SILAR HALLACI

Page 1

by @jamilaumarjanafty

*SILAR  HALLACI...*!

*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*

_Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai_

*REPOSTING NE, BA MU CANZA HARAFI KO ƊAYA A CIKIN LABARIN BA*

*HIJABS CORNER BY JANAFTY*

*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design,  muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*


        *🅿️1*

Shimfiɗa.

Shekara ta alif dubu biyu da goma
2010

*BIRNIN KEBBI..*
_jega local goverment_

"Cikin wata Anguwa da ake kira Sabon gari dake cikin Babban garin jega local goverment dake Cikin Babbar Jahar nan ta Birnin kebbi,acikin Shekaran ta Dubu biyu da goma.

Wani matashin gida nagani ginin Kasa,Wanda akama Shafen Fentin Farar kasa Daga gaban Gidan zuwa baya,gidan bashi da girma Sosai Daga yanayinsa zaka Fahimci mazauna gida dai suna Fama da Rayuwa sai dai godiyar Allah.

Wata yar Tsohuwa ce mai Akallah Shekaru 60 aduniya,Farace ammh ba Farin nan na Sosai ba yadda Duk jikinta yayi zaka Fahimci Tsufanta yayi Saurin bayyana sai kace yar Shekara 80 Saboda Wahala Zaune take atabarma a Kofar dakinta wanda keda labulen kaba kulle kullenta ne Data saba na yau da kullum agabanta irin su kuka,kubewa,Daddawa,citta kanunfari,komai dai na kayan mata na cikin gida,tsohuwa Bara"atu wacce Jikanta ke Kira Kaka tana saidawa Domin Rufama kanta asiri ita da marayan Jikanta wanda Iyayensa suka mutu suka barta dashi kwara daya Tal.

Ta Dukufa tana faman Kulle kullenta Lokaci daya tana Rera wakarta Ahhayye sama Ruwa...Ayyahhhe sama Ruwa kasa. Ruwa..Mata mata..,take fada Lokaci daya kuma takoma tana Fadin "Mata akama Sana"a mata Macen da bata Sana"a Saunace Lale lale maraba da lale Saunace.."

Take Fadi lokaci daya tana Bantalan Goronta datake lalubowa cikin Katon wani Yadi wanda aka mata katon Lalita nan take Zuba komai nata ciki kuma koda yaushe yana kugunta ko barci take Dashi takeyi Kaka bata da yarda ko kadan balle Sha"ani na kudi bata da Wasa kaka akwai neman na kanta.

AHMED yana daga cikin karamin Dakinsa Dake kallon na Kaka Zaune yake bisa wata yaloliyar katifarsa mai kama da Tabarma Dakin babu ko leda ammh yana Share Tsab Daga gefe sai Tarin Littafan karatun boko dana Arabi,Daga yammah kuma Wata jakace karama wanda kayansa ke ciki  sai gefe kuma Takalmansa ne Wadanda sukaji jiki guda uku ke Da mazauni awajen.

Karatu yake ammh Sam Hayaniyar kaka ya hanashi Sukuni Gabadaya Dagulamai Lissafi take kamar wata budurwa yar Shekara goma ta Zauna tana Wani Rera waka Tsaki yaja kafin ya mike Lokaci daya yana kwafa Kansa ya Dafe saboda Atsarinshi bayason Hayaniya gashi ita kuma kaka yar Hayaniya ce yafi kowa sanin yana mata mgana Sai dai karshenta ya bar gida nan in kaka ta Fara mita har gobe da Safe ajiyar zuciya kawai ya Sauke  lokaci daya ya karisa kofar Dakinsa yana kokarin Sakin Labulen kaban dake Daure asama.

Kaka ta dago ido tana kallonshi Baki Ta tabe kafin tace"Kai dai Wlh Ahmadu kaji Haushi ko Mace bata kai ga gulma da Tsegumi ba.."yana jinta ya mata banza sai ma Sauke Labulen kaban dayayi ya koma ciki da Harara ta bishi tana Fadin"wlh naso kayi mgana daka ga Tijarata Sabuwa acikin gida nan Dan Kusan Uwa...Yaron nam sam Bansan meke damunsa ba na Lura matattaciyar Zuciyar Uwarsa Zaliha ya gano domin dai  Sama"ila irina ne akwai Zuciyar neman na kai..."Tafada Lokaci daya tana saka gora abakinta ta gatsa yana jinta ammh ko Niyyar Fitowa baidashi saboda Sanin Hallin kaka ba bakon Abu bane Shekaru fin Ashirin yana Tare da ita yafi kowa sanin Halinta Shigen son ta Tara kudi ko ta halin kakane Mganar neman nakai bazai karyataba Kaka akwai zafin nema Domin dashi take ci dasu tasha dasu kuma acikin neman natane ma Ya samu ya Shiga Kolejin Horas da malamai ta Burnin kebbi Wato Federal Collage of Education Birnin Kebbi.

"Kaka..Wayyo Kaka na Shiga uku..."Wata Budurwan yarinya ta Fada wacce ta Fado Gidan kamar Daga sama a kallah bazata Haura Shekara 19 aduniya ba Ammh Daga yanayinta zaka Fahimci ta Fito Daga gidan Jin Dadin,Tundaga kayan alfarma dake jikinta na wata Doguwar Rigar kirar Armani wanda ta yafo karamin mayafin kayan Doguwa ce mai matsaikacin jiki,Tana da kyau daidai Gwargwardo,Zabura kaka tayi tana Binta da kallo lokaci Daya tana Fadin"Ke SAMIHA lafiyanki kuwa kika Fado man gidan kanki Tsaye ba Sallama ko wannan Tsohon naku ne ya sheka wanda bai fittar da Zakka balle Hakkin Makota ka.."?

Tafada tana Jifan Samihan da wani kallon Raini da Kuma mamaki,Samiha ta Zube Bisa gwiwoyinta tana kuka Hawaye na Zubomata,bata damu da kalaman Kaka saboda bawai yau ne na Farko data ke fadi agaban idonta cewa Mahaifinta bashi da kirki baya zakka balle Fitar da Hakkin Makota,bata damu dataji Haushi ko kar kartaji itadai sai ta Fada ko za"a mutu ne, cikin karyar Da murya Samiha tace"Na shiga uku kaka..ina Ahmed...Yana ina wajensa nazo..?

Kaka tace"Ikon Allah lafiya toh kiketa Rafzan kuka.? Kai Ahmadu Fito ga Budurwanka yargidan masu kudi daga gida sai gida tazo Fito maza kajata ku Fitarmin Daga gida,bazaku min Shanshancin da kuka saba ba acikin Gida.."Tafada kai Tsaye tana kara Taunar goranta,Ahmed Dake daki da Sauri ya Fito Jin Muryan Samiha tana kiranshi da Farko Hargowan kaka kawai yaji Shiyasa ya Shareta yaciga da karatunsa jin muryan Samiha ne yasa ya Fito da Sauri yana gyara zaman Rigar Shirt din Dake Jikinsa.

Ahmed Dogon Namiji ne karkkarfa mai cikar Zati da Haiba ba Fari bane Sosai Sai dai yana da kala mai kyau,Doguwar Fuska gareshi mai Dauke da Dogon Hancinsa da karamin Bakinsa Kwarjinsa da Haibansa Shike karamai kima a idon Mutane,uwa uba kuma kwanya da baiwar da Allah yayi mai Duk da ya kasance Yafito daga Gidan da Babu Arziki sai Rufin Asirin Allah,akallah Shekarunsa na Haihuwa Ashirin da biyar alokacin.

Tana ganinshi tatashi ta nufeshi Cikin Tashin Hankali ya Tareta yana Fadin"Samiha lafiya kuwa..?meke faruwa kike kuka..?

Gabansa kawai ta Zube tana kara Sakin Kuka Lokaci daya tana Fadin"Ahmed Abba ya kasheni...Wai Aure zai min nan da Wata daya da wani abokin kasuwancinshi Dake Jahar kano..."Tafada Lokaci daya Hawaye suna kara wanke mata Fuska.

Ahmed dayaji Zencen kamar Sauran aradu ya Zaro ido Lokaci Daya yana Fadin"Aure kuma Samiha...? Wani irin mgana ce wannan..? Ammh wasa kike min ko..?yafada cikin Tashin Hankali da Dimuwa Cikin Fitar Hawaye ta Girgiza kai tana Fadin"Ahmed na taba maka irin wannan Wasan..?kamar sakarai Haka ya Girgiza mata kai Cikin Kuka tace"Da gaske nake Ahmed Abba zai Rabani da kai yace wai bazai baka Aurena ba saboda baka da wata sana"ar da zaka iya Rikeni,bazai yarda na Aure ka ba..yariga yabama Alhaji Bashir wambai ni amatsayin mata Har Waliyaina sun karbi Sadakina.."

Takarishe fada tana kara saka kuka Tana Durkushewa nan gabanshi Shima cikin Wani Fitan Hayyaci da Daukewar Numfashi,ya Sulale agaban Samiha idanuwansa sun kada sunyi Jajir Saboda Damuwa Lokaci daya jijiyoyin kansa suka Tashi kamar wanda ya Shekara yana Ciwo cikin Wani irin murya yace"Bazai bani ke ba Samiha...?

Yake fada kamar yana koyon mgana,Kaka dake gefe tagama jin Komai ta saki Tsaki lokaci daya tana mikewa tare da Fadin"Eh yace bazai baka ba saboda baka da Sana"ar da zaka rike mishi y'a ko karya yayi kana da Abunyi da zaka Dauko Aurene yanzu Ahmadu..? Tafada tana tsayawa kikam agabanshi Cikin Fitan Hayyaci Ahmed ya dago yana kallon Kaka da idanuwansa da suke neman Zubar da kwallah.

Shewa kaka tayi Lokaci daya tana Fadin"Mezan gani haka ni Bara"atu huwai..Kuka zakayi koma kafara ne don mai garinku..? Tafada harda Leken Fuskarsa Saurin kauda kai yayi Saboda Takaichin kaka itako yar Dariya tayi tana Fadin"Nifa mahaifinki baita burgeni ba Samiha ba sai yau daya bada Auranki ga wani ba Ahmadu ba..?

Gabadaya Daga Samiha har Ahmed lokaci Daya suka Dago Suna kallon Kaka wacce ta gyara Tsayuwa tana Fadin"yo zencen gaskiya mana...Tsaya ma kaji Ahmadu ba karya ba Boye boye akwai Ranar Kiyama ni ce nan na wanke kafa naje har gidansu Samiha na samu mahaifinta nace in ya samu mai son yarshi Tsakani ga Allah gwara ya lallaba ya mikata Domin kai dai ba Auranta zakayi ba,baka da Sana"ar komai baka Tara ba kuma baka nema ba,kuma baka ijiye mai baka ba,Waka ke dashi banda ni ni kuma mai na Tara,wannan Kawun naka kake Takama shima dayatafi chan kanon neman kudin kaga ya samo..? Shima fama yake da kanshi balle har ya Dauki Dawainiyarka ina kaga Kudin Aurenta ehe Ahmadu banda Dorama kai Wahala muna Fama da kanmu,kaje ka kwaso mana Aure naci dakai kuma na koma ina ci da ita..?Wlh baka isa ba gwara kai in na wahala dakai jikana ne itafa..? Indama ace Ubanta nada Hannun bayarwa ne ammh Bai dashi kullum sai dai ya Wuce a katuwar Mota yana kwance abayan Mota Direban na Jansa yana mana kallon Hadarin Kaji,kai kuma kana nan kana Hure ma yarinyarsu kunnen da karyanku na ya'yan zamani,shiyasa na yanke Shawaran Zuwa na Sanar dashi gaskiyan mgana kada Daga baya a sako Sunana cikin Mayaudara ina Dalili haka kawai.."

Take fada tana wani Dauke kai Daga Samiha har Ahmad wani Bakinciki da Takaichin kaka ne ya Tikasu,cikin Wani Fushi Ahmed ya mike Lokaci daya yana Fadin"Gaskiya kaka bazan Boye miki kin cika azabarbi da Fadi ba"a tambayeki ba ina Ruwanki da Soyayyata da Samiha had'a na aike kine wai..'? Harara ta sakarmai tana Fadin"Bansani ba Hudu Dufa dufa..."Tafada cikin Igilanci Wani Tsaki yaja mai Tsawo yana Fadin"Nidai Daga yau zan miki iyaka  da Shiga Harkata Kaka...Bana so...Karki kuma min irin haka Tunda ban aikeki ba.."yafada cikin Nuna bacin Ran dayake ciki Baya taja Tana kallonsa lokaci daya tana Fadin"Oho dai...babu yadda za"ayi Dani Hajiya Bara"atu nake yaro Tun Ubanka baisan zai zo Duniya ba na keta Hazo..muda muka ga shekaranjiya muka ga jiya kuma Muna Shirin ganin Yau da gobe da yardan Allah."Tafada harda Rike kugu ko kallonta baiyi ba,lokaci daya ya Riko Hannun Samiha yana Fadin"Tashi mu Shiga Daki Same...Muyi mganar achan.."yafada yana Mikar da ita Tsaye cikin Ajiyar zuciya ta mike Ta bishi Suna kokarin Shiga Dakin nashi Kaka ta tare bakin Kofar Tana Fadin"Kan Bala"i...Na Rantse Harga Allah Ahmadu kayi kadan kashiga Dakin nan da Ita kaji ma Na Rantse Tun Wuri ka sakar musu hannun ya kafin na Zumduma maka ihun kwarto..Wa"izabullah kai ko kunya bakaji Matar aure fa Wacce aka karbi Sadakinta yanzu Fisabillah Ahmadu mene Amfanin Rashin ta ido irin naka...'?

tafada tana wani kara babbake Kofar Ahmed kamar ya Fasa ihu haka kawai ya Tsaya yana Bin kaka da Ido cike da wani Takaichi mai Hade da Bakinciki,bai mata mgana ba Illah Takalminsa Dake Kofar Dakin ya zura lokaci daya yana kara Riko Hannun Samiha Dayayi kawai suka kama Hanyar Fita Daga gidan Baki Bude kaka ke kwalamai kira tana Fadin

"kai Ahmadu...Kai Ahmadu ina zaka kuma..? Au fitan kayi.? Na shiga Tara ba uku ba Ni Bara"atu Jikar Audi bassakwace...'Take fada tana Bin Ahmadu da kallo Wanda suka Fice Daga gidan,Haba kaka ta Rike ta Dade Tsaye kafin ta saki kwafa tana Fadin"Oho dai nadai ji Dadi ina Dalili muna fama da kanmu ka karomana aiki yadda ta saba da Kwanciyar sama Sulbi kasa Sulbi ai sai tazo ta raina mana arziki muna Shan koko da kosai da Safe tace ita Renon bota ne kuma Wannan Tsohon nata na tabatta biyar bazai Dinga Taimakomana Dashi ba yo haka d'ai Chan gasu gada duk dai Abunka Haka zaka Hakura tayi Aurenta Uban kowama ya Huta kai kuma Dan Buhu da Rabi zaka zo ka sameni Har inda nake ne karyan tsiya kake yaro an mai gata ammh shi baya gani Sakaran yaro kawai mara Tunani.."

Haka kaka keta Sababinta Ita kadai kan Tabarman Data tashi ta koma ta Zauna tacigaba da Kullen kullenta tana ta Mitar Ahmadun ita kadai Lokaci daya tana kwafa,Shikuwa Ahmed suna Fita bai Dire da Samiha ko"ina ba sai wani Koridin layin da zai Fitar dakai wani layi saboda kauda Idanuwan Mutane,Cak ya tsaya gabanta lokaci daya ya sakarmata idanuwansa yana kallonta kafin yace"Samiha wat d is Solution now..Kaka ta riga tagama Dagulama komai Wlh kai wannan Tsohuwar Tana gamawa dani wlh.."yake fada cikin Takaichi kamar Zai Fashe da kuka.

Hannayensa Samiha ta riko Lokaci daya tana Fadin"Ahmed bani da wata mafita sai guda daya..Abba in yayi mgana bazai taba chanzawa ba balle kuma ga Abunda kaka taje ta fadamai nasan Duk da Haka yasa ya yanke wannan Hukunci.."Idanuwansa yana kanta Cikin Fitan hayyaci yace"Wata mafitace Samiha..Yi sauri ki Fadamin naji kin Tabbata bazan Jura rasaki ba.."Idanuwansu na cikin na juna tace"Mu gudu kawai Ahmed,muje mu samu wani garimuyi aurenmu mu zauna,achan har zuwa Tsawon Wani Lokaci sai mu dawo Lokaci Abba bashi da yarda zaiyi Dole ya Hakura..."

Baya yaja yana Fadin"Mu gudu fa kikace Samiha..?U are not Serious Samiha bazan Taba bin Wannan Shawaran naki ba in ke kina da kuruciya da yarinta ni nasan Ciwon kaina in na gudu dake dame zan Rike ki..? Haba Samiha Ki duba dakyau ki gani wannan ba Mafita bace.."Kuka ta Fashemai dashi Lokaci daya tana Fadin"A"a karkace haka Ahmed...Wannan itace kadai mafitan da zamu Mallaki juna Duka mafarkanmu akan juna su Tabbata..."girgiza kai kawai yake yi lokaci daya yana Fadin"Bazai Taba yuyu ba Samiha..Rayuwarki datawa ba iri Daya bace...Gaskiyan kakane Bani da Abunda zan iya Auranki na Rike ki Samiha! Ni marayane Daga bangarem Uwa dana Uba kuma bawasu Cikakkun Dangi masu Asali na taso hannun kaka itace Dukkan Wahalata Samiha Duka Burin kaka yana kaina ne bata da kowa kamar yadda Nima bani dashi Daga junanmu sai Allah sai kuma kawu maude wanda shima kina gani bashi dashi wajen shekara uku kenan da Tafiyarshi kano shida iyalansa neman kudi har yau bawani labarinsa su kadai nake Dashi ki Duba saboda karatuna ba sana"ar da kaka batayi ba  Saboda Ta inganta Rayuwata ammh ace yau saboda Soyayya sai na Gudu na barta...! a"a bazan iya ba Samiha Hakan bamai yuyu bace...hakuri kawai zamu yi da juna  dama kila Allah ya Kaddara bazamu Taba samun Cikar Burinkan mafarkinmu ba Samiha.."yafada Yana Runtse ido Lokaci daya Zuciyarsa na soya so yake yayi kuka ko Zaiji Dadi ammh kuma Karfin Halinsa da 
taurin Zuciyarsa sun hanashi iya Zubar da kwallah.

Itako Samiha tana kuka ta Sulale kasa Ta Riko kafafun Ahmed Tana Fadin"meyasa zaka ce haka Ahmed..? Ka manta Rayuwarmu a Kolejin Birinin kebbi ka manta yadda muka Fara gudanar da Soyayyarmu cikin yardan juna da kauna mai Tsanina ina alkawarin dakamin na kasancewa Dani na har Abada Ahmed ina kaunar dakake ikararin kanayimin Ahmed Ashe duk karyace bazaka iya Sadaukar da komai ba saboda Farincikina da naka ba Ahmed.
? Why meyasa bazaka juyo ka kalleni ba ka Tuna nice Samihan ka Sameluv dinka fa agaban ka Ahmed plz dont say No kazo mu Tafi bamu da Isashhen Lokaci..."tafada tana kuka Tana kallonshi.

Ya daɗe yana Kallonta kafin Lokaci daya ya jaye kafarshi yana ajiyar zuciya Kokarin kara Rikosa take ya Dakatar da ita da Fadin"A"a Samiha...Bazan taba yimiki Abunda kike so ba..Indai wannan kike kira Rashin so na yarda Zuciyarki ta karyata Soyayyata gareki Samiha..Domin ina Sonki sai na Hanaki kima mahaifinki Biyayyah Haba Samiha...yakamata ki natsu ki Dawo Cikin hayyacinki kila Haduwarmu da Soyayyarmu tana cikin kaddaran kowannenmu ne,Kila dama Allah bai Hadamu Domin mu Auri Juna ba..!bai kuma Yarda cewa Duka mafarkanmu su zama gaskiya ba ya hadamu ne domin Jarabatan Duka imaninmu Samiha...Kisani kuma kikara sani ina Sonki ina Sonki..Ina kaunarki kuma Ina mai Tabbatarmiki ko na Rasaki Samiha babu macen da zata Maye min gurbinki koda Nasamu Wata Samihan bazan Taba samun mai Nagartanki ba..Ki koma gida ki yi ma Mahaifinki biyayyah Allah ya baki zaman lafiya da Mijinki ni kuma Allah ya bani Juriya Ki Tashi kije Na Gwammace na Rayuwa cikin Shauki da kuma Begen Soyayyarki ta gaskiya ko da da ita kadai zan Tsira Samiha..Na gwammace na nuna kauna ta karshe ta hanyar sakaki Hanya Madaidaiciya.."

Yafada Lokaci daya yana juyamata baya ya Share karamar kwallar data gangaromai,kuka Samiha keyi kamar Ranta zai Fita kafin ta mike tana Share kwallarta tana Fadin"Nagode Ahmed...Banta tsammanin zaka juyama Soyayyata dakai baya ba..Zan bi Dukkan Mganarka zan koma gida Abba ya Auramin Wanda yakeso ammh fa ina so ka sani ni Samiha har Abada bazan Taba iya zaman Aure da wani Namiji ba bayan kai...Kai nake so..! Kai nake Burin ka zama miji na Saboda haka zan cigaba da Adana maka kaina...Tsakanin  Duk wasu Shekarun da zasu sakama Tazara da nisantar juna na Tabbata in Soyayyar gaskiya kakemin zaka Dawo gareni...Sai Wata rana...! 

Tafada lokaci daya kafin ta Fita Daga Lungun da kuka  Shima kamar ya Fashe da kuka haka yabi bayanta da kallo Lokaci Daya wasu Tawagen zafafan Hawaye suka zubomasa yasaka Hannu ya Share yana Fadin"Na tabbata zan jure...Zan iya..Zan iya jure Rashinki Samiha sai dai ki sani har na koma ga Allah bazan manta dake ba...Sai Wata rana.."yake fada cikin muryan Rauni da karaya ya Dad'e cikin Lungun nan Haka mutane Daya daya ke wucewa suna kallonsa suna Tambayanshi ko lafiya..? ganin haka yasa yaja Jikinsa da Kafafunsa da sukagama Sanyi ya nufi gida yana Tafe yana Rangaji cikin Ciwon Rai dana Zuciya.

Kaka na cikin Dan karamin Madafin Gidan ya Shigo,ko sallama baiyi ba jan Takalminsa kadai taji ta Fito tana kallonsa cikin Salati take Fadin"La'ila ha'illallahu Ni Bara"atu me zangani Ahmadi kana tafiya kamar wanda aka Zukema Ruwan Jiki sai kace ita Samihan in ka Rabu da ita Ranka ce.."

Tafada tana Kureshi da ido Tsabar yadda Ranshi ke bace cikin Wani Fushi ya waigo yana sakarma kaka jajayen Idanuwansa Lokaci daya yana Zaro mata su baya Taja tana Fadin"Na shiga uku..Ni jikar Audu,Ahmadu bakaken aljanu gareka ne..? Tafada tana Lafewa jikin Kwanon da akayi Madafin dashi Lokaci daya tana Rawan Jiki bai kara kallonta ba yaja Kafarsa ya Shige Dakinsa Harda Turo Kofar katakon Dakin nashi kan Katifarsa mai kama da Tabarma yafada Lokaci daya kawai yaji kuka ya kawomai Abun mamaki baisan sadda ya Fashe da kuka ba mai cin rai da Bakinciki.




*Aisha alto...*
*Janafty*