Hs 11
by @legendspen
_Page 11_
Ajiyar zuciya ta sauƙe tana cewa. " Amen." Ƙasan zuciyarta kuma yana raya mata cewa akwai matsala.
Murmushi yayi ganin ta tafi duniyar tunani ya ce. " Mar'atussaliha!."
Juyowa tayi tana kallon shi ta ce. " Na'am Hayati."
" Kar ku saka damuwa a ranki kinsan ciki ne dake, yanzu ba lokacin tunani bane, yanzun lokacina ne." Ya daga mata gira.
Dariya tayi tana fadawa kirjinsa.
*Senate*
Yana zaune a tsakiyar gadonsa shi da Anas suna video call da Juraij da Salman.
Salman ya ce. " Senate soyayyar yarinyar nan ya saka baka gane komai."
Anas ya ce. " Hmm!! Ku da bakwa tare dashi kenan amma har kun gane, idan zaku bawa yaron nan shawara tun wuri ku bashi, bayi da magana sai na Bhatool."
Rai a bace ya kalli Anas yana cewa. " Na fada maka ka daina kiran sunanta tsirara kana cewa Anuty Bhatool."
Dariyar rainin hankali Salman yayi yana cewa. " To kaji dai ko Anas, saboda haka take note."
" Ni fa bazan ce mata Anuty ba, after all na girme ta."
" Wallahi da Anuty zakana kiranta." Senate yayi maganar yana hararan shi.
Dariya kawai yayi yana kallon Juraij ya ce. " Ya kayi shuru fa?."
" Hmm!! Ba shuru nayi ba, lamarin Senate ke ban tsoro, nifa nasan yarinyar kuma akwai rawan kai, ga rigima, kaga Senate kuma bai iya ba, shine nake tunanin soyayyar nasu."
A tsawace ya yi maganar wanda yasa dukan su yin shuru. " Ina ruwanku idan tana da rigima, ko ku zaku zauna da ita ne? For the last time idan daya daga cikin ku ya sake embarrassing din matata ban yafe ba, kuma sai mun rabu dashi."
" Gaskiya ne baka so kuma dole sai mun fada maka." Cewan Juraij a fusace yana disconnecting din nasa, Salma ya ce. " Mun ji ayi hakuri." Shima ya kashe.
Anas ya tashi ya nufi kofa yana fadin. " A dakin k'asa zan kwana sai da safe."
" Ku kuka sani kuma." Ya fada yana jan bargo ya rufe fuskarsa.
~~~~~~~Washe gari
Tana tashi da safe ta shirya dan yau suna da lecture na karfe takwas kuma tana so tayi attendance, shiryawa tayi cikin abaya blue mai ratsin fari, sai sheki da daukar ido yake, tayi roiling din veil dinsa.
Handbag dinta ta dauka ta saka perfume nata da lips glow ta jefa biro a ciki, kafin ta dauki wayanta tana bud'e wardrobe ta dauki kudi ta zuba.
Sauri sauri ta fito, a daining ta hangi Yaya Karima da mijinta suna breakfast, isa gurin su tayi ta gaishe su tana cewa. " Na tafi muna da class eight."
Barrister ya bata kudin machine, ta karba tana godiya ta fito waje.
Tana tsaye machine yazo ta hau, a bus stop ya ajiye ta ta bashi kudinsa ta hau wani machine zuwa Makarantar.
Tana shiga Makarantar ta kira number Amrah, bugu daya ta dauka tana cewa. " Billahil lazi kiyi sauri wai test zai yi."
Kashe wayan tayi tana sauri ta isa department nasu.
" Excuse." Ta fada cikin sanyin murya.
Kusan duka ajin sai da suka juyo da hankalin su zuwa gare ta, a hankali Lecturer ya sauke glass din idanunsa ya zuba mata ido.
Magana class din ya dauka wasu na fadin bazai barta ta shiga ba wasu na cewa ya fada soyayya da ita.
Muryansa taji yana cewa. " Ki shiga test zanyi."
Da mamaki team nasu suka kalli juna, Jannah ta ce. " Kun ga kallon da ya mata kuwa?."
Amrah ta rage murya tana murmushi ta ce. " Ni kuwa na gani."
Suhaima na fadin. " Ku bari sai mun fita kafin muyi magana, yanzu any slice of mistake zai fitar damu." Shuru suka yi suna zubawa Bhatool ido.
Duk taji wani iri, a sanyaye ta soma tafiya zuwa gurin su ta zauna, paper ta ciro ta rubuta reg no ta, kafin ta fara rubuta question din, question biyar ya rubuta ya ce a amsa duka kuma 30 minute, sannan ko wanne da a and b.
A hankali ya soma zagaye class din yana kallon su daya bayan daya, dai-dai bayanta ya tsaya yana zubawa yatsunta kallo ganin yanda take rubutu a natse.
Ji tayi kamar an tsaya a kanta hakan yasa ta juya ba shiri, karaf suka had'a ido, da sauri ta janye idanunta tana kallon Amrah ta gefen ido, murmushi kawai suka yi wanda iya sune suka gane abun su.
Sai da ya tabbata ta gama kafin ya ce. " Submit, before I count 1 to 5." Kafin ka ce me har kowa yayi submitting.
Suna fitowa daga ajin Amrah ta ce. " Guys I don't get rite, me hakan ke nufi?."
Tafiya suka cigaba da yi zuwa wajen garden Jannah na cewa. " Maybe kawai ya taimake ta ne."
" Wannan ba taimako bane, ko kin manta waye Dr Hashim? Ranar fa bani da lafiya nazo amma ya hanani shiga lecture dinsa, yau kuma Bhatool tazo kuma tayi letting amma ya bar ta ta shiga." Suhaima ta fada tana zama a kujera bayan sun iso garden din.
Kallon su kawai Bhatool tayi kafin ta gyara murya ta ce. " I don't think that so, maybe kawai ya taimake ni ne kamar yanda Jannah ta ce."
Tabe baki suka yi suna chanja hira, a cikin hiran ne Amrah ke cewa. " Yau ban ga wannan kyakkyawan saurayin yazo ba."
Lokaci daya Bhatool ta hade rai tana cewa. " Ina ruwan ki dashi?."
" No kawai tambaya nayi fa, naga ya saba zuwa ne, kin ga dole na tambaya ko lafiya."
Ba ta bata amsa ba suka wani yazo gurin su yana cewa. " Bhatool tazo inji Dr Hashim nan da minti biyar." Ya karashe yana juyawa ya tafi.
A tare suka hada baki gurin furta. " Whatttt!!!!."
Amrah ta ce. " Wallahi na fada muku dama kallon da ya mata ba'a banza ba akwai dalili, ya fola." Ta karashe suna tafawa ita da Suhaima.
" Kai dalla shut up, ku fa kun zare I swear, kun san me nayi ne?." Tayi maganar tana duba gefe da gefe kafin ta cigaba da cewa. " Amma idan ya nuna alamun soyayya, to idan mun kara yin karatun shi make i bend, ai na banza ya samu." Ta mike da wuri tana cewa. " Bari naje kar na makara."
" Bhatool idan kin ga ruwan sanyi ki kawo mana." Cewan Jannah suna dariya.
*Senate*
Ko da suka hadu da Anas a daining babu wanda ya yi wa wani magana, har sai da Momi ta lura da haka ta ce. " Naga yau baku yiwa junan ku magana ba, is that any problem?."
Girgiza kai Anas yayi yana cigaba da cin abinci, mikewa Senate yayi ya koma perlo ya zauna yana kallo amma rabi da kwatan hankalin shi yana gurin Bhatool.
Sallaman abokanan shi yaji, da sauri ya juyo dan tabbatar da su din ne.
Salman ne da Juraij kowa rai a hade, suna kallon shi suka dauke ido, gurin Momi da Anas suka nufa suna murmushi.
Da mamaki Senate ya mike yana kallon su, kamar zai yi kuka ya ce. " Ni kuke sharewa? Then sai me idan kun ki yimin magana, Mtsw." Ya dauki key din motansa ya fice daga falon Momi na cewa ya tsaya bai saurare ta ba.
Salman yayi murmushi yana cewa. " Momi zafin soyayya ke rudar shi, yanzu ba'a isa a fada masa gaskiya ba inde akan Bhatool ce."
Fuskar Momi da damuwa ta ce. " Me ya faru ne?."
Juraij ya ce. " Hmm! Momi dan kawai mun ce yarinyar tana da rigima shine yayi fushi damu, shi ne muma muka yi fushi da shi."
Bata ce komai ba ta nufi dakinta dan dauko wayanta ta kira shi.
*Bhatool*
Da sallama a bakinta ta shiga office din nasa, yana zaune akan gujera mai juyi yana facing din kofar shigowa.
Bayan ya amsa sallaman ne ya nuna mata kujera yana cewa. " Have a seat."
Zama tayi tana sunkuyar da kai, bata ankara ba taji maganar da ya kusa toshe mata kunne da ganin ta....
✍🏼 Legend's pen ***.
ku yi following sabida samun update akai akai, sannan ku dan duba discussion ku ce wani abu mana pls😫 kamar na fasa ihu
Vote and comment pls