SILAR HALLACI

Page 2

by @jamilaumarjanafty

*SILAR  HALLACI.*

*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*


_Da sunan Allah mai Rahma mai jinkai_

*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*

*Sanyi flusher!* 
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. 
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta  dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.

*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa  da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.

        *🅿️2*

Shekara ta dubu biyu da goma Shabiyar
2015

*KANO..*
Area:gadan kaya..

"Kura masa ido kadai tayi tana kallonsa cikin mamaki da al"ajabi gani take kamar ba Alhajin data sani bane, kamar ba Mijinta ba kuma uban ya"yanta ba gani take Tamkar Shigowar SAMIHA rayuwar Uban ya"yanta ta chanzashi wanchan Alhaji mai Tsausayi jin kai Dattako da Sanin Darajan mutane uwa uba mai nuna Tsabar jin kai ga ya"yan daya Haifa ya kuma yayi Shekaru wajen basu Tarbiya da kulawa da Lafiyansa da kuma aljihunsa.

Hawaye suka kawo mata cikin kwarmin idanuwanta Bata da Zarafin Hanasu Zubowa tana ji kuma tana gani suka fara Sauka Bisa Fuskarta cikin mamaki yake Binta da kallo yana Tsaye atsakiyar wani kayataccen Bedroom wanda yaji gadon Alfarma hade da Shimfidun alfarma,sai wani makeken Wardrope mai kama da alkarya guda sai madubi wanda yake Shake da kayan kwalliya na mata.

Akallon Farko in kayima Nagartattacen Namijin dake Tsaye zaka Fahimci ba yaro bane Duba da,yadda Farin Furfura ya cika kanshi har zuwa Gemunsa hade da Sajensa Dogon Namiji ne mai a kallah Shekaru 70 aduniya Alhaji Bashir wanbai mutum ne nagari mai halin Dattako da girma acikiin Idanuwan mutane yana da Tarin Dukiya ammh kuma Allah bai Azurtashi da samun D'a Namiji ba matarsa Hajiya Rabi tun Auran Saurayi da Budurwa ita ta haifamai Zaratan ya"ya har Guda shida duka mata kuma Suna nan da Da ransu kafin Shekara biyar baya Alhaji Bashir bashi da wata mtsala ammh bayan Shekara biyar data wuce komai ya lalace daga Bangaren Gidansa Tun bayan Shigowar Samiha Rayuwarsa wacce inda ace ya"yansa sunyi Aure da Wuri yayi jika da ita ko ayanzu ma sai dai Suzo Tsara da yarsa ta Hudu wato Nazifa.

Ita kanta Hajiya Rabin ba yarinya bace Domin a kallan  Farko zaka Fahimci macece hakima mai Jiki da Tsawo akallah zata bama Shekaru 47 baya yanayin data ke ciki ne na jin dadi suka boye Shekarunta ammh daga ganinta zaka Fahimci ansha miya aduniya.

Ganin yadda Hawaye ke Zubomata ne yasa yace"Rabi meye haka..? Yanzu saboda nace miki zan maida Samiha gombe da zama Shine kikemin kuka kamar wata karamar yarinya..?

Yafada cikin mamaki lokaci daya yana kallonta Cikin Takaichi ta dago ido tana kallonsa kafin ta saka Hannu tana Share Hawayenta Lokaci daya tana Fadin"Ba maidata gombe da zakayi bane ya sakani kuka ba Alhaji ina kukan Tsausayin kaina ne da na ya"yana Saboda yadda yarinya karama ta maida Rayuwarka kamar kwallo Tana garawa Haba Alhaji Duk Tarin Gidajenka dake Birnin kano yarinyar  nan  duk basu mata ba Sai ta Daukemin kai ka bita waata uwa Duniya..? Wakake dashi agarin Gombe Duka kasuwancinka suna garin nan ne,Duk Fifita tan daka dinga yi akaina akan ya"yanka bai mata ba ka Duba Fadin Girman gidan nan Na tabbata ko mata goma ake Aure zaka aurosu kasasu acikin Gidan nan su zauna wasu basu matsa wasu ba,ammh Kiri kiri yarinyar nan ta zauna agidanan tace bazata iya zama da matarka da ya"yanka ba kamar wata yar gold Haka ka biye mata jikinka na Rawa ka Dauketa ka sata Sabon Gidan da ka gina da sunana ammh ka sakata ciki saboda ta zabeshi shine Ra"ayinta anya Alhaji Yarinyar nan da iyayenta Sun barka haka kuwa..? Bata wanke gabanta ta baka kasha ba..,?

Tafada tana kallonsa cikin Tabbatar da Tunaninta wani kallon Banza ya jefata dashi kafin ya saki Tsaki yana Fadin"Mts*** Rabi kidaina Abunda kikeyi wannan Wata irinmganar banza ce..ina Daukanki mai Hankali Ashe kallon Kitse nake ma Rogo bansani ba..? Na tabbata ko Abida Bazata aikata abunda kike aikatawa ba abun gwanin kunya kina kishi da Sa"ar yarki..Mganar zan maidata gombe Ina Ruwanki Inace dai Samiha matatace kuma tana Hakki akaina Ina sonta kuma na mata alkawarin komai take Bukata agidan Duniyan nan indai bai gagareni ba zan mata shi karki manta bata sona Mahaifinta ya Tursasa mata ta yarda ta Aure kuma take zaune dani duk hakan ba hallaci bane ni kuma saboda ke sai na kasa mata Abunda take so..?yafada lokaci daya yana kallonta a harzuke..

Bata samu Zarafin Mgana ba Saboda mamaki illah baki da Hanci data saki tana kallonsa,Cikin Hargowa yana Gyara zaman Babban Rigan Shaddar dake Jikinsa yace"Kul dinki Rabi wlh ahir dinki ki Fita daga Sha"anina da Samiha..ba Ruwanki yadda kike matsayin matata haka itama take matata...Ki Kula da abunda ya Shafeki kawai malama Banda ma yadda Girma da jan Raini ina ke ina Tsayawa kishi da Samiha..? Toh bazai sabu ba kijama ya"yanki kunni wlh Daga ke har su duk wanda ya kara batama Samiha Rai wlh nidashi zamu samu babban mtsala..Bana gayamiki zata koma gombe da zama bane domin ina jin Tsoronki sai domin na Fita Hakkinki kada kiji daga baya kice ban gayamiki ba,kishigaTaitayinki Rabi..Ki Fita Daga idona na gayamiki.." yafada yana karkada mata Hannu kafin ya juya ya gyara Hula  ya kama Handle din kofar Bedroom din ya waigo yana Fadin"Tun jiya dama aka gama saka komai na gidan so yanzu zamu wuce ni da dawowa sai bayan kwana biyu dama Abun yazo adaidai kwanar na samiha ne sai na dawo saura naji wata mgana wlh daga ke har ya"yanki Rayukanku su baci Kinjima na Rantse.."

Yana gama Fadin haka ya bude Kofa ya fice Afusace kamar zai Tashi sama Da Kallon takaichi hade dana mamaki Hajiya Rabi ke Binsa da kallo kafin ta Sulale ta Zauna Bisa gado tana Fadin"Allahuman Ajirni fimusibatihi..Domin Wannan yarinyar Shigowarta rayuwarmu masifa ce babba wlh."take fada tana Share kwallah.

Cikin Zafin nama da Fushi yake saukowa Daga kan steps Tundaga Nesa yake bankama Abida da Adama Harara suna ganin haka kowacce ta mike tana Rawan Jiki domin tunda sukaga yadda yake Saukowa jikinsa ya basu ba lafiya har ya karisa saukowa yana Hararansu cikin Girgimawa suka Durkusa suna Fadin"ina kwana Abba.."Harara ya kara Wurga musu kafin ya nuna su da yatsa yana Fadin"Abida...Adama..!Kuna son kuga Fushina acikin gida nan ko..?

Da Sauri suka girgiza kai cikin Tsoro kada kai yayi yana Fadin"Toh Bihallahil Azim in baku cire bakinku akan Matata Samiha sai na saka kafan wando daku acikin gida nan banda Rashin Da ba Matsayin Uwa take gareku ba,..? Ammh saboda Iskanci kuna biyema Shawarar sakaryan uwarku kuna abunda kuka dama ko..? Toh wlh wannan ne na karshe Don Ubanku duk wacce ta kara gayamata wata mganar banza sai nayi mganinta kuma Kowaccenku ta kirata tabata Hakuri duk da burin Uwarku ya cika ta barmu ku garin Duk daba haka Ranta yaso batasone Aurena da Samiha ya kare ta zuba ruwa akasa ta sha sai Allah ya nuna mata iyakarta.." yafada yana Huci,Kowacce kanta ta sadda kasa cikin kunar rai da Takaichi cikin Tsawa ya sake fadin"Kunji ko baku ji ba..?

Da sauri Adama ta Dago tana Fadin"Munji Abba..."Abida kuwa Sarkin Zuciya kunkuni ta Fara kamar tayi kwallah kwafa yayi ya Fice daga Falon yana Fadin"Karma ku kira..Wlh ni daku ne.."Da kallo suka Bishi har ya Fice daga Falon yana kokarin Dauko wayarsa dake Ruri cikin Aljuhun Rigarsa daga ganin yadda ya daga kiran cikin Rawar Jiki yar gold ce ta gaji da Jira ta biyo ba..

Sai da ya fice kana Abida ta mike Cikin Bacin rai tana Fadin"Na Rantse harga Allah bazan kira wannan yar iska yarinyar na bata Hakuri ba..Tabdijam ga duka ga Tsinka jaka.."Adama ta mike tana gyara dankwalin Doguwar Rigar dake kanta tace"Karma kifara wannan Tunanin Abida wlh Dalilin Haka Abba zai ya cima miki mutumci kuma kinsan Sauran harda Umma zai iya hadawa Tunda dama yace ita ke Zugamu.."Abida tace"sai kuma kiyi Anty Adama na Rantse sai dai ko Abba ya koreni daga gidanshi ammh bazan kira wannan matar na bata Hakuri ba..",Daga haka ta wuce Fuu tafara Haura Step cikin  Fushi mai Tsanani da kallo Adama Ta bita tana kada kai kafin ta Dauki wayarta saman Kujeran da suka tashi da marama Abida baya zuwa sama inda Bedroom din Umma yake wato Hajiya Rabi.

Tana Zaune Tun bayan Fitan Alhaji gefen gado inda ta Sulale tayi kukan harta share Hawayenta Sai ga Abida ta Turo Kofa ta Shigo ta Dade Tsaye bakin Kofa tana kallon Mahaifiyar nasu lokaci bayan lokaci take share kwallah cikin Kuna da bakinciki cikin Takaichi Abida ta tako Tsakiyar Dakin,Hajiya Rabi bata sani ba sai dai kawai taji ta Zauna kusa da Ita lokaci daya ta Dafata tana Fadin"Umma..."tafada cikin Rauni da Tsausayi 

Cikin Sauri ta Dago kanta ganin Abida zaune gefenta yasa tayi Saurin goge idanuwanta tana Fadin"Abida baku Tafi makarantan Bane..? Mirmishin dayafi kuka ciwo Abida ta saki kafin tace"Eh umma dayake dama Text kadai garemu so Classrep dinmu ya kiramu yace sai monday.."Kai ta gyada kafin tayi mgana Adama ta Turo kofa ta Shigo Bedroom din Lokaci daya Tana Fadin"Umma kigayama Abida karma ta fara wannan gangancin na kin kiran Anty Samiha ta bata hakuri kamar yadda Abba ya Umarcemu kada ta jawomana wata masifar bayan wacce muke ciki ."Tafada tana zama itama gefen Umma.

Atsanake Umma ta kalli Abida tana Fadin"Ke meyasa kin cika Taurin kai ne..?kina gani ma yan"uwanku dake gidajen mazajensu dai bai kyale ba,kina dai ji Najwa tazo har gidanan tana Fadin irin Dibar albarkar da Abbanku yaje har gida yayi mata gaban mijinta da ya"yanta kan taga wannan yarinyar awani biki bata gaisheta ba ko..?kai Abida ta gyada Umma bata bari tayi mgana ba tacigaba da Fadin"Kuma shine kema kikeso ki jawo ma kanki dani gabadaya..? To karma ki fara Abida yar"uwanki ta fiki hankali Abida kunga Sha'anin mahaifiku da wannan Yarinya wlh ya wuce duk Tunaninku zai iya kakkabeku acikin Rayuwarsa indai Ta nuna bata bukatar hakan..."Ido Abida ta Zaro lokaci daya tana Fadin"ya kakkabemu kuma Umma mufa ya"yansa ne..?

Dariyan dayafi kuka ciwo Umma ta saki kafin tace"kina mamaki ne Abida..?toh kidaina mamaki kunga Fitar mahaifinki yanzu babu Abunda bai gayamin ba kawai dai Bazan iya gaya muku bane ammh musabbabin zuwansa Domin ya sanar dani ne ya Siyama yar gold din nashi gida a gombe tace bazata iya zama agarin kano ba saboda ku,yanzu ma mganar danake muku sallaman kenan zasu wuce chan gomben.."Daga Abida har Adama suka hada baki wajen Fadin"Gombe..Fa kikace Umma...
? Suka fada cikin mamaki.

Mikewa tayi Lokaci daya tana Fadin"ya wuce wai ma...Shiyasa nake son gayamuku ku kwantar da Hankali kawai kubi komai a sannu in muna so dukkanmu mu Tsira da mutumcinmu sai muyi Fatan Allah yasa komawarta chan ya zama kwanciyar Hankalinmu gabadaya.."Atare suka amsa da Ameen suna kara janjanta lamari sun jima Dakin Umma kafin su Fito su barta zuwa Falon kasa ammh cikin Ransu suna kara jinjina Lamarin mahaifinsu suna kuma Tunanin kodai Samiha bata bar mahaifinsu haka ba Bayansu da suke gida basuyi Aure ba,bai kyale ba Hatta yayyinsu dake gidan Aure ba wacce ya kyale Anty Nabila ce kadai bata taba shiga bakin Abba ba saboda Tana bala"in kawaichi da gudun mgana wani lokaci ita ke ma musu Fada in suna wani Abun,in da suna bin mganarta kila da yanzu Abba bai sakoso gaba ba koma miye suna Tunanin Bata bar Mahaifin nasu ba tagama asirceshi sai yadda tayi Dashi.


******

Wata bakar motace Camry ketasha Sharara uban Gudu Bisa Titin da zai kai mutun Garin Gambe,Acikin bayan motan Alhaji Bashir wambai ne da Amayarsa kuma matarshi, Samiha Muhammed Argungu,Motar gabadayanta tana lullube da Tinted ne,Direba ne ke muhallin Gidan gaba yana jansu su kuma suna baya Abunda zai baka mamaki Shine ganin yadda Alhaji ke ta zubamata Hira yanayi yana washe baki Lokaci daya yana kallonta ammh ita tana wani Hakimce, wata faskekiyar wayace ahannunta tana latsawa yadda kukasan bada ita yake mgana ba ammh baisa ya fasa ba duk da ya Fahimci Hankalinta baya kanshi.

Cikin Muryan kauna da Soyayya ya Furta.."Sami...Sami..Sami yan matana.."yake fada lokaci daya yana kura mata ido Wani Siririn Tsaki ta saki kafin ta Dago tana kallonsa bayan ta sakarmai manyan Idanuwanta masha Allah Farar mace alkyabban mata Doguwa ce daga ganinta Dole Alhaji ya Rude ya Susuce domin ko Daga Zaune ta mallaki Sura mai kyau da jan Hankali,Fuskarta bata da fadi sosai ammh ta tsaru da Dogon Hancinta wanda ta sanyama Barima,sai ya kara Fitomata da Asalin kyanta Bakinta bashi girma sai dai yana da Dan Tudu da Fadi kadan,wanda ya sha wani purple din jan baki kamar abakinta aka Zanashi Zarara gashin idanuwanta sun ma manyan idanuwanta kwanya Gsshin giranta yana da yalwar kamar yadda take da yalwar gashin kai,Hakoranta Farare ne sai kuma hakorin makka guda Daya daya kara mata kyau tana sanye da Wata Doguwar rigar materil mai kalan Purpple and pick anmata Dinki Bubu,sai pick din gyle dake yane asaman kanta kafarta data dora kan daya kuwa Sunsha jan lalle cikin Wani Pick din Takalmi mai igiya da Tsini wanda har ya wuce Misali lalle Sarki ya Tabbata ga Shugaban Hallitun Duniya Samiha takai macen da zata Ruda maza da dama irin Alhaji Bashir goma ma ba Daya ba ballema yadda Fatar jikinta ke Fitar da wani haske na musamman na alamun Hutu da jin Dadi,yar shekara Ashirin Da Hudu matashiyar budurwace mai ji da komai da komai na bangaren rayuwa.

Idanuwan data zubamai ne yasa ya kara rikecewa cikin Lallashi yake Fadin"Yi hakuri gimbiya..Allah baki hakuri cigaba da Abunda kikeyi.bazan kara matsa miki ba..

Tsuke baki tayi kafin tace"Haba don Allah Alhaji meyasa wai kai baka Duba Right time ne..?da wannan Hayaniyar naka zanji koda mgana mai muhimmancin Danake awayata.? Tafada tana wani lumshe idanuwanta.

Da sauri ya Tara Hannuwa Alaman Roko yana Fadin"Allah huci ran gimbiyata...Allah baki hakuri cigaba da mganarki bazan kara mgana bama.."

Yafada yana wani karya wuya kamar wani yaron goye Audu Direba dake gaba yana kallon Abunda ke Faruwa ta madubi yace acikin Ranshi."Kai gaskiya Abunda Yallabai yake baya kyautawa yadinga Son kamar ya Dukama wannar yarinyar wacce bata gaji arzki ba ji wannan Abun kunya Alhaji da kimarsa ammh ya koma ya susuce gaban yarinya karama.."Cikin Ranshi yake wannan mganar domin bai isa ya Furta afili ba in ko ya kuskura ya furta haka hanyar cin Abincinshi ta kare daga Ranar domin kan wannan yar gold din Alhaji zai iya sallama kowa acikin Rayuwarsa domin yaga ya Farantamata.

Bata kara kulashi ba illah maida kanta datayi ta cigaba da latsa wayarta Lokaci daya tana sakin Mirmishi shiko ganin tayi mirmishi kar kuso kuga yadda yawani washe baki gabadaya hankalinsa yana kanta bashi da aikin komai sai na kallanta Wayarsa ne ta katsemai kallonta daya keyi ya Zaro acikin Aljihu yadaga yana Fadin"ya akayi ne Manaja...?

Jin yafara mgana da karfi ne yasa ta Dago ta kara sakarmai manyan idanuwanta cikin Sauri yace"Kaga manaja kabari mu isa zan kiraka daga baya..kar mu damu gimbiya.."yagama fadin haka ya yanke kiran Nura manaja baiyi mamaki ba saboda duk wanda ke tare da Alhaji Shekara Biyar dole ya koyi girmama Gimbiya Samiha in ba hakaba ya kara gaba shiyasa bai damu ba illah maida wayarsa dayayi aljihu yana Fadin"wannan gimbiyar itace Jarabtan yallabai.."



*Aisha alto..*
*Janafty*