kuma rasuwar Aunty Halima, wallahi Inna mutuwar Aunty ta shige ni sosai". Shiru Inna ta yi tana bin ta da kallo. A hankali ta sauke numfashi ta ce "Ma'u, ina so ki yi haƙuri ki cire damuwar nan a ranki, ki sani duk abin da Allah ya ƙadda zai samu bawa babu makawa sai ya same shi, Allah ya ƙaddara Yaya Saminu da sauran jama'a ta hannun waɗannan azzaluman mutanen za su rasa ransu, ki yi haƙuri ki yi musu addu'a ita suke buƙata a yanzu su da Halima ba wannan kukan da kike zaman yi ba. Sannan ki ƙara godewa Allah da ya tsiratar dake a hannunsu, ki yi haƙuri kin ji Ma'una, na san ba abu ne da za ki manta da shi da wuri ba, amma ina so ki rage yawan damuwar nan ki saki jikinki kin ji, ba na jin daɗin yadda nake ganinki kullum a takure".
Jinjina mata kai Ma'u ta yi ba tare da ta ce mata ƙala ba, Inna ta shiga rarrashinta sai da taga ta daina kukan da take yi sannan ta bar ɗakin.
*****
Zuhura na kwance a falo saman 3seater tana dannar wayarta, Abbi ya shigo falon da sallama, ɗago da kanta ta yi ta ce "Sannu da zuwa Abbi".
Ya ce "Yawwa Zuhura, ya aka yi na ganki a nan ba ki tafi gurin aiki ba?". Yamutsa fuska ta yi, ta ce "Wallahi Abbi ni asibitin ce duk ta ishe ni".
Kallonta ya yi da mamaki, saboda ba ta taɓa cewa haka ba. Ya ce "Zuhura, asibitin ce ta ishe ki? To saboda me kika ce haka? Kar fa ki manta nine mamallakin asibitin, idan har ƴar da na haifa za ta yi fashin zuwa gurin aiki ba tare da wani ƙwaƙwaran dalili ba to don wasu sun yi hakan ai ba za a ga laifinsu ba". Tashi zaune ta yi, tana kallonsa ta ce "Abbi ni dai gajiya na yi da zuwa asibitin ne, sai na huta zan koma". Abbi ya sauke numfashi ya ce "Babu dalilin komai kika ƙi fita aiki ko Zuhura? Shikenan ya yi miki kyau, za ki gani a albashinki, ba zai yiwu don kina ƴata ba ki karya doka kuma a ƙyale ki, wannan ba adalci ba ne". Daga ya tashi ya bar mata falon. Ita ma tashi ta yi ta shige ɗakinta, tana shiga ta zauna saman gadonta, lambar Sudais ta kira. Yana zaune a office ɗinsa ya ga kiranta ya shigo, kamar ya share kiran sai kuma ya ɗaga ya kara a kunnensa ba tare da ya yi magana ba.
"Assalamu alaikum Habibi, barka da rana, ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya?".
Kamar wanda aka yi masa dole ya ce "Fine". Shiru ta yi tana kallon wayar ba tare da ta sake yin magana ba. Sudais ya yi gyaran murya ya ce "Idan ba ki da abin da faɗa ne zan kashe wayata". Cikin shagwaɓar da ba ta san ta iya ta ba ta ce "Da ma na kira ka domin in ji muryarka ko zan ji sanyi a raina".
"Me ya zafafa ran na ki da kike neman jin sanyi daga gare ni?" Sudais ya tambaya yana kunshe idonsa. Ta ce "Ba Abbi ne ba ya yi mini faɗa daga na ce ba zan je gurin aiki ba".
"To ke me ya sa ba ki je gurin aikin ba?". Ya tambaya. Cikin jin daɗin ya kulata yau ta ce "Ni asibitin ce duk ta ishe ni, ana yin wasu abubuwa ne da na kasa fahimtar su". Da sauri Sudais ya buɗe idonsa ya ce "Waɗanne irin abubuwa ne ake yi a asibitin da har zai sa ki ƙi zuwa? Kar fa ki manta mahaifinki ne ya buɗe wannan asibitin".
Zuhura ta ce "Eh na san da haka, amma Habibi wasu daga cikin likitocin ne na kasa fahimtar inda suka dosa. Lokaci da dama na sha jin suna yin wasu zantukan da na kasa fahimtar me suke nufi, haka kwana ki ma...." Sai kuma ta yi shiru, ta ce "Idan na huta zan koma".
Sudais ya sauke ajiyar zuciya yana murmushi kamar tana gabansa, ya ce "To shikenan, idan kika huta sai ki koma, amma duk lokacin da kika ji wani abu, ko kika ga abin da ba ki gamsu da shi ba, ki sanar da mahaifinki". Zaro ido waje ta yi ta ce "Rufa mini asiri, kar Abbi ya ce ba na son yin aikin ne shi ya sa na bijiro da haka". Ya ce "Haka ne kuma, to idan kika ga abin da ya shige miki duhu sai ki tuntuɓe da zancen, in sha Allah zan ba ki shawara ba tare da kowa ya sani ba, kin san ni ma fa na yi karatun nan, kawai ban mayar da hankali a kai ba ne, na shiga harkar business ɗina" cikin jin daɗi ta ce "To shikenan Habibi". Sosai Sudais ya saki jikinsa da ita suka yi hira, abin da bai taɓa yi mata ba. Zuhura ba ƙaramin daɗi ta ji ba, sun ɗauki lokaci suna hira kafin suka yi sallama.
****
Ana ta shirye-shiryen bikin Ilham da Saddik, ba don ranta ya na so ba take ɗaga wayarsa idan ya kira ta saboda tana gudun ɓacin ran Momy. Yau ya rage saura kwana ɗaya a ɗaura aurensu. Tun da safe ta gudu daga gidansu ta koma gurinsu Mammy tunda dama can ne za a ɗaura auren. Saboda Uncle ya ce "Ko da Yayansa baya raye a ƙofar gidansa za a ɗaura auren tunda iyalansa na nan" hakan ba ƙaramin ɓata ran Momy ya yi ba, ba don ranta ya so ba ta haƙura. Ko da Ilham ta ce "Za ta je gidan" ta so ta hana ta zuwa, sai da taga Uncle ya nuna ɓacin ransa sannan ta bar ta ta je. Ko da ta je gidan ɗaki suka shige ita da Zahra, cikin damuwa Ilham ta ce "Yanzu Zahra shikenan ina ji ina gani zan auri wanda ba na so?". Ta yi maganar tana fashewa da kuka. Rungume ta Zahra ta yi tana rarrashinta, tare da ba ta haƙuri. Da ƙyar ta samu ta daina kukan da take yi, haka ta kasance a gidan cikin rashin walwala. Misalin ƙarfe goma da rabi na dare, kwance take a ɗakin ta kafe idanunta sama kamar mai kallon wani abu, wani azababben zafi take jin zuciyarta na yi kamar ana kunna wuta a ciki, alamar shigowar saƙo ta ji a wayarta, a hankali ta sauke ajiyar zuciya, kamar ba za ta duba saƙon ba sai kuma ta ɗakko wayarta tana duba wa, tashi zaune ta yi da zaro tana kallon wayar, kusan minti biyar ta yi tana kallon saƙon tare da nazartarsa. Numfashi ta sauke, jiki a sanyaye ta fara mayar da reply, tana gama wa ta kwanta tare da lumshe idonta tana jin wani sanyi na ratsa zuciyarta.
Washe gari tunda safe gidansu Sudais ya fara cika da jama'a, saboda Mammy ta gayyato ƴan uwanta da wasu daga cikin ƙawayenta. Gidan Momy ma ya cika da jama'a sai shagali ake yi amma babu amarya a gidan, wanda hakan ba ƙaramin baƙanta ran Momy ya yi ba da jama'arta, nan suka fara surutu da ƙananun maganganu. Tare da ziga Momy ana ɗaura aure ta kira Ilham ta dawo gida.
Ilham kuwa tana ɗaki ban da kuka babu abin da take yi. Da ƙyar Zahra ta lallaɓa ta yi wanka ta shirya cikin wani rantsatsen les fari, ba ƙaramin kyau ta yi ba, Zahra sai koɗa ta take yi, nan ta fara yi musu hotuna da videos, Ilham ƙawarta Ummie ce ta zo gidan, saboda ƙin sanar da kowa zancen auren ta yi saboda ba ta so, Zahra ta gayyato ƙawayenta su uku, a cewar ta gara ko kaɗan ne a ga sun gayyaci jama'a gudun surutan mutane. Nan suka haɗu a ɗakin Zahra suka kunna kiɗa sai rawa suke yi. Ilham na zaune tana binsu da ido, abin duniya duk ya ishe ta.
Da misalin karfe goma sha biyu. Ƙofar gidansu Sudais ta cika maƙil da jama'a babu masoka tsintsiya, manyan attajiran ƴan siyasa da ƴan kasuwa duk sun hallara a gurin. Waliyan ango dana amarya sun haɗu, Sudais da Faruk sun sha kyau cikin farar shadda sai baza ƙamshi suke yi, kamar yadda addinin ya tanada, an fara gudanar da abubuwa cikin tsari da natsuwa. An biya sadaki ana ƙoƙarin ɗaura aure ne kira ya shigo wayar Alhaji Bashir sai dai har ta katse bai ɗaga ba, wani kiran ne ya sake shigowa, Dady ya dube shi ya ce "Ka ɗaga wayar mana sai faman kiranka ake yi". Wayar ya ciro daga cikin aljihunsa, ɗauka ya yi ya kara a kunnensa tare da yin sallama, shiru ya yi yana sauraren abin da ake faɗa a cikin wayar "Innalillahi wa inna ilaihim raji'un, wace irin magana ce wannan?". Da sauri Dady ya dube shi ya ce "Lafiya dai?". Shiru ya yi yana binsu da kallo, jiki a sanyaye ya sauke wayar daga kunnensa, kallon Dady ya yi, cikin tsananin jin kunya ya ce "Abokina, ina mai baƙin ciki da takaicin sanar da kai cewar auren nan ba zai yiwu ba, dole ne a haƙura a fasa shi". Gaban Dady ne ya buga da ƙarfi, Sudais bai san lokacin da ya ce "Saboda me za ka ce haka? Bayan an gama tara jama'a za a ce auren ba zai yiwu ba?". Alhaji Bashir ya ce "Sudais ku yi haƙuri, amma tabbas auren nan ba zai yiwu ba" ya mayar da dubansa ga Dady ya ce "Am so sorry abokina, ka yi haƙuri zan yi maka bayanin komai daga baya, ina ga a sallami jama'a kawai. Tunda an fasa auren" kasa magana Dady ya yi tsabar baƙin cikin da yake ji a cikin zuciyarsa. Jama'ar dake gurin waɗanda suka ji abin da yake faruwa kowa sai zare ido yake yana mamakin me dalilin da zai sa a fasa auren? "Ba za a fasa auren nan ba, kamar yadda aka tara jama'a, ba za a sallame su ba har sai an gudanar da ɗaurin auren nan. Uncle na amince ni a ɗaura auren da ni" Sudais ya yi maganar tare da ciro kuɗi daga aljihunsa ya ajiye a gurin. Wani irin sanyi ne ya ziyarci zuciyar Dady, nan take fuskarsa ta faɗaɗa da fara'a, Faruk ma murmushin yake yi. Ba tare da ɓata lokaci ba Dady ya karɓawa Sudais auren Ilham a gurin wani ɗan uwansu da yake gurin, ba tare da sauran jama'a sun fahimci mai yake faruwa ba aka ɗaura auren Ilham da Sudais. Sai dai bayan an ɗaura auren ne aka fara tambayar da ma shi ne zai aure ta ba ɗan gidan Alhaji Bashir ba?
Amanarcool
***