HASASHEN SOYAYYA

Hs 12

by @legendspen


_Page 12_












Bayan ya amsa sallaman ne ya nuna mata kujera yana cewa. " Have a seat."


Zama tayi tana sunkuyar da kai, bata ankara ba taji maganar da ya kusa toshe mata kunne da ganin ta.


" Za ki aure ni?."


Da sauri ta dago da manyan idanunta ta zuba masa, kamar wacce aka ce an aikowa da sak'on mutuwa, muryanta har rawa yake gurin cewan. " Sir Ina da wanda nake so."


" I don't care 🤷‍♂️, ba shawaran ki nake nema ba umarni na baki." Ya fada yana nuna ta da yatsa, kafin ya cigaba da cewa. " If not duk abunda kika gani ke kika jawowa kan ki, na baki nan da gobe kadai."


Wani yawu mai kauri ta hadiye, tun da take ba'a taba yi mata barazana ba sai yau, hakan kuma ba karamin tasiri yayi ba a kanta.


" You can go." Ya fada yana juyawa akan kujera.


Da sauri ta tashi ta fita daga office din har tana k'ok'arin fadi.


Gudu yake tsulawa akan titin, horn kawai yake yi sai motoci su matsa, da gudu ya shigo YSU yana parking a tsakiyar Makarantar.


Ya dade a ciki kafin ya fito yana bata fuska saboda zafin ranar yau din daban ce, gurin garden ya fara nufa amma sai yaji zuciyarsa bata canja bugu ba, da mamaki ya furta. " Bata nan kenan.." Bai karasa ba ya hango ta tana nufo garden din duk a burkice.


Duk da ya ganta a burkice amma sai da murmushi ta kufce masa, cike da k'asaita ya fara nufo inda take yana murmushi, wanda ita ko lura dashi bata yi ba.


Tana shirin shiga garden ne tayi tuntube za ta fadi, cikin zafin nama ya taro ta ta fada kirjinsa, yana furta. " Subhanallah tunanin me kike yi haka."


Sai da ta runtse ido kafin ta bude tana zuba masa, duk a tunanin ta zata fadi, janye jikinta tayi tana dan yin baya kafin ta ce. " Thanks."


" Tunanin me kike yi?." Senate ya fada yana duban fuskarta.


Girgiza kai tayi tana cewa. " Babu."


Bai ce mata komai ba har ta isa gurin su kawayen ta ta zauna.


Dukan su ita suke kallo, kafin Suhaima tayi magana a sanyaye. " Me ya faru Bhatool?."


Shuru ta musu bata ce komai ba, ganin kamar bata tare dasu ne yasa Amrah taba ta tana fadin. " Bhatool!!!." A furgice ta juyo tana kallon su.


Jannah na fadin. " Me ya fada miki?."


Girgiza kai ta shiga yi tana kallon inda Senate yake tsaye ya zuba mata ido, duk kuma maganar da suke yi yana jin su.


Kamar baza tayi magana ba sai kuma ta ce. " Babu abunda ya faru, just kawai gaisawa muka yi."


Dariyar rainin hankali Jannah tayi tana cewan. " Wallahi karya kike Bhatool, tun yaushe muke tare da ke, mun sanki ciki da bai fa."


Hararan ta Amrah tayi tana cewan. " Barta ta raina mana hankali ne, idan bata yarda damu bane ai shikenan damuwar ki." Amrah ta mike a fusace zata tafi.


Tashi tayi kamar zata yi kuka ta rike ta tana fadin. " Ba wai ban yarda da ku bane, after all kun fi kawaye a gurina kun koma jinina ne."


Suhaima ta girgiza kai ta ce. " Idan har kin dauke mu jininki ai zaki fada mana ba wai kice ba komai ba."


Wani yawu ta hadiye mai kauri, kafin ta juya ta dubi Senate da ya hade hannun a kirji ya zuba mata ido yana jiran yaji me zata ce, kafin ta sunkuyar da kai ta ce. " Wai sona yake yi, dana ce masa ina da wanda nakeso shi ne ya ce ya bani daga yau zuwa gobe wai na yarda, ko kuma duk abunda ya faru ni na jawo."


Maganar da ya kusa hargitsa zuciyar Senate kenan, bai san sanda ya bar gurin a furgice ba.


Kusan a tare suka furta. " Whatt!!!."


Jinjina musu kai tayi tana cewa. " Bansan me yake nufi ba, and...." Ta juya taga baya gurin hakan yasa tayi shuru tana tunanin ina yayi.


Amrah ta ce. " Dama kwarto ne, ai na dade da fada muku kune baku yarda ba."


" Yanzu ya zamu yi Bhatool?." Cewan Suhaima a dan tsorace.


Numfashi ta sauke ta ce. " Duk abun da zai yi yayi, karshe dai ya ce bazan yi passing din course na shi ba ko."


" Ni fa ba wannan ba ne tsoro na." Cewan Jannah tana cigaba da cewa. " Kin san duk yarinyar da ya ce yana so sai ya same ta, idan kuma bai same ta ba to ya saka ayi raping na ta."


Dukan su shuru suka yi kowa da abun da yake tunanin a zuciyarsa, kafin ta kalli agogon hannunta tana fadin. " Ni zan koma gida."


Suhaima tayi magana a sanyaye cike da damuwa. " Ki bari mu gama lecture mana."


" A'a akwai abun da zanyi ne." Ta karashe tana daukar handbag din ta.


Har bakin get suka raka ta ta hau machine kafin suka dawo cikin Makarantar ita kuma ta nufi gida.




*Senate*


Bai san sanda ya isa gurin motarsa ba ya shiga ya mata key ya fice a 360, idanunsa yayi ja ga wani ruwan da ya kwanta a ciki, fuskarsa tayi ja abunka da fari, jijiyoyin kansa sun fito rad'a-rad'a.


Gudu kawai yake zubawa akan titin kalamanta yana masa yawo a kwakwalwa. < Wai sona yake, ni kuma na ce masa ina da wanda nake so.>


Bai lura ba da machine din da yake gabansa har ya kusa bugawa, wani burki ya danna da karfi ji kake chusssss, buga kansa ya soma da stirring yana fadin. " Why? Why!!!! Waye wanda take son? Dama tana da wanda take so ban sani ba? Ba zai yu ba, ni zan aure ta ba kowa ba! Ni neeeee!!!." Ya karashe da karfi.


Wayansa ce ta soma ruri ya duba, Momi ce hakan yasa ya ki dauka dan yana kusa da gida, tada motan yayi ya karasa gida yana horn da karfi wanda ya saka mai gadi lekowa dan yasa waye ne.


Yana kallon motan yasan Senate ne hakan yasa ya bude da sauri, cilla hancin motar yayi ba tare da yayi parking dai dai ba ya fito ya nufi ciki.


Duk suna tsaye a parlon Momi na fadin. " Yaki picking fa, me ya....." Bata k'arasa ba ya shigo falon.


" Subhanallah." Kusan a tare suka fad'a, kafin Momi ta nufi gun sa da gudu tana kama shi ta soma furta. " Me ya faru da kai? Hatsari kayi ne? Kai da waye?."


Ido kawai ya zuba musu, kafin ya janye jikinsa zai haura sama ya ce. " Duk wanda zata aura ni ne ajalin shi, idan kuma ban aure ta ba to ni zan kashe kaina." Ya karashe yana shiga dakinsa ya rufe da key.


Duk sakin baki suka yi Juraij na cewa. " Ta haukata shi, saboda yarinyar nan Senate ya zare, idan ba'a aura masa ita ba Wallahi zamu rasa shi kamar yanda ya fada din." Ya karashe yana kallon su.


A hankali Momi ta tako ta zauna tana had'a tagumi, ta rasa ta ina zata fara duk kanta ya dau zafi.


Anas ya zauna kusa da ita yana dafata ya ce. " Momi the best solution shine a kai kudin auren yarinyar nan."


Salman ya ce. " Ita ta ce muku tana son shi ne?."


Ajiyar zuciya Momi ta sauke kafin ta ce. " Ita fa bata ma san yana wannan shirmen ba...." Bata k'arasa fad'a ba suka ji karar fashe-fashe a dakinsa.


A guje suka haura upstairs har Juraij na buge Momi dan sauri, buga k'ofan suka shiga yi Momi na kuka tana fadin. " Senate kar ka kashe kan ka dan Allah."


Legend's pen ***

kar agaji dani, following din dai