KWATAR KAI

KWATAR KAI PART 1

by @fatimadahirufuntuwa

๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟKWATAR KAI๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

  
               NA

FATIMA  DAHIRU FUNTUWA  BINTA

PAGE  1

๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ๐ŸŒฟ

***

      "Assalamu Alaikum." 

   Yayi sallama, tare da d'age labilen d'akin; ya shiga. 

        Tana zaune bisa kujera, ta amsa mai babu yabo babu fallasa, ya samu wuri ya zauna gefen ta. 

        Tayi mai wani irin kallo, shima ya kalleta, sannan ya sadda kanshi  'kasa,  ya ce

      "Suwaiba yaya dai?" 

       Ta ce "Dame fa??" 

        Ya ce "Nagane kinayi min wani irin kallo, kamar kinga mara gaskiya." 

          Ta 'kara maida hankalinta sosai akan shi,  ta ce   "Yo ai gani nayi ka shigo d'akina a yanzun,  kuma ni banga amfanin yin hakan ba." 

          Ya kalleta cike da mamaki,  ya ce   "Yaufa  KWANA NA TALATIN kenan dayin auren nan, kuma inaga ai kamar iyakar kwanakin da kika bani kenan ko? Naga sun cika shiyasa na dawo gareki yau." 

         Ta kalle shi a yatsine, ta kauda kanta, wani takaici  ya 'kara isar ta, ta kuma daure cikin rashin damuwa ta ce "Yo  kwanakin har sun cika? Ni naga sunyi sauri." 

          Yayi dariya ya ce "Sun cika mana, yau nake dawowa d'akin ki, ai iyakar abinda  kika bani kenan, kuma ai kinga bai kamata.....................

         Ta d'aga mai hannu  tare da fad'in,  "kaga; dakata Naseer! Ba tambayar ka nayi ba, na dai baka abinda kake so, kuma burin ka ya cika! Kayi Amarya, na yarje maka kaje kayi WATA GUDA A D'AKIN TA, kuma kayi, to magana  tame? Aiba tambayarka nayiba!" 

          Ya ce  "A'ah! to aini sai naga ranki ne kamar ba yadda na saba ganin ki ba, kuma yau na dawo d'akin ki, tsawon lokacin dana d'auka a wurin Amarya, yau kuma na dawo wurin ki, ai kamata yayi in ganki kina fara'a,da d'okin gani na, kema ki zama tamkar Amaryar." 

         Ta ce ni asuwa?Ai bankai wannan matsayin a wurin kaba Naseer! Da nakai wannan matsayin a wurin ka, kana jina kamar Amarya, da baka d'auki tsawon kwanaki TALATIN a wurin ta baka wai waye niba! Ko banza nasan wacece ni a wurin ka! Nasan matsayin daka ajiyeni!! ka 'bullomin ta hanyar da Amaryar ka zata raina ni, domin tasan ni ba komai bace a wurin mujina, kuma ka siyoma kanka rashin zaman lafiya a gidan ka!!!!"

         Ya ce "To! Dakata Suwaiba, na gane inda kika dosa, to amma kuma naga ai kwanakinnan ke kika d'ibar minsu, ba ni nad'iba da kai na ba, ke kikaga dama kika ba ni, kuma nayi, to miye kuma abin tashin hankali a ciki ?" 

           Ta ce   "Kuma kayi? Saboda bakasan darajar matar kaba, kayi watsi da ita tsawon wata guda, saboda kayi Amarya!!" 

          Ya ce "To ni miye laifina a ciki?" 

           Ta ce "Ai ba zaka gani ba! Abinda idanun ka sun rufe! Baka ganin kowa sai Amaryar ka, taya za'ayi kaga kayi ba dai-dai ba? Ai komai kayi da ita dai-dai ne! Ka wula'kanta ni! Ka biyo min ta hanyar da Amaryarka zata d'auke ni ba bakin komai ba!!Tunda har mujina zai iya watsi dani harna tsawon wannan lokacin, ba tare kuma daka damuba, kaga kenan dani da banza duk d'aya!!"

         Ya ce "Suwaiba inda nasan 'karin kwanakin da kikayimin zai zama haka da banyi ba, da nasan ranki zai 'baci akan cika umarnin da kika bani da banyi ba, amma tunda hakan ta faru kiyi ha'kuri, abarshi komai ya wuce, imma kuskure ne nayi; to na d'auka, don Allah kiyi ha'kuri."

        Ta ce "Aidama iyakar abinda zakabani kenan! Ni kuma ka cuceni ka cuci banza!to ka kwana da sanin cewa  idan aka kasa samun zaman lafiya a gidan ka, daga irin rashin adalcin ka ne!!"

         Ya ce  "In Allah ya yarda bama abinda zai faru; sai zaman lafiya, ai Hauwa'un tana da ha'kuri." 

  
     Ta ce  "Ba tambayar ka nayi halin taba! ni dai inta kawomin raini a dalilin abinda kayimin ba ha'kura zanyi ba." 

       "Ya ce  "Abar maganar, Uwar gida sarautar mata! Duk yadda kike so ai hakan za'ayi, mulkin gidan fa a hannunki yake, ba wadda ta isa ta kwace maki wannan  sarautar, duk yadda kikabi da gidan ki ahaka za'a bishi, wane umarni zaki bayar kuma yanzun?" 

     "Ya fad'a a cikin wasa tare da shafo fuskar ta.

 *Bayan kwana biyu*

   suwaiba na zaune tare da 'kawarta Farida wadda ta kawo mata ziyara, sunata fira.

        Suwaiba ta ce "Ke nifa Farida gaba d'aya shawarar da kika bani banji dad'in ta ba, hakanan a banza kinsa naba mujina damar yaita kwana a d'akin Amaryar shi harna wani lokaci, amma ba wani abinda ya sauya, suna son juna su har yanzun, kuma ke kikacemin in basu lokaci su gama d'okin juna tukunna, su gundiri juna, amma ni banga alamar hakan ba, na basu dama ta a banza!!!"

         Farida ta ce" Ban gane ba? Kina nufin kice suna d'okin junan su har yanzun? To wannan wace irin maiyar kishiya ce kika samu? To ni bari kiji, haka nayima mujina, a cikin sati biyu sun fara gundurar juna, sai gashi ina kallo suka fara tashin hankali, da fad'ace-fad'ace, in ta'kaice maki auren ma baije ko inaba, dole ungulu ta komo gidan ta na tsamiya, muka dawo muka zauna daga ni sai shi."

        "Suwaiba ta ce"!   "Toni dai wannan shawarar taki ba tayi mani amfani ba, ke dai tayi maki, amma ni ba tayi mani ba, don har yanzun rawar kai yake da Amaryar nan, tun ina danne kishi na harna fara gajiya, wai dama haka Namiji yake idan ya 'kara sabon Aure?  Kiga dake da babuke a cikin gidan ma duk d'aya, 
 tamkar bai ta'ba Aure ba sai a kanta, wani abin idan sunayi tamkar basa ganin idon kowa a kansu."

    Farida ta ce "Shiyasa nima da naga muji na ya fara wannan rawar kan, saboda yayi Amarya, saina bar mashi ita, nace taje yaita zama da ita na wani lokaci, ya gama d'okin sannan ya dawo gareni, amma in kika cika shige masu ranki kullun  'baci zai ri'ka yi, gara ki barshi inya gama d'okin ya dawo gareki, kinga saiku zama dai dai."

    Humf!! Suwaiba tayi ajiyar numfashi ta ce  "Ke dai kinyi nasara, amma ni banga alama ba, kullun suna manne da juna, Farida nayi ha'kuri sosai, na kauda kai na, amma duk da haka suna cika ni, ba buri na in  kore ta ba, amma so nake mu zama dai-dai ni da ita a wurin Naseer, wannan kirinkin da yakeyi a kanta ya isheni!! wai yaushe ne zamu zama d'aya ni da ita ne??"

        Farida ta ce "Ki 'kara yin ha'kuri, ki ba da wani lokaci ki gani, komai zai wuce, sai kin 'kara kauda kan ki." 

       Suwaiba ta ce "Ni wallahi gaba d'aya  Naseer  mamaki yake ba ni, kiga mutum kamar ba shi ba, na bashi kwana Talatin!! Amma ko d'an irin jayayyar nanma baiyi ba, wai Misali ma ya ce : yaya za'ayi inje inyi wad'an nan kwanakin a d'akin wata, ai bai kamata ba, In gaya maki Farida sai yayi mursisi yaje yayi, ko damuwa bai yi ba, har da wani yimin godiya, to idan yarinyar nan ta raina ni a cikin gidan nan, zaiga tashin hankali, domin kuwa shiya jawo shi, shi ya zubar min da kimata a idon ta."

       Farida ta ce  " Ahh!Gaskiya bai kyauta ba, domin ko ni da na cema muji na; na bashi kyautar kwanaki na, yaje ya yi su a d'akin Amaryar shi, gaskiya sai da ya ja,  ni na kafe nace sai yayi, to kinga ai kasan an kula da kai,
amma kawai daga cewa kaje kayi shikenan kamar kana jira, ba wata jayaiya, gaskiya bai yi maki halacci ba, amma ba komai, wata rana sai labari,  ni na tabbatar maki nan gaba sai kun zama dai-dai, amma sai kin shanye damuwar ki."

        Suwaiba ta ce  " To ai shine abu mai wahala, na gaji!! Farida na gaji!!! ba zan iya gani ba, ki barni dasu kawai, tunda shi bai san al-kunya ba, sai munyi fito na fito dashi, kafin mu dai-daita."

MISALIN   'KARFE TARA NA SAFIYAR RANAR ASABAR 

    Yayi shirin shi tsaf! zai fita, ta taso da sauri ta nufo wurin shi, tare da fad'in    "Fita zakayi?" 

        Ya ce  "E  fita zanyi wani abu?" 

         Ta ce   "Dama ina so zani gidan mu ne, ko in shirya sai ka sauke ni?" 

       Ya ce  "To kiyi sauri kada ki 'bata min lokaci." 

         Ta ce   "To shikenan."

   Sannan tayi sauri ta shirya ta fito. 

    Ta biya tayi ma Hauwa'u sallama, tare da fad'in "Zamu fita, sai mun dawo." 

       Hauwa'u ta ce "To sai kun dawo, ta kalli Nasser ta ce   love bye bye, ka dawo lafiya, Allah ya tsare min kai, sannan ta kalli Suwaiba ta ce Aunty sai kun dawo." 

        Suwaiba ta ce "Allah yasa." 

         Sannan suka fita, cikin motar  shi suka shiga, yaja suka fara tafiya.

        Ya  ce  "Kinsan wani abu suwaiba?" 

         Ta ce "Saika fad'a." 

          Ya ce  "Aboki na Ibrahim na Funtuwa shine yake gayamin zaiyi Aure, watanni ukku masu zuwa." 

         Ta ce    "Ikon Allah, komai da lokacin shi, sai yanzun zaiyi aure fako?" 

        Ya ce "E sai yanzun Allah ya kawo lokacin, kinga kenan inada biki." 

        Ta ce   "Kwarai kuwa, kaga sai ka tafi da Hauwa'u, itace bata ta'ba zuwa Funtuwa ba." 

        Yayi dariya ya ce ita ma wannan maganar tayi ce koko??"

         Ta ce "Wane irin tayi kuma? Da gaske nake ka tafi da ita." 

          Ya ce "To ai ina gudun kada a mai mai tane, halin naku ne na mata sai ku, ku zakuce ayi abu kuma daga baya yazo ya dame ku." 

         Ta ce   "To ai ni gaba d'aya Nasser mamaki ka bani, daga cewa kaje kayi wata d'aya shikenan ko gaddama bakayi ba, kaje kayi abinka hankalin ka kwance." 

        Ya ce "To ai ni nasha irin halaccin nan ne naku na mata kikayi mani, ganin ke shekara Hud'u muna tare dake, shine kika tausaya mata, ki ka bata wad'an nan Kwanakin, shi yasa banyi maki gardama ba, to yanzun kuma ga tafiya ta tashi kince in tafi da ita, kinga ai dole in san kyautar taki iya baki ce koko har zucci?"

       Ta ce Da gaske nake, ku tafi." 

         Ya ce "A'a, duk wadda aiki ya fad'a kanta ranar da ita zan tafi, shikenan ko?" 

        Kafin ta  'kara yin wata magana,  wayar shi tayi Ringing, yasa hannu ya d'aga

     "Hello baby na yaya dai?"

       Ta ce "Love yaya hanya?" 

      Ya ce   "Hanya gata nan munata bi kin fara missing d'ina ko?" 

      Ta ce   "Aiko kamar kasan abinda zan fad'a kenan." 

       Ya ce   "To kiyi ha'kuri kinji, yau muna tare, indai nine ki kwantar da hankalin ki, zan dawo da wuri, duk abinda kike so dani kinga sai kiyi." 

      Ya yi kissing d'in wayar tare da fad'in "Bye, ki jira ni ina nan dawowa." 

       Sannan ya yanke kiran, tare da 'kara maida hankalin shi bisa titi, ya ce   "Wai har yanzun bamu kai bane?" 

       Ita kuma da take gefen shi a zaune, ta riga ta gama cika ma'kil!! Ta ce "Ai wai dama Nasser ka iya irin wad'an nan kalaman ni bamma sani ba? wai ko ka d'auka kai kad'ai ne a cikin motar nan ne?" 

         Ya ce "Wani Abu kuma nayi?" 

     Ta ce     "Au! Ba ka masan abinda kayi ba?To bari in fito maka a mutum! Na gaji! Cin kashin karen da kuke yimin kai da Amaryar ka ya isheni!! Wai ni meka maida nine? Da ni da babu ni duk d'aya!Kai nifa na lura tunda ka  'kara auren nan d'okin naka yaki 'karewa! Adadin kwanakin dana baku ya tafi a banza kenan?Tunda abin ya'ki ci ya'ki cinye wa! To gaskiya ni bazan iya ba!"

         Ya ce  "Ya kike so ayi?" 

          Ta ce  "Sauke ni a nan, na fasa tafiyar!Domin tafiya da kai ma ba'abinda zai haddasamin banda ba'kin ciki! Ka sauke ni nace tafiyar na fasa!!" 

         Ya ja birki ya tsaya, tare da kallon ta ya ce   "Wai ni Suwaiba na rasa abinda yake damun ki, gaba d'aya  kin canza." 

         Ta ce   "Nice ma na canza? Kai ba kaga irin canzamin d'in da kayi ba, ai kai ne ka fara canzawa, ni ma na zame maka haka, kuma muddun ba dawowa kayi yadda na sanka ba to haka zakaita gani na, nima babu ranar da zan canza! Aida ba haka kake ba, auren nan da kayi shine ya dabar-bar-taka, kuma indai ba zaka dawo yadda na sanka ba, to haka zamuyi ta zama da kai babu ranar canzawa!!"

         Ta bud'e murfin motar ta fita da sauri, ta re da tare mai adai-daita sahu ta hau, ya juya da ita gida.

          Shi kuma yana nan zaune ya d'ora kanshi akan sitiyarin motar, yana tunanin irin wannan hali na Suwaiba, shi dai yasan lokacin da yake neman auren nan da goyon bayanta akayi, amma
 yanzun gaba d'aya ta canza, ba ta ta'ba nu na mani wani  'bacin rai ko rashin yarda, lokacin da nake neman auren nan ba, sai yanzun da Amaryar ta shigo gida, ko da dai har yanzun bata ta'ba bud'e baki tace min auren ne bata soba, to amma miye kuma na abu kad'an sai ta hau?Shima yana nufin kishi take yi da ita kenan? Ko dani ban ta'ba ganin ko sa-in-sa ta shiga tsakanin ta da Hauwa'u ba, suna zaune lafiya, to amma ni me yasa take yimin haka? Wane hali na canza mata ne?"

        Ya girgiza kan shi tare da jin tafiyar ma duk ta sure mai, don haka ya juya kan motar shi ya koma gida.

       'Dakin Suwaiba ya wuce, ya same ta zaune tayi tagumi da hannayen ta, hawaye naci gaba da gudu a fuskar ta.

       Gaban ta ya zo ya tsaya, tare da fad'in, Innalillahi wa inna'ilaihirrajiun!Suwaiba me nayi maki ne? Miye kika ga na canza maki; wanda ada nake yi maki shi, yanzun kuma na daina? menene yake tada maki hankali game da nine?"

        Ta d'ago ta kalleshi idanu jajur ta ce    "Bai kamata kayi min wannan tambayar ba, yaya zaku d'auke ni sakarya kai da Amaryar ka! Sannan ka zauna kana tambaya ta? Inba wula'kanci ba!! ai tasan ina tare da kai, don miye zata kira ka?  Kai kuma ka saki jiki kana fad'a mata wasu kalamai dani tunda nake ban ta'ba jin sun fito daga bakin ka ba, ai abinda kuke yi min 'baro-'baro yake a fili!Kai ma ka sani ba sai ka tsaya tambaya taba!! "

       Ya ce  "To in ta kira ni ba matata bace?" 

      Ta ce  "Ai dama haka nake so ka fad'a!Yadda aka raba kwana, maganar ma zan iya sawa a raba ta! Irin wad'annan maganganun ta ha'kura in kun shiga d'aki can kuyi a binku, amma ba'a gaba na ba! wannan ai cin fuska ne!! Taya za'ayi ina jinka kana fad'a mata kalamai wa'danda ni tunda nake ban ta'ba jin ka fad'a mani irin su ba!Bamma san ka iya ba!sai kawai dalilin ka 'kara Aure sai ka bijire ka canza dabi'ar ka! da halayyar ka!! Don miye hankali na bazai tashi ba !!!!"

       Ya tsugunna gaban ta tara da dafa 'kafafunta, ya ce "Kiyimin uzurin abinda zai fito daga baki na yanzun, 

      Wallahi Suwaiba har yanzun na kasa gane laifi na a wurin ki, saboda duk abinda nakeyi gani nake dai-dai nakeyi." 

        Tayi saurin ture hannayen  shi daga jikinta ta ce  "Ai ba zaka gani ba! Soyayyar Hauwa'u ta rufe maka idanu! Baka gani kowa sai ita! Ita kad'ai ce 'yar lele a wurin ka, ita kad'ai ce kake nunama tsantsar soyayyar ka a gareta!! ni kuma shikenan ka gama yayina!!" 

         Humff!!  Yayi ajiyar numfashi tare da fad'in "Me yasa kike so ki fito min da tsantsar kishin ki ta haka ?Meyasa kike dafa ni da ruwan dana kasa fahimtar na zafi ne ko na sanyi? karki manta Suwaiba, babu wanda ya isa yaci zamanin shi, sannan yaci na wani, shekara hud'u muka yi ni-da-ke muna soyayya, dom me ita don tazo tayi na wata d'aya rakk! zaki tada hankalinki? Kuma naga wata d'ayan nan ma ai ke ki ka ba nishi ba niyyar kaina tasa nayi ba."

      Ta ce "Nasan haka sai ta faru!!!  Wai me yasa koda yaushe ku maza Azzalumaine!!!!?kai tsakaninka da Allah abinda kakeyima Hauwa'u yanzun shi kayi min ada?" 

         Ya ce   "Har wanda yafi nata ma nayi maki." 

       Ta ce  "To ni ban gani ba! Ai abinda kuka
 iya fakewa da shi kenan da zarar kun 'kara aure! sai kuyi ta wula'kancin ku da rashin kunyar ku a gaban matan ku, idan mace ta nuna ranta ya 'baci, sai kuce ai da itama anyi mata haka!Kuma naga ai da ta wuce! In kuma ka isa ka tariyo ta ta dawo baya!!"

        Ya ce "To ni dai na gane manufarki, yanzun kwanakin da kikabani na yi a  d'akin ta, sune suke damun ki?   To ko maida maki su zanyi in kashe wannan wutar?" 

      Sai jin muryar Hauwa'u suka yi ta d'ago labilen d'akin tare da fad'in.

       "Daga baya kenan!Ai wad'an nan kwanakin ta riga tayi asara su! In banda 'karamin tunani irin naki! Ta yaya don kin bani KWANA TALATIN da muji na zai gundure ni! ai saidai mu 'kara son junan mu, Idan kuwa har uwar gida za tayi tunanin ta d'auki kwanakinta taba ma Amaryar ta, wai don su gundiri juna, to tayi kuskure! ita me yasa tsawon shekarun da sukayi da mujin nata basu gunduri junan suba? Sai wata ce da take sha-sha-sha!! Zata gunduri mujin ta,  to ni da Nasser daram-dam!!soyayya ma ba kiga komai ba!!!"

           Ya yi saurin dakatar da ita, tare da daga mata hannu, cikin tsawa ya ce  " Ki fita!!ki fita na ce!! me ma ya kawo ki d'akin??"

         Suwaiba ta ce" Barta ta idasa abinda zata fad'a, koma miye kai ka jawo mani! Ta dakata d'in me? Bayan ta gama fad'in abinda zata fad'a, koma dai miye ni kai ka jawo mani! kai ka fara zubar min da mutumci na a wurin ta, shi yasa ta samu damar abinda ta gayamin yanzun! Laifin gaba d'ata naka ne! kai ka 'bullo ta hanyar da gidan ka zai kasa samun zaman lafiya, saboda wallahi kai ba ADALIN MUJI bane!!!Ka gama tozarta ni a wurin Amaryarka!!Tunda har gashi ta samu damar da take yimin La'be. "

        Hauwa'u ta ce" Ni bazan iya baki muji na yayi kwana TALATIN a d'akin ki ba, kidai d'auka kawai wad'ancan kwanakin kinyi asarar su, tun............

         Naseer ya ka tseta tare da tura ta waje, ya ce   "Fita da Allah!! Waye ma ya sako ki cikin maganar mu?"   ya kore ta; ta bar d'akin. 

      Sannan ya juyo ga Suwaiba, ya ce   "Aikinga irin ta, gashi nan........

        Ta ce "Kada ka  'kara yimin magana!!FITA KAIMA!!!! ka fita kabarmin d'aki!!!!!  NI yanzun ba bu abinda zaka gayamin in saurare ka!!!"

        Ya ce "Amma ai..........

         Ta ce   "Ka fita nace!!!!!!"

         Cikin fushi ya bar d'akin, ita kuma ta zauna, wani irin matsanancin kuka mai sauti ya kwace mata.

         A fusace ya shiga d'akin Hauwa'u, yana fad'in   "Wai wane irin neman fitina ne wannan? ya kuke so ku mayar da nine? meya kai ki d'akin ta; al-halin kin san ina ciki? Wane irin neman tashin hankaline wannan?" 

        Ta  'karaso inda yake cikin sanyin jiki, Ta ce   "My love ba haka bane. 

Ta kama hannayen shi cikin shakwa'ba ta ce 
     " Kwantas don Allah, samu wuri ka zauna kaji." 

      Humf!  yayi sansanyar ajiyar numfashi, ta d'ago ido ta kallai cikin fari, sannan ta jawo shi ta zaunar dashi bisa kujera.

        Ta ce   "Nasan kun fita, amma  bansan dawowar kuba, shine naji hayaniya a d'akin, koda naje   'kofar d'akin zan shiga sai naji kana cemata.

     (To na dai gane manufarki, yanzun kwanakin da kika bani nayi a d'akin ta sune suke damunki? toko maida maki su zanyi in kashe wannan wutar?) 

       To  gaskiya bansan lokacin da naji hankali na ya tashi ba, domin kuwa babu abinda na tsana irin kayi nesa dani, ina yi maka wani irin so da ban iya nisa da kai na tsawon sati guda, to amma sai inji kana zancen zaka maida mata KWANA TALATIN, gaskiya ni bazan iya wannan ha'kurin ba."

      Ya ce "Hakane, amma ina so ki fahimci wannan matsalar ba taki bace, tsakani na da ita ne, bata saka ki a ciki ba, ki fita harkar ta, babu ruwan ki, rigimarmuce ni-da-ita, kar ki 'kara saka bakin ki, tunda take tashin hankalin ta bata ta'ba sako ki a ciki ba, kin san ko tun yaushe muka fara wannan rigimar? Tunda bata saka ki  a ciki ba; ina abinda ya dame ki? Karki 'kara! na gaya maki."

        Ta ce  "To shikenan." 

         Ya ce "Tashi muje ki bata ha'kuri, domin bana son rigimar nan ta had'a dake." 

    Ta d'anyi jimmm!sannan ta ce "To muje, suka tashi suka nufi d'akin suwaiba. 

     A zuciyar ta tana fad'in, "Badon ita zani ba, don dai kawai in cika umarnin  mujina ne, koba komai zai 'kara yarda da hankali na, ya kuma 'kara so na, matsayi na na me yi mashi biyayya, In kuma 'kara saima kaina daraja a wurin shi."

        Yana gaba tana biye dashi, har 'kofar d'akin ta, ya bubbuga, domin kuwa ta rufe shi gamm!

     Ya ce  "Suwaiba ki bud'e, tare da bubbuga 'kofar,  "Ki bud'e Suwaiba." 

       Ta ce   "Bazan bud'e ba! saboda ba abinda zaka gaya mani yanzun! abinda dai kake so ai kayi! don haka ka tafi ka barni inji da abinda yake damuna!!" 

        Ya ce  "Ki bud'e  kiji abinda ya kawomu mana." 

          Ta ce   "Bazan bud'e ba! bana bu'katar jin komai daga gareku!!!" 

      Ya juya ya kalli Hauwau ya ce   "To jeki shikenan." 

         A zuciyar ta ta ce "Alhamdulillah! Dama haka nake so, haka nan kawai a sani inje in wani ba kishiya ha'kuri, gara ma da ta'ki bud'ewa." 

      A fili kuma ta ce  "To shikenan love muje, ai anjima na nan, sai in bata ha'kurin." 

         Ya ce   "Ki rabu da ita kawai, kaddai ki  'kara shiga tsakani na da ita, kinji ko?"

           Ta ce  "To shikenan, in Allah ya yarda za'a kiyaye." 

     Suwaiba kuwa data gaji da kukanta sai ta lalubi wayar ta, ta kira Farida.

       "Hello Farida yau an  'bata mani rai!kishiya ta wai take gaya min nayi asarar Kwanaki na!" 

         Farida ta ce "Garin yaya?" 

         Suwaiba ta ce "Wai harni take cema soyayyama banga komai ba!  Wallahi Farida laifin Nasser ne, kawai shine ya bata damar tayi mani hakan." 

        Farida ta ce  "Waime ya kawo ta gaya maki hakan?" 

         Suwaiba ta ce "Nasser ne ya ce zai maida mani kwanaki na, saboda yaga hankali na ya'ki kwantawa." 

        Farida ta ce   "To ke me yasa kika kasa kwantar da hankalin ki? Abinda ya wuce fa ya riga ya wuce, sai kuma adubi gaba, kiyi ha'kuri kawai ki kwantar da hankalin ki, wata rana zakiga abin ya wuce kamarma ba'ayi ba." 

         Suwaiba ta ce "Tayaya za'ayi hankalina ya kwanta?Kinji yadda suke magana? har wani suna suka sanyama junan su, ni naga iskancin nasu ma ba 'karewa  yake ba." 

       Farida ta ce To kema ba sai ki sanya mai sunan ba. "

        Suwaiba ta ce "Don tace ina gasa da ita? ke nifa Allah nema ya taimake shi, ba d'aki na yake ba yau, da sai mun kwana tashin hankali, amma ba komai, zai dawo ai." 

        Farida ta ce  "Kafin ya dawo d'akin naki kin huce, don Allah ki ri'ka danne zuciyar ki Suwaiba, ba komai ke damunki ba kishi ne kawai, amma kiyi ha'kuri komai zai wuce."

          "Humff!! Suwaiba tayi ajiyar numfashi ta ce  "To shikenan sai anjima, na gode."

Fatima Dahiru Funtuwa Bintaโœ