SILAR HALLACI

Page 4

by @jamilaumarjanafty

*SILAR  HALLACI*!

*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*


*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*

*Sanyi flusher!* 
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*. 
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*

*Tightening set na hade mace ta  dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.

*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*

*Muna da gimbiyar zabuwa  da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.

        *🅿️4*

"Ranta in yayi Dubu yagama Baci na irin Wulakantatan da ake Niyyar yi a ma"aikatar mijinta,Cikin Fushi ta juya baya tana kallon Motar da tazo da ita,wanda  Direbanta ya tukota,waya ta ciro cikin karamar jakar dake Hannunta   wata faskekiyar waya ta zaro cikin Sauri da alamun Fushi ta lalubo lambar da zata kira ta kara kunni Sauran ma"aikatan suna daga gefe suna kallon Ikon Allah cikin Fushi ta Fara mgana da cewa

"Alhaji dama Ashe duk ma"aikatan da ke dauka marasa mutumci ne bansani ba..?Alhaji Bashir dake zaune falon Hajiya Rabi yayi Saurin mikewa yana Fadin"Meya faru ne gimbiya..?cikin Fada tace'Miye ma bai Faru ba Don Tsabar Wulakanci kamar Ni nazo Shopping mall dinka a hanani yin Abunda nake so..? Saboda nace ina Bukatar kowa ya Fita sai nagama Abunda zanyi na Tafi kana wani zai iya Shiga Shine wasu kananan kwari ke gayamin mgana har kiran wani suke yana bada odar in bazan Shiga ba sai dai na kara gaba.."Tafada tana wani jijjga jiki cikin rawan jiki dana baki Alhaji ke fadin"Haba gimbiya Waya isa yayi miki iko da wannan Wurin..?basu sam cewa Dani da komai nawa muna karkashin ikon ki bane..? 

Baki ta tabe kafin tace"oho inaga baka Taba sanar dasu bane...Sai ka kirasu ka sanar dasu matsayina ko nasaka duka su Zama korarru musamman ma wannan Banzan dake ciki yake bada Umarni.."Cikin lallashi yake Fadin"Allah huci Ran Gimbiyata Haba Sami na..kiyi hakuri kece da Zan Fita baki gayamin zaki Fita Siyayyah da ba sai ma kin Wahalar da kanki ba,Har gida za"a kawomiki duk Abunda kike Bukata.."Tsaki ta saki tana Fadin"Ai bamu taba Haka dakai ba..na In zan fita anguwa sai na Sanar dakai ba,Ka kira kowaye ka sanar dashi ina son ganinshi yanzu agabana.."Cikin Rawan murya yace"Hakane Bari na Kirashi inaga Ahmed ne mijin Abida.."

Sanda ya kira Sunan Ahmed sai da Zuciyarta ta amsa cikin Wani yanayi tace"Ahmed.... ? Eh Ahmed mijin Abida mana Baki sanshi ba ammh ai kina jin Sunansa abakina shine Wakilina a Duka Harkan kasuwancina"Baki ta tabe kafin tace"Koma mijin Rabi ne ba Abida ina son ganinshi yanzu yanzu nan..."Daga haka ta yanke Kiran ta bar Alhaji da Zufan goshi Cikin mamaki Hajiya Rabi ke kallon sa kafin tace"Wai lafiya Alhaji..?

Yana lalubo lambar Ahmed yake fadin"Ina fa lafiya gimbiya taje Siyayyah Shopping mall dina sun hanata shiga wai sai dai in zata shiga tare da mutane ita kuma kin santa bata son hayaniya shine tace tana bukatar kowa ya Fita sai ta gama toh kinsan Ahmed akwai zafin Zuciya inaga shi ya bada Umarni kar abarta ta Shiga batare da yasan Gimbiyata bace nasan daya sani bazai fara ba.."Galala Hajiya Rabi ta bishi da kallo Daidai Lokacin dayake saka wayarsa bisa kunni cikin Takaichi da mamaki take Fadin"Yamin daidai wlh...Ita yar gidan Uban wacece da zatace Kowa sai ya Fita zata shiga tayi Siyayyah..? Aiko yar Shugaban kaasa,tana shiga waje kuma ta cukuda da mutane ma ba"a ganeta ba balle ita yar Yariman kashi..'

Wani kallo yake ta watsa mata kafin ya kama hanyar Barin Falon Daidai lokacin da Ahmed ya Daga wayar yana fadin"Ina kwana Abba.."bai tsaya amsa gaisuwan nasa ba yafara fada yana Fadin"Kai Ahmadu kana da Hankali kuwa..? Gimbiya ce fa tazo ta kuma bada Umarni tana Bukatar kowa ya fita sai ta gama Abunda takeyi ta tafi kana kowa zai iya Shiga kuma domin Rashin mutumci sai kuka hanata shiga Kasan wacece kuwa..? Cikin mamaki Ahmed yace"Abba wacece Bansanta ba..?

Cikin Haushi Abba yace"Gidanku nace Ahmed...Samiha ce fa gimbiyata.."Da Sauri Ahmed yace'Oho Abba ai bansani ba ammh kuma tazo tace duka costumer su fita waje kana ganin daidai ne Abba.."inda Ahmed na kusa dashi ba abunda zai hana bai kasheshi da mari ba cikin Bacin rai yace"Bansani ba nace...Mallam maza kaje ka bata Hakuri kuma abi Umarninta duk Abunda tace shine za"ayi.."

Cikin mamaki Ahmed ya bude baki zaiyi mgana Abba yace"Kaji Abunda nace ko..? Cikin Sanyin Jiki Ahmed yace'Naji Abba za"ayi yadda kace.."Dan sakin Rai yayi yana fadin"yauwa ko kaifa Ahmed..ka bata hakuri kaji ko..? Numfashi ya saki yana fadin"Shikenan Abba.."Dariya yayi yana Fadin"Allah maka albarka Shiyasa nake sonka akwai Hankali kaji sai hakuri nima Hakuri nake da ita.."Saboda takaichin Abba dakyar ya iya amsawa sukayi sallama Daidai lokacin da suka karisa Fitowa haraban  mall din manaja na binsa abaya,ajiyar zuciya ya sauke yana karema Matar kallo wacce ke Tsaye jikin Motarta prado baka ta juya baya Hannuwansa ya Tusa cikin Aljihun Shaddar dake Jikinsa yana kallon Manaja yace"Wai Ashe Amaryan Abba ce.."

Ido Manaja ya ware yana Fadin"Bala"i...Matarnan Wlh bata da Mutumci tasa Yallabai ya kori ma"aikata dayawa..Bala"in Tsoronta yakeji kamar wanda ta asirce.."Ajiyar Zuciya ya sauke kafin yace"Yanzu ma hakuri yace na bata kuma abi Umarninta ga duk Abunda tace.."Baki Manaja ya Rike kafin yace"yanzu kai din ne zaka bata hakuri..? Koda yake  shi kanshi Yallaban hakuri yake bata yana mata Biyayya kamar itace mijin fa.."Kai ya kada kafin yace"Mudai karisa..ya zamuyi Allah dai ya kyauta.."yafada suka Fara takawa zuwa wajen da Samiha take Tsaye ta juya baya tana Latsa wayar Hannunta.

Sai da suka zo daidai wajen kana Ahmed ya saka baki ya kira Sani ya Rugo da gudu yazo yana Fadin"Gani Ranka ya dade..'Cikin muryansa din nan mai cike da Haiba yace"Ku lallabi Costumer din mu dake ciki ku basu hakuri,su Fito in tagama tatafi sai kowa ya Shiga ka gayama Nasir Manaja.."kai ya gyada kafin ya tashi ya Shiga cikin mall din da Sauri.

Karisawa yayi gabda da ita kafin yace"Amh..Hajiya kiyi hakuri bamu san ke bace yanzu kowa zai Fito zaki iya shiga.."Yafada cikin Tsare gida Yana gama Fadar haka yajuya yana Fadin"Kowa ya koma bakin aikinsa..Manaja muje.."yafada yana kallon Ma"aikatan da suka Taruwa awajen kamar amafarki taji wata murya wanda ko Mutuwa tayi ta dawo Zata fadi wanda ya mallaki wannan muryan mai cike da iko da Takama da Haiba da Izza jitayi kamar Kunnuwanta na mata amsa kuwwa da Sauri ta waigo lokacin har Ahmed ya juya sun Fara Tafiya Shida Manaja bayanshi ta fara Hanga yanayin Tafiyarsa da komai irin nashi ne Shekara goma bazai saka ta iya manta komai nashi ba,yadda ta haddace komai nata haka ta haddace komai nashi cikin Wani Sauri ta Fara taku da Takalmanta mai Tsini tana Fadin''Malam dan Jimana.."tafada cikin Sanyayiyar Muryanta wanda Shekaru basu chanzata ba.

Tana fadin haka ya Tsaya cak Shima yana Tunanin kamar Yasan wannan Muryan sani kuma bana wasa ba Muryan ta kasance tana mai amsa kuwa acikin kunnuwansa Shekarun baya da suka Wuce yana Tunanin kila kama ce ta murya cikin Sanyinsa da kuma wani aji ya waigo yana Fuskantanta,Ido hudu suka Hada da juna wanda yasa Zukatansu suka Buga atare,Ido ya Waro cikin mamaki itama Haka tayi Lokaci daya tana ja da baya Shekaru goma basu ga juna ba ammh kuma kammanin kowannensu bai bacema junansu ba Ahmed din data sani a baya Matashin yaro ne,Yanzu kuwa Ahmed din dake gabanta Matashin Saurayi ne mai kimanin Shekaru Talatin da Biyar aduniya yayi kiba ya kara kyau da Natsuwa ga Haiba da kwarjinin data sanshi dashi Tun Dadewa kallonsa take daga sama Har kasa tana nunashi da yatsa bakinta yakasa Furta komai sai Manyan idanuwanta da suka Tara kwallah.

Shima Narkakkun idanuwansa ya saka yana karemata kallo Samiharsa daya sani abaya yarinya Danya Sharaf mai Shekaru 19 aduniya,ammh wannan Samihan dake gabansa ta zama Wata babban mace ta kara wayewa da Budewar ido Duk da Shekaru sun ja kimamin Shekarunta na Haihuwa 29 da tara kenan,Kudi tare da Hutu sun sa tazama wata irin mace mai ji da komai na wayewar Rayuwar Duniya,Tunda ga Takalmin kafafunta yakekallonta tana sanye da wani Milk din Takalmi mai Wasu Duwatsu daga samanshi jikinta kuma sanye da wata bakar Abaya ta kirar Armani mai Stone din Milk suna daukan ido tayane kanta da wani Vail Milk colour shima mai Adon Duwatsu,Hannunta kuma Wasu zobban zurfa ne guda biyu,wanda ta sakalo karamar Milk din Jakarta itama mai adom Duwatsu,wayarta na sagale ahannunta wanda yasha adom Lalle ko ashekarun baya yasan Samiha yar gayu ce ammh wannan karon komai nata ya zama na musamman ne.

Gabadaya yadda suka Tsaya suna karema juna kallo ne yasa Hankula suka fara dawo kansu manaja kuwa baki ya saki da Hanci yana kallon Ikon Allah ganin Haka yasa Ahmed yayi saurin Shanye mamakinsa na ganin Samiha alokaci da kuma ayanayin da kuma bai zata ba,Saurin kauda kanshi yayi lokaci daya yana Basarwa Ganin haka yasa Samiha ta fara taku cikin Wani salon Wahainiya zuwa gaban Ahmed tana Fadin"Gaskiya ce ko kuwa dai irin gizonka dana saba gani ne Ahmed.."?tafada lokaci daya tsayawa agabanshi  kafeshi tayi da Narkakan Idamuwanta da suka dade cikin mayen sonshi.

Dan ja da baya yayi Lokaci daya yana saki Dan mirmishin yake yana Fadin"Ba gizo bane Samiha nidin ne dai Ahmed Isma"il Jega...Bantaba zaton zan kara ganinki ba arayuwata samiha ashe ma kina kusa dani Bansani ba.."yafada yana kokarin kauda kanshi da irin kallon datake Jifamshi dashi Mirmishin Farinciki ya Subuce ma Samiha Lokaci daya kuma sai ga Hawaye ta kalleshi ido cikin ido tana Fadin"Allah nagode maka...Daka dawomin Da Farincikina adaidai Lokacin dana cire rai da ganinshi...Bana gayamaka ba Ahmed zaka dawo gareni ko bayan kowani dadewar Lokaci..Na tabbata zaka dawo gareni ina da yakini mai girma da Muradi akanka.."Takarishe fada wasu hawayen na Kara zarya Bisa Fuskarta Saurin tareta yayi da Fadin"Hmm haka dai kikace Samiha..? Ashe kuma Abba Kika Aura tun wanchan Lokacin..? Baiyi zamu hadu bane nasha zuwa ganin Abba in kikazo Hutu nan gidanshi na State road ,Allah ya sake hadamu amatsayin Surukan Juna Kila dama Abunda Allah ya Boye kenan tsakaninmu  bamu sanii ba.."Yafada yana kokarin kara matsawa saboda ganin yadda take kara matsowa kusa Dashi Nunashi tayi da yatsa tana Fadin"Kenan kai ne Ahmed Din da Alhaji ke yawan Mganarka..?

Kai ya dagamata lokaci daya yana Fadin"Eh nine Ahmed Din da kikaji Abba na mgana kuma Mijin Abida ba.."yafada yana kallon Kwayar idanuwanta wanda Kwallar suka kwanta asamansu,Wani kallo ta rika jifanshi dashi kafin tafara taku daya bayan Daya takara matsowa gabanshi tana mishi wani kallo mai cike da ma"anoni dadama Shima kallonta yake ammh cikin Zuciyarsa cike da Fargaba Domin samihan dayasani ba itace bace yanzu agabanshi ba wannan tasan Duniya da duk Abunda ke cikinta.

Wayarta ta Daga wajen Fuskarsa Tana Fadin"Ashe kai ne Ahmed din Mijin Abida...?"Tafada cikin Wani salo mai cike da tarin Tambayoyi,Saurin waigawa Ahmed yayi yaga idanuwan Ma"aikatan wajen na kanshi harda Security da masu shigowa ma Da hanzari ya kara jan baya yana Fadin"Eh nine..Ki shiga kiyi Abunda zakiyi kinga mun tsaida mutane..Sai anjuma manaja mu karisa.."yafada da sauri Lokaci daya yana Riko hannun manaja suka fara tafiya zuwa inda suka Fito ammh a hakikanin gaskiya Jikinsa Rawa yake ko waigowa baiyi ba har suka shige ta kofar baya inda suka fara Haura steps kana ya saki hannun manaja yana Fadin"Baban iman ka wuce office din accounter yadda kukayi zamuyi mgana.."Daga haka yayi saurin Rigashi haurawa ya Shige Office dinsa Zuciyarsa na wani bugawa.

Manaja yayi sansarai yana bin Ahmed da kallo cikin mamaki yana Tunanin dama Ahmed yasan Amaryar Alhaji ne,.? Daga kalamansu zaka Fahimci sun san juna da dadewa..? Ganin bai samu amsar tambayan nashi bane ya saka ya kada kai zuwa Office din Accounter zuciyarsa cike da mamaki da al"ajabin abunda ya faru shiko Ahmed yana Shiga Office dinshi yacema Masijansa kada ya bar kowa ya Shigo zai yi wani aiki Saman kujeransa ya koma ya zauna Lokaci daya yana ciro Hulansa wanda Zufa yagama wankema Fuska,kansa ya dafe da Hannu biyu yana fadin"Innalillahi wa"inna illahirraju"un...Meya dawo da Samiha Rayuwata a karo na biyu bayan Zuciya da Raina sun gama mantawa da ita.? Why samiha..? Meyasakika dawo Rayuwata adaidai Lokacin dana gama cireki araina Rayuwata tafara tafiya daidai..? Yafada yana dago kansa wanda idanuwansa suka kada sukayi wani jajir.

Itakuwa Samiha Har Ahmed ya bacema ganinta tana kallonsa sai da suka shige ta kofar baya ne kana ta iya sakin ajiyar Zuciya ta juya tana Fadi afili.."Ahmed dina ne ya zama mijin wannan banzar yarinyar Abida..? Hmm lalle tayi kuskuran Auran min miji SAMIHA tatafi kuma gashi yau samiha ta dawo..Nayi alkawarin wannan karon sai na cika alkawarina na mallakan Ahmed a matsayin Abokin Rayuwata na Har Abada.."Tafada tana cije baki Lokaci daya kuma tana saka dan Yatsanta ta dauke hawayen Idanuwanta.

Tajuya tafara tafiya kenan Sani ya Biyota yana Fadin"Hajiya kowa fa ya fita kuma an dakatar da kowa da shiga sai kin Fito.."Bata waigo ba illah hannu data dagamai tana fadin"zuwana yagama amfani Daga wajen nan..So zaku iya cigaba da Harkokin ku.."Daga haka ta wuce ya Bita da kallo da sauri Direbanta ya Fito ya Budemata gidan Baya ta Shiga ta Zauna ya Rufe da kuma Sauri ya Koma Bangaren Direba ya shiga ya Tada Motar ya zuba Hon Security suka wangale musu get suka Sulala waje da gudu kowa awajen da mamaki ya koma bakin aikinsa suna mamaki me suka Gayama juna ita da Ahmed wasu ma Tunda akace musu Amaryan Alhaji ce sukafara tsausayama Ahmed kila ya zama korarre wasu kuma suna fadin kila a ragamai Tunda Surukin Alhajin ne,kowa dai danashi Zencen Shidai Ahmed Tunda ya Shige office ba wanda yaji Motsinshi ko waya aka kirashi baya Dagawa yana ganin kiran Abida ya kasa Dauka gabadaya Kansa ne ya fara ciwo,idanuwansa Sun chanza launi,Jijiyon kansa sun mike Radau ga yunwa yanaji ammh kuma Bakinsa bazai iya cin Abinci ba,mikewa yayi kasala ta Rufeshi Kwandon Abincin da yazo dashi da Safe ya dauka da wayarsa dama key din motarsa na cikin aljihunsa hula a hannu ya Fice masinja na fadin Ranka ya dade ka tashi ne..?Ko kallonsa baiyi Ba haka ya fice zuwa Haraban Wajen,gabadaya ma"aikatan sunyi mamakin ganinsa zai tafi adaidai wannan Lokacin wanda ba Dabi"arsa ba ne  ko wani waje zashi sai ya shiga cikin ko ina ya Duba yadda aikin ke tafiya kana yace zaije ya dawo ammh yau bai ma kowa mgana ba,ya Bude Gaban motarsa ya ijiye kwandon Abinci kafin ya koma Bangaren Direba ya shiga ya kunna motar yayi mata Ribas ya Zuba Hon,sericuity Suka Budemai get ya Fice daga mall din gabadaya duk wanda aka cema Ahmed ya Fita sai yayi mamaki wasu kuwa har sun fara tunanin kila ya amshi hukunci ne.

Afirgicen ya isa gida Yana ta Zuba Hon ghali maigadi ya Zagaya Da hanzari ya Fito da karamar Buta bai ma gama biyan Bukatarsa nashi ba ya Fito yana gyara zariyan wandonsa saboda Hon din da Ahmed ke Zubawa Da sauri ya wangalemai get ya Shigo gidan da gudu bala"in kadan ya Rage bai gogi Motar Abida Dake wajen ba Saurin Dafe kai Ghali megadi yayi yana salallami da Gudu ya Rugo yana fadin"barka da zuwa yallabai.."Dakyar ya iya amsa mai bayan ya Fito daga motar Kujeran mai zaman banza ya bude ya dauko kwandon Abincin da wayarsa ya maida kofar ya Rufe hulan nashi ma cikin mota ya barta yana Rangaji ya nufi cikin gida A falon Farko yaci karo da Kaka tana Zaune tana kallo har tafara gyangadi ko kallonta baiyi ba ya nufi kichen Inuwar mutum tagani yasa ta Farka tana waige waige tana Fadin"Waye a nan.? Waye ya shigo ke Abida..'?

Take fada tana kokarin mikewa glass din idonta ya fadi kasa dama Shine karfin ganin nata,Abida na kichen tana juya Soyayyiyar Miyar kayan miyan datakeyi taji mganar Kaka ta waigo da Sauri da Niyyar da Fito daga cikin kichen suka ci karo da Ahmed da Hanzari taja baya cikin mamaki ganinsa tace"Hubby.."tace tana kallonsa Daga sama har kasa bai mata mgana ba illah Wuceta dayayi zuwa Kichen ya ijiye mata kwandon Abincinta bisa kantar Kichen din yazo ya Raba ta gefenta ya Fice da kallon mamaki ta bishi kafin ta koma ta Bude kwandon Taga babu Abunda ya taba Abun ya kara Daure mata kai da Sauri ta Fito daga kichen din Ta samu kaka na Laluban glass dinta ta karisa gareta ta dauko mata ta bata tana Fadin"Gashi nan kaka.."Kaka ta karba tana Fadin"Ke Abida wani ya Shigo gidanan..? Yanzu nan barci ya kwasheni ina farkawa naga inuwar mutum ya wuce ina ta magana banji mganar kowa ba kinsan ganin sai ahankali.."

Kai Abida ta kada kafin tace"Kaka ba kowa bane face Ahmed..Ahmed ne yashigo gidan Ransa duk abace nima ina masa mgana yayi banza dani ya shige daki.."Kaka na kokarin kafa gilashinta tace'Ahmadu..? Topha Allah sa toh lafiya nasan Ahmed da Fushin Zuciya Allah sa ba Fada sukayi da wani achan wajen aikin nasu ba.."Abida tace"Bansani ba Kaka ammh bari naje naji.."

Tafada tana wucewa da Sauri kaka na fadin"yauwa bishi muje...Wlh in wani ne ya dakarmin jikana kwara daya a duniya sai na ga Ubanshi yau..Ahmadu shi kadai gareni nake gani naji sanyi ina sonshi kawai wani Lokacin baida Mutumci ne.."Tafada tana gyara zama ta cigaba da mitanta ita kadai.

Abida kuwa da Sallama ta Shiga Dakin Barcin nasu,kwanciyar da Ahmed yayi ne ta bata Tsoro ya kwanta yayi Ruf da ciki cikin Tsoro ta karisa gareshi ta Zauna kusa dashi gefen gado lokaci daya tana sanya hannu abayanshi tana Fadin"Lafiyanka kuwa yau Hubby..? Ka fita baka jima ba kuma kadawo sannan kuma baka taba breafast dinka ba.."tafada tana kallonsa bai mata mgana ba sai ma Juya jikinsa dayayi chan bangaren cikin mamaki tace"Hubby mgana fa nake ko baka da lafiya ne...?

Cikin Fada da masifa ya waigo yana Fadin"Eh bani da lafiya..?karewarta ma chika ne akaina...Dillah malama get lost ki barni i need privency.."yafada yana sakarmata jajayen idanuwansa jikinta na rawa ta matsa baya tana mikewa idanuwanta sun cika da kwalla tace"Ni  kake kora yau kuma Ahmed..?

Cikin Tswa yace"Eh get out nace ko.."bata bari kwallar idanuwanta Sun zubo ba ta kada kai ta juya ta Fita da gudu bayan ta kalleshi ido cikin ido shima kallon ya bita dashi har ta fice Mikewa Zaune yayi wata Zuciya na Fadin"me kayi kenan Ahmed..? Kansa ya dafe yana kiran sunan Allah kafin ya zame ya kwanta rigimgine yana kallon Rufin dakin Lokaci daya Shekarun da Suka Shude na Rayuwa masu tarin kalubale suka fara dawo mai daki daki kamar wanda aka kunna ma kaset yana kallon a magijin Kallo.




*Aisha alto..*
*Janafty*