MARYAMA

Page 43

by @ummufadeela01

💫MARYAMA💫

43


Kwana biyu na yi a asibitin aka sallamoni sai dai maimakon mu koma gida, lodging daki siyama tayi a wani dan karamin hotel ta kaini can a cewarta kar azo nemana a gidansu. Ta sanar dani in three days masu zuwa zamu tafi Port Harcourt din tare da ita, ban musa mata ba amma ina jina So Stranded, ina jin tamkar gangar jikine kawai a tare da ni babu RUHI, ina jin like na bar wani part of me a wani waje daban ina ji..

Siyama tana tare da ni har wajen karfe bakwai na dare, gaba daya na rame na kara haske bau fuskata ta yi tsayi, ba karamin jiki na sha ba akan cire cikin nan da har yanzu na ke jin bai dace in cire shi ba, sai dai na kasa yi wa Siyama musu. 
Abincin da ta fita ta sayo mana ne gabanmu tana ci,amma ni na kasa kai ko da loma daya ne zuwa bakina sai faman tunanin da ya addabi zuciyata.

Kallon kasa kasa Siyama ta mata mai cike da harara kafun ta juya fuska zuwa kalar tausayi ta ce, "Ya kamata kici abinci dan ki samu lafiya Maryama, kinsan halin da kike ciki, so plsss don't stress your self da tunanin banza da wofi o....."

Karan da wayata ta yi ne ya sata tsaida maganar da take yi cike da kissa,banyi yunkurin daukar wayar ba dan nasan mutum daya ne mai kira dan shi kadai ke da lambar wayar. "Ki dau wayar mana kada ta tsinke".

Cewar Siyama tana kokarin dauko phone din saman gadon dake dakin, "Subhanallah, Sadeeq ne fa, ungo yi maza ki amsa kar ya yanke,".

Cewar ta har jikinta yana rawa ta makala min wayar a kunnena bayan ta yi picking.

Lumshe idanu na yi kana na kwantar da kaina a jikin gadon da nake zaune kasanshi ina jin zuciyata tana tsananta bugu,.

"Baby how you?" ya fada cike da kulawa, bude idanu na nayi ina kara gyara kwanciyata na ce "Alhamdulillah, and you?". "Alhamdulillah nima sai kewar wannan daddadar voice din naki. 

I miss you like hell baby, saura kadan a kaini asibiti tsabar yadda nake ta kiran sunanki a inda naje, gashi babu daman in kira wayarki dan ba'a kira a wajen, so whatsup? kema kinyi kewata?" ya fada cike da raha da alamar yana cikin nishadi.

"Uhmmm" kawai na ce ina kara rufe idanuna dan surutunshi ciwon kai ya ke kara min.

"Wait, are you okay Baby? Na ji muryarki wani iri haka, kina lafiya kuwa? Kodai wani abu ya sameki ne?" duk ya rikice sai tambayoyi yake watso mata.

Kukan dake kokarin fitowa na danne da karfin gaske ina saisaita kaina bansan yadda akayi ba na samu kaina da fadin, "Ba kaine ka daina kirana ba" kafin in kai karshe kawai kukan ya fashe na fara raira kuka na son rai, dama mai neman kuka ne aka harbe shi da kashin awaki.

Kuma rikicewa Sadeeq ya yi ya ce, "Oh no sorry Baby, ba haka bane. Ban daina kiranki ba kusan kullum sai na kira sunanki fiye da sau dari a rana, I miss you like crazy, yanzu ki daina zubar min wadannan hawayen naki masu daraja sai in fada maki abin da ya faru. Kukan ki yana daga min hankali plsss stop it baby".

Shiru na yi kamar yadda ya bukata sai ajiyar zuciya da nake ta saukewa...Sassauta murya ya yi kasa ya ce, "Yauwa my pretty ko kefa" Dum dum dum kirjina ke duka jin sunan da ya kirani dashi, ba yau ya fara kirana da pretty ba, amma sai naji na yau din ya tabani, ya tuna min da hamma jay, ko wane irin hali ya ke ciki? ko wanne hali su Innata ke ciki? 

Kara lumshe idanu na nayi dan wani irin yanayi na ke ji marar misaltuwa.firgigit na dawo da ga nisan tunanin da na tafi sakamakon kiran Sunana da yake yi.

"Uhummm ina jinka" na fada jin tambayar da yake min.

"Ba na ki kiranki bane, abin da ya faru shi ne mun samu wata yar matsala kadan ne a wajen sana'ar mu, kuma dole ni kadai ne zan iya tunkarar matsalar, so dole na tafi kuma a can babu network babu wifi. amma kuma tunaninki yana raina har naje na dawo and Alhamdulillah mun samu nasara."

Ajiyar zuciya na sauke kafun cikin taraddadi na ce, "Wanne irin aikine haka,?" Cikin murmushi ya ce, "Wai dama baki san aikina ba?,"kamar yana gani na na gyada mashi kai.

"Baby ni leburane,zaki iya mu'amala da dan dak'o? " ban fahimci inda maganarshi ta dosa ba,, dan haka bance komai ba, jin bance ba shima sai bai kara tambayar ba yaci gaba da magana. 

"Ina aikine da wata ma'aikata ta sarrafa danyen man fetur inda muke safararshi zuwa manyan kasashen turai da latin Amurka kamfanin kuma na hadin guiwa ne so akwai hannun jarin mutane da yawa a ciki. Matsalar da muka samu har na tafi kuwa shine jami'an sintiri na saman teku ne suka kama jirgin mu na dakon danyen man. Shi ya sa babu shiri na tafi dan inyi clearing abubuwan, I am telling you pretty, ba don Allah ya rufa mana asiri sun saki jirgin ba, da mutane da damane zasu samu karayan arziki a cikinmu ta dalilin hakan saboda babbar harka ce muka kulla ta biliyoyin daloli" .

"Ya salam!" na furta ina dafe goshi na, yayin da a gefe guda kuma Siyama ke ta wage baki kamar mai tallan closeup kasancewar a handsfree wayar take.

"Kin fahimci dalilina ai ko?" Sadeeq ya katse min shirun da na yi ta hanyar tambayata."Ehh na fahimta Allah ya bada sa'a ya kiyaye gaba kuma".

Sosai ya ji dadin addu'ar da nai masa cikin farin ciki ya ce," Ameen, my pretty. Dan nisawa ya yi sannan ya cigaba da magana, "Maryama na so ki hada ni da mahaifinki muyi magana kafun ki tafi school dan already admission naki ya fito, tafiyar nan da nayi ce ya dakatar da komai amma yanzu komai ya kammala ya kike ganin za'ayi?"

Ya fada da sigar tambaya. Ajiyar zuciya na sauke ina jin farin ciki a wani bangare na raina na ce, "Har yanzu baffana bai dawo ba kasan idan ya je can gida nijar yana jumawa sosai amma na tabbata idan ya dawo duk inda nake zai zo ya dubani tunda yana matukar kaunar in yi karatu".

"Ohk anyway, Allah ya tabbatar mana da alkhairi ki zama cikin shiri dan an fara daukan lectures a school din naku zan yanke kiran yanzu dan ina da meeting around 8pm."

"Nagode Allah ya bada sa'a" Ameen byeeee" ya fada da dan hanzari yana tsinke kiran.

Wayar na bi da kallo ina mamakin wanne irin meeting ne kuma sai cikin dare za'ayi shi haka? ganin bani da mai bani amsa yasa ni dage kafada kawai.

Mun tattauna da Siyama akan maganganun da muka yi da Sadeeq wanda duk ta ji abin da ya fada, har bayan wasu awanni biyu muna tare da ita kafun daga bisani ta tafi bayan ta tabbatar na ci abinci nasha magani na.

Koda Siyama ta tafi bacci kauracewa idanu na yayi, babu abin da nake sai faman sakawa da kwancewa, a gefe daya kuma ina kewar ahalina. Inajin tamkar ban kyauta ba idan na tafi na barsu, amma budurwar zuciyata sai kara ingiza ni take akan cewa da zaran na gama makaranta na yi kudi zasu yafe min. 

Wannan shine kuskure mafi muni da na aikata cikin rayuwata.

A haka na ke ta jinyar kaina da rayuwa cikin kadaici da takaici, har kwanakin da Siyama ta sanar min zamu tafi yazo.

Kwatsam na ganta da manya manyan akwatuna guda biyu shake da kaya, sai hand bag nata lokacin ko gari bai gama wayeba dan idar da sallar asuba ke nan ta shigo min.

A gaggauce na yi wanka na shirya cikin kayanta da duk wannan lokacin dasu nake amfani tunda babu kayana ko guda daya da na fito dashi, nikab ta bani na sanya itama ta sanya muka tafi tashar mota a kasan raina inaji tamkar in fasa wannan tafiyar tsabar yanda nake kewar ahalina.

Amma ina Allah ya riga da ya kaddara tafiyar tawa haka muka shiga mota ya tafi damu Yola, daga can taxi muka shiga ya kaimu YOLA INTERNATIONAL AIRPORT wannan shi ne karon farko da na fara zuwa airport jirgi kuwa dama tsakanina dashi sai hange daga sararain samaniya, amma duk da haka ban nuna kauyanci ba.
Ko sanda muka shiga ma ban wani tada hankali ba Lokacin da aka bada sanarwar sanya seatbelt Siyama tayi hanzarin janyo nawa ta makala min. Thank God waje daya muka zauna da ita.

Koda jirgin yazo tashi daga doron kasa, toshe kunnuwata na yi da karfi saura kadan in kwala ihu, amma na yi kokarin dannewa ban taba tsammanin haka tashin jirgi yake ba. Da haka jirgin ya daidaita kanshi a sararin subhana muka lula birnin porthacourt.

Tafiyar lokaci kadan ne muka kai
can. Ni dai ina cike da mamaki nasha jin masu zuwa yankin kudancin kasar nan na cewa wata jihar kwana da wuni ake ana tafiya amma gashi yanzu awa daya ya kawo mu.

Yana tsaye ya jingina da motarshi hannuwanshi duka biyu harde a kirjinsa sanye yake da wata yadi fara kal mai daukar ido har kana iya hango farar singlet dake jikinsa, dinkin half jumper da wando, kafafunshi sanye da bakar takalma cover, tsintsiyar hannunsa daure da agogo kirar hublot da zoben azurfa mai dan fadi a yatsarshi ta tsakiya, sai hular shi dake ajiye saman motar da alamar ya gaji da ita ne ya cire dan shan iska gashin kanshi ya sha gyara har zuwa kan sajensa da ya karawa bakin skin nashi wani sirrin kyau. 

Hannu daya yana rike da car keys dinsa, duk da hannun suna harde a kirjinsa, hakan bai hanashi karkada keys din ba idanunshi kyam akan jirgin da yayi landing yanzu daga Adamawa...Sadeeq kenan MAN kamar yadda na ji Mom da Abbun shi suna kiranshi da. 
Ya kwashe wajen mintuna goma tsaye wajen yana jiran isowar su.

Cikin nutsuwa muke saukowa daga kafar jirgin ina gaba Siyama na bi na a baya, tun ina saukowa na hango shi sai na ga ya kara yin kyau hade da cikar haiba da kwarjini, komai ya ji zam. Haka kawai na samu kaina da kasa daina kallonsa. Ta gefen Sadeeq kuwa kure ta ya yi da ido yana tasbihi ga Allahn da ya hallici wannan kyakkyawar baiwar tashi, fuska dauke da murmushi ya dago daga jinginar da yayi yana mana sannu da zuwa ganin mun iso daf da shi.

"Barka da hutawa yallabai" Siyama ta fada cike da yanga da kwarkwasa.

"Barka dai Madam fatan kun iso lafiya?" Ya ba Siyama amsa ba tare da ya kalli ko gefen da ta ke ba. Idanunshi kyam a kaina.

Sosai hakan ya ya ba Siyama haushi amma sai ta dake kamar ba komai, "Pretty hope you enjoy the trip?" Gyada mishi kai na yi ina rufe fuskata da tafin hannuna duka biyu dariya ya yi wannan karon ya juyo yana kallon Siyama ya ce, "Ji wannan bafullatanar wai ni zata yiwa kunya, nima fulani ne fa, ko don kin ganni ba'ki?".

Ya fada yana leko fuskata, dariya itama ta yi ta ce, "Ahto da alama bata sani ba kam."

Wani daga cikin ma'aikatan airport din ya kira ya zuba mana kayanmu a bayan mota sannan ya bude gaban mota yana kallona hadi da kashe min ido daya ya ce, "Bismillah Princess".

Banyi musu ba na shiga ina dan mamakin saukin kanshi, driver seat ya zaga ya shiga yana cewa Siyama ta shiga baya. Tabbas ran Siyama ya baci matuka dan har ta gaza boye hakan kwafa tayi ta bude bayan motar ta shige ya tada motar suka bar filin jirgin.

Maryama dai ta juya kai sai kallon garin patakot ta keyi, ba karya garin ya hadu iya haduwa, tabbas sunfi arewa ci gaba ta bangare daban daban. Wani hadadden anguwa suka shigo wanda yafi kama da estate kasancewar gabadaya gidajen anguwar iri daya ne, shiru babu motsin mutane ko kadan awajen kamar ba anguwannin bil adama ba sai shuke shuke masu ban sha'awa da suka kawata kowanne kofar gida kana kukan tsuntsaye jefi jefi da mutum ke jiyowa sai once in a while kaji wucewar mota shuuuuuuuu, Sadeeq dake driving lokaci lokaci yake dagowa ya kalli Maryama ya saki murmushi sai dai baice komai ba, da haka suka iso bakin wani wawakeken get baka wuluk mai adon golden, horn ya danna da sauri mai gadi ya fito ya leka sannan ya koma hadi da wangale get din.

Saura kadan numfashin Maryama ya bar jikinta lokacin da tayi arba da katafaren ginin bene hawa daya dake cikin gidan, itama Siyama wani irin zaro ido ta yi a ranta tana fadin "Allah dai ya kai damo ga harawa".

Cike da kwarewa Sadeeq ya ci gaba da cusa hancin motar a cikin gidan har zuwa parking space inda ya daidaita motar da sauran motoci guda uku gallah gallah dake pake gefe guda tamkar ba'a hawansu tsabar yadda suke daukan ido.

Saukowa na yi bayan ya bude min gefen da nake, da sauri siyama ma ta sauko dan taga har ya fara tafiya, taku uku Sadeeq ya yi ya tsaya yana tura hannayenshi cikin aljihun rigarshi yace, 

"So, this is my house," da rawar baki siyama ta ce tana washe hakora, "Masha Allah, gidan yayi kyau matuka gaya".

Karkata kai yayi gefen da nake yana yin low da muryarshi ya ce, "Pretty this is our house, ya kika ganshi? Ya miki?."

Tabbas ban taba shiga gidan da ya min kyau ya kawatu kamar wannan ba tunda nake a tsahon rayuwata, ba shakka Siyama tana kaunata ba don itaba da babu yadda za'ayi in sanya kafata a irin wadannan katafaren gidajen,.

"Murmushi na yi na ce, "Masha Allah, gidanka ya yi kyau sosai, ban taba ganin gidan da ya min kyau kamar wannan ba".

Kara matsowa ya yi kadan har inajin numfashinsa ya ce, "Gidanmu dai baby, a nan zamu rain.....ko me ya tuna kuma sai yayi shiru yana dan murmushi kadan yace, "Duk kyan gidan nan kin fishi kyau Maryama".

Wani irin sanyi naji yana ratsani daga tsakar kaina har zuwa tafin kafata, Hamma Jay ne ya fado min a raina wanan irin maganganunshi ne sak, ko ina yake yanzu? mai yake yi? su innarmu sun nemeni? Allah masani.

Da wannan tunani muka iso entrance na shiga palon, dama duk maganar da muke muna tafiya ne, makulli ya sa ya bude kofar gaba daya muka shiga mai gadinshi na biye damu a baya da tarin akwatunan da ya dauko mana.

Allahu Akbar, tabbas manyan kasarmu suna jin dadi, wato iya haduwa wannan palon ya hadu tsayawa bayyana haduwarshi ma bata lokaci ne, kujeru ne na alfarma samfurin turkey set biyu a palon brown and milk colour, da sauran abubuwa da ake samu a palon masu kudi kamar su tv da dining area,, Sai wasu kofofi guda hudu, biyu daga ciki bedrooms ne daya kitchen daya kuma bathroom na palo ,sai kafan bene wanda zai kai ka upstair da komai nashi irin na kasa ne sai dan abin da baza'a rasa ba.

Tsayawa kawai na yi baki galala ina karewa falon kallo, yanzu duk wannan mutum daya ke rayuwa a cikinsa? Kai arziki yayi a rayuwa. Ku karaso mana ya fada yana kallon yanda gaba daya mukayi mutuwar tsaye daga ni har Siyama da ta saba ganin gidajen masu kudi dinma.Mai gadi dai ya shige da kayanmu ciki inda sadeeq ya nuna masa daya daga cikin dakuna biyun dake kasa ya shigar da kayan....

Washe garin ranar da mukaje fatakot muka fara shiga makaranta da nufin fara registration Alhamdulillahi komai yana tafiya yadda ya kamata dan Sadeeq ya yi amfani da lokacinsa da kuma aljihunsa akaina cikin sati daya mun kammala komai, a cikin satin nan kuwa babu wani wajen shakatawa da manyan malls malls da bamu sani ba a patakot ni da Siyama sosai yake kaimu outing muci abinda muke so musha abin da muke so, siyayyar makaranta kuwa ya kashe min kusan 1million da ya ke na zabi zaman hostel ne akan gidansa shima bai musa min ba dan yasan zaman mu waje daya hatsarine. Bangaren suturu kuwa ba'a cewa komai dan ya sai min sun kai kala dari babu kalan da babu.

Yauma kamar kullum ina zaune dakin da yake mallakinmu nida siyama tunda muka zo a kasa.

Parking nake yi dan gobe nake sa ran komawa makaranta da zama tunda komai ya kammala, har na fara daukan lectures. Sanye nake da wasu riga da siket english wears yellow cikin kayan da Sadeeq ya sai min kaina babu dankwali sai dogon gashina da yake samun kula na musamman a yan kwanakin nan, Siyama na kwance gefen gadon sai bacci take sharawa itama zata wuce Adamawa in two days masu zuwa, door bell na palo na ji an danna da karfin gaske, hakan ya bani mamaki matuka dan tun da na zo gidan ban taba ganin wani yazo ba. Jin ana ta dannawa ne ya sani mikewa dan ganin waye wannan tunda nasan Mai gidan yana nan bai fita ba.

Sadeeq yana zaune palon sanye da armless riga da wando three quarter laptop ne gabanshi yana operating sai wasu takardu dake gefe da alamar aiki mai muhimmanci ya ke yi, door bell ya ji an taba, cike da mamaki ya mike dan ganin waye ya zo mashi gida babu notice, lekawa ya yi ta jikin kofar, wani irin sauti kirjinsa ya bada dammm hango Mommy tsaye kikam tamkar soja babu alamar murmushi a fuskanta da wata a gefenta da ko ba'a fada ba yasan khadija ce. danna bell din aka cigaba da yi ganin babu alamar za'a bude musu ne yasa Mommy fara bugun kofar da hannu. Sadeeq da a take wani zufa ya karyo masa kamar yayi wanka a kogi kana jikinsa yana dan rawa kadan kadan ya daura hannu saman handle din kofar ya fara budewa, hakan kuwa ya yi daidai da fitowar Maryama daga dakin kanta babu ko dankwali.......