Page 3
*SILAR HALLACI.*!
*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*
*HIJABS CORNER BY JANAFTY*
*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design, muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*
*🅿️3*
Alu venue:Kano
"Da sauri take gudanar da komai Agogon dake manne a bangon Kichen din ta kai Duba karfe Takwas Saura mintina goma kachal cikin Hanzari ta gama juyevSoyayyan Dankalin Turawan da kwai cikin Wata karamar Kula,waje ta fita har tana neman Faduwa Saboda Sauri Cikin kayatattacen Dan madaidaicin Falon Daga gefensa akwai wani Danning din abinci karami wanda iyakarsa Zaman mutane Hudu.
Doguwar mace ce,mai karamin ciki atare da ita tana sanye da Riga da zani na wani Leshi kanta ba Dankwali sai dai wani Vail data Lullube jikinta Dashi da Sauri Take komai har tagama jera Duka kayan Breafsat din saman Dinning din Daidai Lokacin da agogon Falon ya Buga karar Karfe Takwas Daidai.
Kanta ta Dafe Lokaci daya ta kwashi Sauri Sanin Halin Hubby yanzu sai ya shammaceta ta iskeshi yagama Shiryawa kuma yace bazai tsaya ya karyaba Saboda Takwas tayi tana Shirin Nufar hanyar da zata sadata da jerin Dakunan Barcinsu ne Taji Muryan Kaka na Fadin"'Motsin wai waye nake taji ne Tun dazu ana kaf kaf da Abu..waye anan nace..?
Tafada cikin Muryan irin ta Tsufan nan,Ajiyar zuciya Abida ta Sauke kafin ta Dafe kai lokaci Daya tana Juyowa sai da ta kariso Tsakiyar Falon kana tace"Nice kaka..ina kwana ."tafada tana Ramkwafawa Kaka dake Tsaye Taci Riga da zani na Atmafa an guma Daurin nan na yanmatan Jiya sai wani Siririn Glass dake Idanuwanta,Kallo daya zakamata ka Fahimci Jiya ba yau ba,karfinta bai kare ba sai dai shekaru da sukaja domin gabadaya kanta ya cika da Farin Gashi,ammh FatarJikinta akwai Hutu da jin Dadi...
Baki ta washe tana Fadin"A"a Abida ce Ashe...Ina kwana ya shi Lafiyan Ahmadun..? Tafada tana wani kifkifata idanuwa,lokaci daya tana laluban Wajen zama kuma ga idanuwanta tardasu ganin haka sai Abida ta matso kusa ta kamata zuwa kan Daya Daga cikin Kujerun Falon Tana Fadin"Kaka kinga Kujera nan Zauna kada ki Fadi.."Zama kaka tayi tana Fadin"Nagode Abida..Allah shi miki albarka.."Da mirmishi ta amsa da Ameen kafin kaka ta cigaba da Fadin"Ai ni wlh Abida babu Abunda zan ce ma Ahmadu sai Allah ya isar min."tafada harda wani goge Hanci kamar wata yarinya.
Baki Abida ta kama Lokaci daya tana Zaro Ido Duk da ba yau ne na Farko da Kaka tataba Durama Hubby Allah ya isa ba Tun bayan Dawowarsu Daga India inda akayi mata aikin ido Kullum Safe In Ahmed yaje gaisheta sai ta Dankaramai Allah ya isa wai yakaita cikin Nasara jajayen Fata an Hada baki dashi an kwakwule mata idanuwanta masu karfi da kyau irin na bakaken Fata an sakamata na wani Nasaran wanda babu inganci..
Cikin Zolaya Abida ke Fadin"Allah ya isa kuma kaka..? Shi Jikan naki kikema Allah ya isa.."Bata rai kaka tayi kafin tace"Eh Shi jikan nawa yo Ko sama"ila keda rai ya aikata min Abunda maketacin mijin naki ya aikatamin na Mai Allah ya isa ballatana Ahmadu ke bari ma kiji Wani labari da baki taba jinsa ba Ko Tsinema Ahmadu nayi sai ya bi Duniya nice komai nashi ke Abida bari na Takaita miki Labari ko Uwarsa Zaliha bata kaini Wahala da Ahmadu ba,gashi yarintar Kazanta yayi sai fa da girmansa yayi Zaune zaune ya Kirba kashi akwance Lokacin Sama"ila ya Fita kasuwa Nice nan ke wahala dashi kina ganinsa haka nina maidashi ya zama mutum har kika ganshi kika Aura.."Dariya ta kama Abida Sai da tadara ganin Hubby Tsaye Bakin Bedroom dinsu yana Hurgama kaka Harara bai yi mgana ba sai da ya Fito Falon Lokaci daya yana Murza Hula kiran Zanna Bukar Bisa kansa.
Kaka na yar Dariya ta Bude baki tana Fadin"ai in ina baki labarin Tarihin Kuruciyar Ahmadu sai kinsha mamaki.."Cikin Takaichi yace"Don Allah kaka waya tambayeki..? Meyasa wani Lokacin kin cika Fadi ba"a Tambayeki bane .?
yafada yana Saka Hannuwansa cikin Aljihun wandon Farar Shaddan dake jikinsa Kallonsa Abida Tayi cikin Wani Salon ni zaka ma Haka itama Hararan ya jefata dashi yana Tsuke bakinshi.
Kaka Najin muryanshi tace"Ahmadu anfito..Allah yamaka Albarka..Allah yasa ka gama da Duniya lafiya.."kallonta yayi kafin yace"Ameen ammh bayan kin gamamin Allah ya isa..Allah dana sani na barki kin makance."Salati kaka ta saka Lokaci daya ta Fashe da kuka tana Fadin'Na shiga uku ni Bara"atu..Ni yanzu Ahmadu kake Kiran dama na makance..? Cikin Hade rai yace"eh mana Tunda baki son gwaninta ba.."
Cikin Kufuluwa tace"To Ta Allah bataka ba Wlh..Mugu kawai Har sai naka idon ya mutu ya bar nawa Ja"iri dan Buhu da Rabi kawai.."Ko kallonta baiyi ba ya saka kai yana Fadin"Sai kuma kiyi kaka batun yau ba nasha kamaki kina Zagina Allah inna Fusata bazakiji da dadi ba.."Kaka tace"Kar naji din..!nace kar naji dim Don Ubanka in kaso karka barni da Rai marassa mutumci.."Tashiga Fada da masifa Abida ce ke bata Hakuri Shiko Ahmed Tuni ya Dade da barin Falon Daga cikin Bedroom din yake kwalama Abida kira cikin Kakkausan murya.
Da sauri ta bar Kaka nan Zaune tana Mitanta na Fama ta karisa cikin Bedroom dinsu Tsaye ta ganshi gaban Madubi yana gyara zaman Hulan kansa ta bayansa Taje ta Rumgumeshi Lokaci daya tana kwantar da kanta Bisa Dokin bayanshi ajiyar Zuciya ya Sauke yana Bin Fuskarsa data bayyana cikin Madubi AHMED ISMA'IL JEGA kenan wanda ada yake Matashi yaro yanzu ya koma Matashin Saurayi mai kimanin Shekaru Talatin da Biyar aduniya,mai mallaki gida da mota da kuma matar Aure ta Hanyar Samun Uban gida na gari,wanda ya bashi wajen Zaman domin cin Abinci da kuma Bashi damar karo karatu saman na Nce din dayake dashi Daga Farko bayan nan kuma ya Daukeshi kamar d'an daya Haifa gefe daya kuma Yana da wani girma acikin Idanuwansa Domin ya auramasa yarsa ta cikinsa gashi hartana Dauke da Rabon da zai wanzuwa Atsakaninsu,kuma duk ta sanadin Kawu maude wanda kullum yake ma Addu"an Allah yasa yagama da Duniya lafiya.
Ajiyar Zuciya yakara saukewa Lokaci daya yana Shafa Siririn Sajen dake Bisa Fuskarsa Domin ko Daya Ahmed bai chanza ba,sai da yakara girma da Shekaru da murjewa,kana kallonsa zaka Fahimci ya samu Hutu da kwanciyar Hankali gefe daya kuma kwarjinsa da Haibansa suna nan Tare dashi yana da Izza wani lokacin har da isa Haka Allah yayishi mai Farinjini ko ina ya Shiga kowa na Sonshi kuma karyane Ahmed yasama Abu hannu baiyi albarka ba,Shiyasa Alhaji Bashir Wambai ke ji da Ahmed kuma yake alfahari dashi Shekaru Biyar da Haduwarsa da Ahmed Bunkusan Kasuwancinsa ya karu riba kuwa baisan iyakaba Shiyasa yake Kiransa Ahmed mai sa"a,shi kuma baya ganin komai sai na kokarin yadda zai Tattalama megidansa Dunkiyarsa ta karu kuma ta Bunkusa,yasan Harkan kasuwanci Sosai kuma yana da Farinjinin Costumer,bakomai yas a yake da Jarjirjewa ba sai Dalilin Silar Hallacin Alhaji Bashir agaresa Wanda har Abada bazai Taba mantawa dashi ba.
Gajiya tayi da lafewa Bisa Dokin Bayansa ta Dago kanta ta Zagayo ta gabanshi ganin ya Shiga Dogon Tunani yasaTa lakacemai Hanci tana fadin"Hubby wai Fushi kake da Abunda kaka tayi yau kuma..? Kallonta yayi Lokaci daya yana lumshe ido kafin yace"Ko Daya me kika gani..? Lau da ido tayi Lokaci daya tana gyaramai Botiran gaban Rigansa take Fadin"Naga Fuskarka ba Walwala ne.."Dan Mirmishi ya saki kafin ya saka hannu ya Riko Duka Kafadunta yana Fadin"Ko daya Ba kaka bace ta batamin Rai ba..Kece..! Domin in har Dabi"un kaka na batamin rai da Tuni Hawan jini ya kasheni kece kike bani Haushi Swestheart.."
Yafada yana kallonta ido cikin Ido Lamgwabe kai tayi bata samu Zarafin mgana yace"Karki ce min komai Abida ki Duba Halin da kike ciki..Bazaki bari na saka Umma ta samo mana wacce zata Dinga taimaki miki ba kin gwammace kiyi ta Wahala har wani Abu ya sameki keda Abun da ke Cikin ki.."shgawabe Fuska tayi tana Fadin"Haba Hubby nidai nace abar mganar wata yar aiki..Ni zan iya komai da kaina ai ba gobe ko jibi zan Haihu ba infact ma sai nan da wata shida..Ni bazan iya zama ina kallo wata yar aiki na giftawa tsakanin Mijina ba kafi kowa sanin ina kishinka bazan juri ganin wata acikin gidanan ba bayan ni da kaka ba..."kura mata ido yayi kafin ya saka Hannu yana Shafa Fuskarta lokaci daya yake Fadin"Nasani Sweetheart ammh abunda nake so ki gane ni Ahmed naki ne ke kadai bawata mace data isa ta samu kyakyawan Kallo daga wajena Sauran matan Duniya Duka maza nake kallonsu ke kadai ce nakeji kuma nake iya gani.."
Ya karishe fada ya sakarmata Kiss Bisa kanta da Sauri Tafada Jikinsa Shi kuma ya saka Hannuwansa ya Rumgumeta yana Sauke Numfashi sun dade ahaka kafin ya dago da kanta yana Fadin"Na makara fa Madam...I hv to go.."
Kiss ta sakarmai Bisa Kumatunsa tana Fadin"oya muje kayi Breafsat.." bai mata mgana ba sai da ya Dauko karamar Briefcase dinsa da wayarsa Lokaci daya yana Fadin"Bazan tsaya yin Breafast ba Sweet,ki hadamin komai cikin kwando in na isa office na gama abubuwan gabana sai na karya.."cikin Sauri tace"angama Ranka ya dade.."Tafada kafin ta fice daga Dakin da Sauri ya Bita da kallon Sha"awa da kauna wayarsa ya kurama ido yana Neman Layin Abba ammh har ta katse bai Daga ba, daya kara kira sai kuma yaji an kashe wayar sororo yayi yana Bin wayar da kallo Cikin mamaki bai samu Zarafin mgana ba Abida ta shigo dauke da Kwandon Abinci irin mai Zip din nan,shake da flks din Abinci dana Ruwan zafi sai kayan tea da Buredi,ta tsaya gabanshi tana Fadin"Ready Sir.."
Dagowa yayi yana Fadin"Nagode Madam.."yafada yana kokarin karban kwandon Hannnunta sai ta make Hannun Dagowa yayi yana kallonta kafin yayi mgana ta Rigashi da Fadin"Barni na samu ladanka yau da Safe Tunda ka Hanani wanchan ladan nayi maka wanka da tayaka Shiryawa.."Mirmishi ya saki Har Hakoransa Farare suka bayyana waje Kumatunta ya Duka ya Sumbata yana Fadin"I love u..."Lumshe ido tayi kafin ta Bude tana kallonsa Cikin Wata murya mai cike da amo da Gardi tace.."Love u so much Hubbyna..."
Hannunta ya Riko suna ma Juna Mirmishi yana gyara zaman Jakar Hannunsa bayan ya saka wayarsa Aljihu yana Fadin"kinga fa Abba nakira da farko ba"a Daga ba na biyu kuma sai naji an kashe wayar.."kallonsa tayi daidai suna Fitowa daga Bedroom din kafin tace"hmm.ai bazaka sameshi ba jiya Anty Adama da mukayi waya take Fadamin yar gold din nashi ta Shigo gari.."
Sai da suka kariso Tsakiyar Falon inda Kaka ke Zaune ta kurama Katon Talabijin dake manne abangon Falom kamar tana Fahimta ido,Ahmed sau daya ya kalleta yana fadin"Wai gimbiyar Abba kike nufi,metazo yi kuma kano."?Abida tace"wai hutu tazo..Kasan ita yar Hutu ce sai Abunda tace shi Abba ke yi.."
Dariya yayi yana Fadin"Haba dai...Kawai dai Abban naji da ita ne,Niko kinga Tunda nake banta ganinta ba sai dai labarinta kawai nake ji a bakin ku da bakin Abba.."Tabe baki Abida tayi kafin tace"Meye kakeson ganinta..? Bawata babba bace domin bata wuce Sa"ar Anty Nabila,baka taba zuwa gidan Abba na State Road ba lokacin kuma tazo Hutu.."Kansa ya kada yana Fadin"Eh..Ammh banganta ba Falon baki na tsaya muka gama mgana da Abba na Tafi gaskiya ban ganta ba.."
Abida ta kada kai tana Fadin"Miye ma na wani son ka ganta wai..? Tafada cikin Bata Fuska Dariya yayi yana Fadin"Miye kuwa..Allah huci Zuciyar gimbiyar matan Ahmed.."Dariya ta saki tana kallonsa kaka dake gefe tana kallonsu tana Tabe baki gefe daya kuma tana Hararan Ahmadu bai kalleta ba yace"Kaka ni zan Fita..".
Baki ta washe kamar gaske tana Fadin"Ahmadu an fito..? Ya gyada kai yana Fadin"Eh kaka.."mikewa tayi tana Fadin"madallah nace ba..ko zaka mikani gidan Maude,zaman Shurun ni ya isheni Wlh.."Kallonta yayi kafin yace"A"a ni kam ba inda zan kai ki Kaka na makara in kin matsu ki Fita ki hau adaidaita.."kallonsa tayi tana Fadin"au haka kace ko Ahmadu..?kai tsaye yace'Eh lokaci daya yana Tsuke baki.."
Kaka tace"toh sai me..? Ka dade baka Tafi ba kafi jirgi tashi karewarta kenan Dadin Abun ma Allah yabani lafiyan kafa babu inda bazan iya Takawa da Kafata ba Ehe.."Bai damu ba ya kama hanyar Barin Falon yana Fadin"Eh dama bance karkije ba...Motatace dai yau banyi Niyyar ki Shiga ba Fakat.."Cikin Takaichi kaka ta saka kuka tana Fadin"Allah yajikan Sama"ila da Rahma Lokacin yana Raye bai taba sabamin ba ammh yau ya mutu ya barni da dan jakar uban yaronan Wlh Ahmadu ka Fita daga idona na Rufe.."yana jinta yayimata banza sai ma Abida da ya tsaya yana cema"Bani ki koma Daga nan.."yafada Fuskarsa ba walwala
Mika mishi tayi bayan ta Rusuna,lokaci daya tana Fadin"Na tuka kaka muje gidan Kawun mauden anjuma.."kai tsauye yace"A"a ban amimce ki taka ko nan da kofar gida ba..Ki koma ciki na Tafi sai na dawo..kaka sai na dawo.."yadaga murya yana Fada Duk da Tsiyan da Suka gama sha haka ta Bishi da addu"ar dawowa lafiya ya Fita daga Falon yana yar Dariya kaka in ba haka yake mata ba sai ta batamai Lokaci da Rai abanza awofi.
Haraban gidan ya Fita wanda yake Dan maidaidaci yana Fitowa Ghali mai magadinsa ya Rugo da gudu ya zube yana gaisheshi cikin Fara"a ya amsa yana Fadin"Ghali muntashi lafiya ya aiki.."? Ghali megadi ya amsa da Fadin"Alhamdulillah yallabai.."yafada yana karban kwandon Hannunshi lokaci kuma Ahmed ya Riga ya bude Booth din Wata bakar mota dake pake aharaban wajen Accord ce baka sai wata kalan ja kiran piagion 607.haraban gidan bashi da wani girma sosai domin bai wuce a kara mota daya ba Gurin ya cika gabadaya.
Sai da ya Fara bude bangaren mai Zaman banza ya ijiye Briafcase dinsa kana ya koma Bangaren Direba ya Bude ya Shiga,ya zauna Wayarsa ya Fito da ita daga gaban Aljihun Gaban Rigansa,ya jiyeta saman jakarsa Set belt ya Daura kafin yama Motar key yamata Ribas Ghali ya Budemai Get ya Sulala waje,bayan ya Dagama ghali megadi hannu wanda ke Binsa da addu"ar dawowa lafiya.
Sai da ya Daidaita zaman Tukinsa Bisa kwalta kana ya sakarma motarsa nashi gudu Yanayi yana Duba agogon Fatan na kamfanin, Rado dake daure atsitsiyan Hannunsa takwas da Rabi gabadaya ranshi ya baci bayason african Time kuma ya Tabbata yanzu haka Nura Manaja yana chan yana jiransa Karamin Tsaki ya saki Daidai lokacin da yakawo Zoo raod inda yayi kwana ya zuba Hon a wani Rantatsen Ginin Bene mai kyau da Tsari wanda Daga sama wani Katon Tambari kema mutane maraba mai Dauke da WAMBAI SHOPPING MALL,katon waje ne mai Dauke da kowani bangare babu Abunda ba"a saidawa awajen Wambai Shopping mall yana cikin manyan manyan mall din Alhaji Bashir wambai wanda yake ji Dashi anan office din Ahmed yake Yafi yawan zaman awajen duk da yakan Leka sauraran wajajen yana Duba abunda ke Tafiya duk da Suna da ma"aikata Fiye da Dari Biyar akowani waje bayan kuma Kananun Shagunan dayake dasu a kasuwar wambai da kwari.
Da hanzari Security din wajen masu sanye da Uniform suko suka wangalemai get suna mai barka da zuwa Hannu kawai ya Daga musu kafin ya Sulala da motarshi inda aka Tanada domin parking Space,yana fitowa daga motar a hanzarce ya Bude kofar mai zaman Banza ya Dauko karamar Jakarsa da wayarsa Lokaci daya ya Zurata aljihu ya nufi bayan Booth ya dauko kwandon Kayan karyawansa ya Rufe kenan sai ga wani matashi ya Rugo da gudu yana Fadin"Barka da Zuwa yallabai.."
Waigowa yayi yana Fadin"A"a Sani.! Ya amsa yana karban Jakar Hannunsa da kwandon Abinci yana Fadin"ina kwana yallabai.." ya amsa yana gaba shi kuma yana Binsa abaya lokaci daya yake Fadin"Sani Nura manaja ya iso kuwa..?
Sani yace"Eh ranka ya Dade ya dade da zuwa.."kai ya jinjina bai kara mgana ba ta baya yabi saboda bayason mutane su Tsaidashi ammh duk da haka sai ya Dinga haduwa da wasu suna tsaidashi suna gaisawa bayan wanda yake Dagama Hannu har suka Shiga cikin wajen yallabai kawai ko Ranka ya dade ke Tashi,steps yafara takawa zuwa office dinsa Sani na biye dashi Sai da suka hau saman Benen kana ya Tura kai cikin wani kayattacen Office masinjansa dake Zaune gefe ya mike da Sauri yana mai barka da Zuwa bai amsa ba illah kai daya Daga yana Fadim"Ka amshi kayan Hannun Sani ka Shigarmin dashi ciki,kai kuma sani ka koma kaje kace ma Manaja na Shigo.."
Daga haka ya sakai cikin Uwar Dakin Office din nashi Falon Kujeru ne kadai da Tibin kallo wajen zaman baki ne da kuma Aikin masinja ,daga ciki ne wajen zamanshi yana Shiga ya Zauna Daidai lokacin da iliya masinja ya Shigo,kan karamin Firizan dake Gefe ya Dora kwandon,jakar kuma ya Zubemai Bisa Babban Tebur din Dake gabansa ya Fice Wayarsa ya ciro Daga gaban Aljihu ya ijiyeta saman Tebur din lokaci daya yana jawo Jakar Briecase dinsa ya Fito da System dinsa da wasu Takardu,Hulan kansa ya maida baya ya kunna System din Lokaci daya kuma yana Duba takardun gabanshi manaja yayi sallama ya Shigo.
Bai dago ba illah ya amsa mai lokaci daya yana Fadin"Hv a sit Manaja.."da Sauri wanda aka kira da Manaja ya samu kujeran dake Kallonta ta Ahmed ya Zauna, sai da ya Dauki Tsawon Mintuna biyar yana Duba Takardun gabanshi kafin ya Dago Cikin kulawa ya mikama Manaja hannu yana Fadin"Ina kwana Baban iman."Dariya manaja yayi yana bashi hannu sukayi Musabaha lokaci daya yana Fadin"Lafiya lau Angon Abida.."Hararansa Ahemd yayi kafin yace"Eh fadi ka kara ba gatse bane angon Abida nake.."Dariya suka saka gabafaya kafin Manaja ya Fito da wata bakar Leda cike da kudi ya Tura gaban Ahmed lokaci daya da wasu Takardu yana Fadin"Na turamaka Sauran bayanin ta email dinmu.."
Kai Ahmed ya gyada yana Fadin"Zan Duba yanzu Manaja Aikinka na kyau in nagama Duba komai zan yi mgana da Abba abun da kenan zamu yi mgana ta waya,yanzu Abunda za"ayi shine ka Dauki kudin nan ka samu accounter ku Shigar da duka bayanan kudaden,ku Fitar da Riba,da sauran Abubuwan da aka saba D rest kuma sai ku tura zuwa Asusun Abba zan kirashi ta waya.."Kai manaja ya jinjina kafin yace"Shikenan Ranka ya Dade ammh Wambai Store fa kaya sun yi kasa na kira Alhaji ban sameshi ba shine nace bari in nazo sai mu Tattauna.."
Kai Ahmed ya Dafe kafin yace"Kash..Wlh Jamilu yamin mgana Shekaranjiya,Kuyi hakuri Kayan suna tafe cikin Satin nan Jiyama Dauda yakirani daga kasuwar kwari Shagon Sarin Lesuma yace kaya sun yi kasa,duka yanzu zan kira uwaisu naji tsaikon mai aka samu har yanzu kaya basu iso ba.."Mikewa Manaja yayi bayan ya Dauki Ledan Kudin bai samu zarafin mgana ba Telephone din dake saman Tebur din Gaban Ahmed ta Dauki Ruru,yana duba wasu Takardu bai dauka ba sai aka kara kira yadago yana Dagama Manaja hannu.
Dagacham Bangaren Masinja yace"yallabai waya ce akayi da Shashen shago,wai ga wata mata nan tazo siyayyah ammh ta bada dokar duk wanda ke cikin mall din ya Fita sai in tagama Abunda zatayi tatafi sannan kowama zai iya Shiga..."Cikin Kufuluwa Ahmed yace"Stupid....Wata mata ce..? Cikin girmamawa yace"Bansani ba yallabai.."Tsaki yaja kafin yace"Tell dem karsu dakatar da kowa in bazata iya Shiga ba ta iya karawa gaba mu nan wajen..Na kowa da kowane Talaka da mai kudi.."
Daga haka ya kife wayar Manaja ya kallesa bai samu zarafin mgana ba Ahmed yace"wlh wasu mutanen basu da Hankali ka Dubafa Baban Iman wai wata matace tazo siyayyah ammh wai sai kowa da kowa ya Fita kana zata Shiga kuma ba wanda zai Shigo sai tagama tatafi..kaji Rainin Hankali.."
Manaja yace"Ikon Allah..."Ahmed ya gyara zama kenan wannan karon wayarsa ne ta Dauki meman agaji yana Dubawa yaga Nasir manaja ne cikin Sauri yadaga yana Fadin"Manaja ya akayi ne..? Cikin girmawa yace"yallabai sai fa ka Fito ga matarnan sai Gayama ma"aikatanmu mgana take tana Fadin duk karshen aikinsu yazo..Kuma so take ta ganka da idanuwanta dakace kar abi Dokarta.."Mirmishin Takaichi ya saki kafin ya mike yana Fadin"Gani nan zuwa zata gane bata da wayau."Daga haka ya katse Kiran yana Fadin muje Manaja wata mara Hankali ce tazo mana nan wajen zata watsama Kasuwanci muje na ganta na kuma ga dame take takama..
Wayarsa kadai ya Dauka ya Fice Manaja yabi bayanshi Rumgume da leda shima yana son ganin wata Matace wannan ko kuwa wata Sarkin karfin Halin ce.
*Aisha alto.*
*Janafty*