Charles 17
A katafaren parking space ɗin gidansu Mammy Dady ya tsayar da motarsa, cikin nutsuwa ya fito tare da bawa Ilham umarnin fitowa. A hankali ta fito daga cikin motar kanta a ƙasa, cikin nutsuwa suka fara tafiya. Ilham jin kanta take yi kamar ba ita ba, wani baƙon yanayi take jin yana ziyartarta, ko da suka shiga falon gidan su Mammy kaɗai suka tarar a ciki sai ƙanninta su biyu, kasancewar yamma ta yi ya sa Mammy ta sallami jama'a kowa ya kama gabansa. Cikin sakin fuska Mammy take faɗin "Oyoyo ga ƴata, ga ƴata." Ta yi maganar tana miƙewa tsaye ta je ta riƙo Ilham za ta zaunar da ita a gurin, Dady ya ce "Aunty A'isha riƙo ta mu je can ɓangaren Sudais ɗin ina son in sa da ta ne da ɗakinta, ina fatan Sudais na gida ko? Domin na kira shi a waya na sanar da shi gani nan zuwa kuma ina son ganinsa ne idan na zo". Mammy ta ce "Eh yanzun nan ya shigo yana ciki". Jinjina kai ya yi daga haka ya yi gaba Mammy ta bi bayansa. Da sallama suka shiga cikin haɗaɗin falon na sa, yana kashingiɗe saman 2star. A hankali ya ɗago da kansa fuskarsa ɗauke da murmushi ya ce "Sannu da zuwa Uncle." Dady ya zauna yana faɗin "Yawwa Sudais, lafiya dai na ganka a haka?"
"Lafiya ƙalau Uncle gajiya ce kawai"
Dady ya ce "To ma sha Allah." Mammy ta zaunar da Ilham ƙasa saman cafet, Sudais ma saukowa ya yi ya zauna a ƙasa, Dady ya yi gyaran murya ya fara magana "Alhamdulillah, dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah maɗaukakin Sarki, mai kowa mai komai, wanda ya nuna mana wannan rana ta farin ciki ba tare da mun yi tsammanin zuwanta ba. Ƴaƴana, a yau na tsaya a gabanku ne ba kawai a matsayin uba ba kawai, har a matsayin wanda Allah ya ba wa amanarku. Tun daga ranar da kuka zo duniya a hannuna kuka tashi. A yau Allah ya ƙaddare ku da kasancewa a ƙarƙashin inuwar aure, babu abin da zamu yi wa Allah face gode masa, tare da fatan Allah ya sanya alkhairi da albarka a cikin rayuwar aurenku. Ku sani aure ibada ne, kuma ibada tana buƙatar natsuwa da tsoron Allah. Ka da ɗayanku ya ɗauki ɗayan a matsayin abin wulaƙantawarsa, ku ɗauki junanku a matsayin abokan tafiyar rayuwarku. Ku yi haƙuri da juna, ku rufe laifukan juna, ku dinga yi wa juna afuwa da yafiya, domin ɗan Adam duk aziji ne, kai Sudais ka kula da matarka da mutuncinta, ka zama mai tausayi ga iyalinka. Ka zama abin da za ta samu nutsuwa da kwanciyar hankali a gurinsa, ka da ka wulaƙanta ta ko ka cutar da ita, domin Allah zai tambaye ka game da amanar da ya ba ka. Ke kuma Ilham, ki girmama mijinki, ki ba shi duk wani haɗin kai domin ku gina rayuwarku cikin farin ciki da natsuwa, ki zama mace mai haƙuri da kyawawan ɗabi'u, ki kiyaye mutuncinsa a gabansa da bayansa, ki yi masa biyayya. Idan wani abu ya taso a tsakaninku, ka da ku bari fushi da saurin zuciya ya kai ku ga aikata abin da bai da ce ba, ku zauna ku tattauna ku magance ta a tsakaninku, yanzu kun ƙara zama abu ɗaya. Allah ya sa wannan aure ya zama sanadin farin cikinmu baki ɗaya, ya sa albarka, ya kawo zuri'a ta gari. Ya ba ku ikon sauke haƙƙin junanku, ya nisantar da ku daga fitina da sharrin Shaiɗan. Allah ya yi muku albarka." Dady ya kai ƙarshen maganar yana kallon Mammy ya ce "Aunty A'isha idan kina da abin da faɗa bissimillah, duk da na ji an fara kiran sallar magriba." Mammy ta ce "Ai duk abin da zan faɗa ka riga ka faɗa, Ubangiji Allah ya kaɗe fitina ya basu zaman lafiya. Ya kawo mana ƴan dagwai-dagwai." Dady ya amsa da Amin yana miƙewa tsaye, godiya sosai Sudais ya yi musu, sannan suka fita gaba ɗaya har Sudais ɗin yabi Dady suka tafi masallaci, ya rage Ilham kaɗai suka bari a gurin, tashi ta yi ita ma ta shiga ɗayan bedroom ɗin wanda ta san ba da shi Sudais yake amfani ba ta yi alwala ta tayar da sallah.
.....
Yinin yau gaba ɗaya cikin rashin jin daɗi ta yi shi. Zaune take saman dardumar da ta idar da sallar magariba ta rafka uban tagumi, Inna ta ce "Ke Ma'u wai lafiya kike kuwa? Ina lura da ke yau gabaɗaya cikin rashin kuzari kika yini, sai ka ce wadda a ka aikowa da manzon mutuwa."
Haka kawai Ma'u ta fashe mata da kuka hadda shasheka, sakin baki Inna ta yi tana binta da kallo. Abida dake kwance saman gadon ta ce "Yi haƙuri Aunty Ma'u ki daina kuka." Ai kamar ta ƙara kunna Ma'un, cikin takaici Inna ta ce "Ban son iskanci da shashanci, uban me a ka yi miki da za ki saka ni a gaba kina kuka? Na fara gajiya da wannan iyashen na ki, za ki sanar da ni abin da a ka yi miki ko sai na yi mugun saɓa miki?" Cikin kuka Ma'u ta ce "Wallahi Inna ni ma ban san abin da yake damuna ba, haka kawai yau na ji raina yana ɓaci, zuciyata na yi mini zafi, Inna wani abu nake jin ya tokare mini ƙirji wanda narasa ko meye?"
"To kuma shi ne za ki saka ni a gaba ki na yi mini kuka? Irin wannan ai addu'a ya kamata ki yi ba wai ki zauna kina yi wa mutane kuka ba sai ka ce wata ƙaramar yarinya." Shiru Ma'u ta yi ba ta ce komai ba, Inna ta ci gaba da mita har a ka kira sallar isha sannan suka tashi domin su gabatar da sallar.
.....
Bayan gama sallar isha Sudais na zaune cikin masallaci ya yi shiru yana tunani, kira ne ya ji ya shigo wayarsa, kamar ya share kiran sai kuma ya ɗauka ya kara a kunnensa, shiru ya yi ba tare da ya yi magana ba "Assalamu alaikum" ya ji an faɗa a cikin wayar.
"Wa'alaikussalam" ya amsa sallamar
"CEO AAA GLOBAL HOLDINGS, ashe aure ka yi yau ba mu da labari? To muna taya ka murna, Allah ya sanya alkhairi." Sai yanzu Sudais ya fahimci ko su waye. Ya amsa da "Amin nagode" daga haka ya kashe wayar.
Bin wayar suka yi da kallo ganin ya kashe, Alhaji Badaru ya yi murmushi tare da faɗin "Ya kashe wayar, yaro yaro ne. Ba dai za ka zauna a waje ɗaya tare da mace ba? Duk wannan izzar taka da ji da kan da kake za a sauke maka sune." Alhaji Hali ya yi dariya ya ce "Rabu da shi kawai, amma abin nan ya ba ni mamaki, a ka ce babu ruwansa da mata, baya kula su, amma shi ne lokaci ɗaya za a ji ɗaurin aurensa? Ko dai da ma can yana hulɗa da su sani ne baya bari a yi? Kodayake ance ƴar uwarsa, ba da shi a ka so ɗaura auren ba sai a ka samu matsala daga gurin waccan ɗin shi ne a ka mayar da auren a kansa." Alhaji Badaru ya ce "Koma dai me ya je can su ƙarata, Allah ya basu zaman lafiya. Ni yanzu tunani ya zai yi da Zuhura da ya fara zuwa gurinta?". Ɗayan mutumin da tun ɗazu yake zaune bai ce komai ba, ya dube su ya ce "Ni yanzu ba wannan ne a gabana ba, ya ake ciki ne a kan batun ginin da a ka fara? Ina fatan komai na tafiya daidai?" . Alhaji Hali ya ce "Gini na nan har an yi nisa da aiki sosai, yanzu ma haka muna so cikin satin nan mu fara fitar da sanar da sunan kamfanin nasa, muna da tabbacin za a samu customers da yawa da za su bayar da kuɗaɗensu, daga nan mu kuma sai mu fara gudanar da aikinmu kamar yadda muka saba." Ya kai ƙarshen maganar yana dariyar dake nuna tsantsar mugunta. Jinjina kai ya yi ya ce "Da kyau, ku ci gaba da yin duk abin da ya dace, wannan yaron zai gane bashi da wayo." Nan suka ci gaba da tattauna yadda za su gudanar da aikinsu a ƙarƙashin jagorancin kamfanin Sudais domin cimma wata manufa ta su.
....
Sai wajen ƙarfe tara Sudais ya baro masallacin, gidan ya yi shiru, kasancewar sauran jama'ar da suka rage duk sun tafi, Zahra ɗai ya tarar a falon zaune, "Sannu da zuwa Yaya" ta faɗa tana sunkuyar da kai ganin fuskarsa da ta yi a ɗaure. "Ina Mammy?" Ya tambaya yana kallonta, ta ce "Yanzun nan ta shiga ciki."
Bai ce mata uffan ba ya fara taka matattakalan benen. Da sallama ya shiga ɗakin, Mammy na zaune saman gado, ya ƙarasa kusa da ita ya zauna a ƙasa tare da ɗora kansa saman cinyarta. Ya ce "Sannu da hutuwa Mammyna."
Murmushi ta yi cike da ƙaunarsa, ta ɗora hannunta saman kansa tana shafawa ta ce "Yawwa angon Ilham, ya naga jikinka ya yi sanyi ko dai duk cikin angwancin ne?" Ɓata fuska ya yi ya ce "Haba Mammy ki daina faɗar haka, ba na jin daɗi ne, gabaɗaya wani irin nake jin kaina."
Mammy ta ce "Allah Sarki, da ma wasu sukan ji irin wannan yanayin idan Allah ya kai su ga matsayi irin wannan."
"Mammy"
"Na'am Sudais"
"Mammy ya zan yi da yarinyar nan? Me zance mata?"
"Jiƙata za ka yi kasha, ko kuma ka yi decoration ɗinta." Ta bashi amsa tana tsare shi da ido. Ɗago da kansa ya yi sai yaga shi take kallo, da sauri ya sunkuyar da kansa ya ce "Mammy baƙar magana ce kika yi mini?"
Ta ce "A'a fara ce na yi maka."
Shiru ya yi bai ce mata komai ba, ya dinga sauke numfashi a hankali, Mammy ta sake ɗora hannunta saman kansa ta ce "Sudais ina son ka sani yau wata sabuwar rayuwa ce za ka fara, wadda nake fatan Allah ya sa albarka a cikinta, ka sani Ilham amanar Allah ce a gurinka. Ka da ka taɓa wulaƙanta ta ko ka zalunce ta, ka riƙe ta da gaskiya da amana, domin Annabi Muhammad sallallahu alaihi wasallama ya yi umarni da a kyautata wa mata. Idan ta yi kuskure ka gyara mata cikin hikima, ka zamto mai haƙuri, ban da zagi ko cin mutunci,
Ka zama magidanci mai adalci a gidanka. Ka kula da ibadarka Sudais, domin idan dangantakarka da Allah ta gyaru, Allah zai gyara maka dangantaka ka da iyalinka. Duk wata matsala da ta taso, ku yi ƙoƙarin magance ta a tsakaninku ba tare da kowa ya ji ba, sirrin gidanka sirrinka ne, ka da ka riƙa yaɗa shi, ka da ka yi sakaci da haƙƙinta, domin za a tambaye ka game da amanar da aka ba ka. Ina yi muku fatan samun farin ciki da kwanciyar hankali na har abada."
Jikin Sudais ya ƙara yin sanyi da nasihar da Mammy ta yi masa, murya a sanyaye ya ce "In sha Allah zan kiyaye duk abin da kika faɗa Mammy, nagode sosai da sosai, Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana uwa ta gari."
Mammy ta "Amsa da Amin ya hayyu ya ƙayyum. Ubangiji Allah ya shiga cikin lamarinka." Tashi ya yi a kasalance ya yi mata sallama ya fita, bin bayansa ta yi da kallo tana murmushin jin daɗi.
A hankali ya tura ƙofar falon ya shiga, falon tsit babu kowa a ciki sai ƙamshin turaren Swiss flower air freshener, lumshe idanunsa ya yi saboda ƙamshin turaren ba ƙaramin ratsa shi ya yi ba. Ya buɗe idonsa ya fara tafiya cikin natsuwa, ƙofar bedroom ɗinsa ya buɗe, har zai shiga sai kuma ya dawo ya nufi ɗayan bedroom ɗin.
Tana tsaye a gaban madubi tana shafe jikinta da turaruka masu ƙamshin daɗi, daga ita sai wata ƴar ƙaramar rigar bacci, da kaɗan ta wuce ƙungunta, ji ta yi an turo ƙofar ɗakin. Da sauri ta juyo, gabanta ne ya faɗi ganin Sudais a tsaye yana ƙare mata kallo, ko kaɗan ba ta yi zaton zai shigo ɗakin ba shi ya sa ta saki jikinta, nan ta fara dube-duben abin da za ta samu ta kare jikinta domin rigar da take sanye da ita ba ta da maraba da tsirara.
Wani irin kallo yake binta da shi da ta kasa tantance ko na me ye. Ajiyar zuciya ya sauke a hankali ya ɗago daga jikin ƙofar. Babu shiri Ilham ta kai zaune saman gado ta saka kanta tsakanin cinyoyinta.
Amanarcool
***