26
by @gureenjoh
*Ku yi hak'urin jina shiru a satin chan ba ni da lafiya ne ina kuma barar a saka mu cikin Adu'a Allah ubangiji ya yaye mana, marar lafiya na gida da asibiti duk Allah ubangiji ya ba mu lafiya mai amfani*
Police din ne ya nufeta
"Baiwar Allah za mu je da ke division mu karɓi statement da kuma phone number dinki incase in kin tafi muna bukatar karin wasu bayanan sai mu ji daga gareki"
Ta kalleshi sai ta ɗan sauƙe Numfashi kan ta miƙe tsaye taku biyu ta yi ta ga ya shiga gabanta a hankali yana cewa officer ɗin
"We will be going together, ba za ta shiga motarku ba"
Cikin mamaki take kallonshi, me nashi don ta shiga motar 'yan sanda? Ina ruwanshi ma da rayuwarta? Juyawa police din yayi ya tafi sai ya juyo ya kalleta suka haɗa idanu kallo me kama da harara ta mishi a fili take furta
"Ina ruwanka idan ma kan motar zan hau su tafi da ni?"
Bai ce komai ba ya juya kai ya fara tafiya sai ta bi shi
"Ina fata ba za ka gama acting innocent gobe ka kalleni da zargin biyana aka yi in yi framing dinka ba don Allah ya gani ban saka ka ba ni dai"
Idan dutse ya tanka to ya tankata haka ta karaci mitarta kuma ta shiga motar tashi da tuni ya jima zaune a gaba.
Motar police din na gaba suna binsu har cikin police station duk wani bayani ta yi musu yana zaune gaban desk din kaman yadda take zaune, biro aka miƙa mata ta rubuta phone number kan ta saka hannu ya sa nashi da ta bi da kallo ya amshe.
Fararen zara zaran fingers din nashi ta zurawa idanu a sadda yake rubuta numbers ɗin har ya gama kan ta kalleshi sai suka haɗa idanu nata ta zaro tana tambayarshi da ido me haɗinsu? Ta ina layin Wayanta ya zama nashi?
Bai ce komai ba sai ido da ya kawar yana ɗan girgiza kai.
Ko da suka fito daga police station din asibitin suka koma, ana kiraye kirayen magrib dole ya je yayi sallah kan ya dawo, tana nan zaune sai ga likitocin da suka shiga kan yarinyar sun fito.
Asp din ne ya ke tambayar su.
"Ya take? Babu wani abu da ya same ta?"
Babban Likitan cikin jimami yace
"Ta fuskanci mummunan cin zarafi ta jiki da kuma fyade, kuma hakan ya yi matuƙar tasiri ga lafiyar kwakwalwarta da ta tunaninta. A halin yanzu tana cikin yanayin firgici (psychological shock), kuma ba ta cikin yanayin da za ta iya ba da cikakken bayani.
Mun fara ba ta kulawar gaggawa tare da daidaita yanayinta. Za mu ci gaba da kula da ita aƙalla na tsawon kwanaki biyu domin sa ido da kuma ƙarin bincike"
Ya ɗan ja numfashi
"Dangane da zargin fyade, za mu tattara dukkan shaidun likitanci da sakamakon gwaje-gwaje, sannan mu rubuta cikakken rahoto da za a miƙa muku don cigaba da gudanar da bincike.
A halin yanzu an ba ta magungunan da suka dace domin rage raɗaɗi, tashin hankali, da kuma taimaka mata ta samu hutu. Da zarar ta farfaɗo kuma ta samu ƙarfi, za mu ci gaba da sauran bincike da kuma ɗaukar bayaninta."
Diva ta riƙe bakinta tana ambaton Allah hakan ya sa Shehi da shima ya shiga damuwa da halin da yarinyar take ciki don duk mai imani idan ya ganta sai ya tausaya mata, yayi mamakin ganin cikar hawaye a idanun Diva ita kuwa idan akwai wani kalma da ke ɗaga mata hankali ya biyo bayan kalmar rape, ina ma za ta ga waennan mutane da kafin su je ga hukuma sai ta tabbatar ta gana musu azabar da ko mace suka gani tsirara ba za su taɓa jin sha'awarta ba.
Duk tattaunawar da ya kamata Likitan ya yi da police din waenda zai bayar a rubuce ma zai bayar, Adu'ar samun lafiya Shehi yayi mata kan ya kalli Diva da har lokacin take cikin damuwa da bai buya akan fuskarta ba yace
"let's go"
Ta kalleshi shima ita yake kallo kwarjinin da ta ji ya mata da kuma yanayinta ya sa ta kasa mishi musu sai da ta miƙe kan ya ɗauke idanu daga kanta yayi gaba ta bi bayanshi har mota, ta shiga ne kawai ba tare da ta san inda za su ba shi ya faɗawa drivern ya kai shi hotel ɗin shi har suka isa babu mai magana a motar, sai da ya sauƙa ya cewa drivern ya kaita hotel ɗinta daga nan ya juya ya shige ta bishi da kallo a ranta tana raya ji ƙarfin hali ɓarawo da sallama ko ina ruwanshi da sadda za ta bar asibitin? Shi ya kaita ne ko me? Haka dai ta gama mitarta har ta gaji kan ta yi shiru drivern na sauke ta ta wuce ciki ta adana sakon Jagaban.
Wanka ta fara kan ta rama sallolin kanta, kayan bacci kawai ta saka karamar riga da iyaka cinya ta yi waya da Jagaban kan ta kwanta Kasancewar flight ɗinta da wuri ne bata sha komai ba gudun matsala, da kyar bacci ya dauketa kuwa tsabar tunanin yarinyar nan da bata san ko sunanta ba.
Ina za su kaita? Ta ya suka sace ta? Ya iyayenta suke ji a yanzu? Duk babu abin da bata raya ba ta yi tsaki ya fi cikin kwando kan bacci ya dauketa, da sassafe kuma ta farka ta yi wanka ta shirya ta kira Bolt ta kuwa ci sa'a ta samu ya zo ya ɗauke ta zuwa Airport da yarinyar ta farka amma ta tabbatar tunda tana hannun police za su yi duk abin da ya kamata.
Babu ɓata lokaci ta gama duk abin da za tayi karfe takwas na safiyar ranar jirginsu ya ɗaga daga Abuja zuwa Kano, tana sauƙa a Airport na Aminu Kano ta lumshe idanu ta buɗe tana shakar iskar Kano da tayi kewa kwarai, murmushi ne kwance a kan fuskarta don ji take kaman ta shekara da barin jihar da ta fi wayo, tana fitowa Arrivals kuwa ta ci karo da su Shaly ɗaya bayan ɗaya sai da tayi hugging nasu dukkansu shidda suna ta murmushin ganinta itama haka.
"Barka da sauƙa Shugaba mun yi matukar kewarki"
Pascal ya faɗa Skipo da ke saka jakan ta a SUV ɗinta yace
"Ai faɗa ma ɓata baki ne Kano ya zama lami da baki a cikinsa Diva, amma tunda kin dawo komai zai koma norrrmal neee"
Suka yi dariya tace
"Na gode, ku muje"
Baya ta shiga Pablo ke driving Obafiya na gefenshi su kuma duka suna daga ciki.
Hira kawai suke suna bata labarin wasu abubuwan da suka faffaru bata nan wani tayi takaici wani ta yi dariya cikin yanayinta na yanga.
Jagaban shi kanshi yayi murna da ganinta don hugging ɗinta yayi itama ta mayar suna murnar ganin juna daga nan ta shige ɗakinta don ta huta kan a ɗora daga inda aka tsaya.
****
Waya yake da Ammiey cikin natsuwa suke tattaunawa yake sanar mata cikin wani sati ma zai dawo Kanon in Shaa Allah za su gama program din jibi akwai dai abin da zai ƙarasa wanda ba za'a rasa ba.
Ta yi masa Adu'a kan tace
"Ni ko kana ƙiran yarinyar nan da na ce kuwa? Idan ma fa baka kira ya kamata ka ƙirata ku na gaisa wa Shehi don wani satin ne za'a kai kudin aurenku"
Ya ji daaɗi da bata tsaya jiran jin amsar tambayar farkon ba don bai san me zai ce mata ba, ya amsa kawai da in Shaa Allah daga nan suka yi sallama.
Yana ajiye wayan Ammar ya ƙira.
"Ya Sheikh!"
"Ammar kana lafiya?"
"Alhamdulillah ya Abuja?"
"Alhamdulillah"
Sun fara tattaunawa kan harkokin Shehi da ya bari nan Kano sai da ya ji komai na kan tafiya lafiya kan suka shiga wata firar, shi ne ma ya ke cewa Ammar ɗin
"Ammar layin yarinyar nan nake so ka samo min"
"Wace yarinyar?"
"Amm Na'imah yeah ita"
"Ka ce min dai your wife to be"
Yana buɗe system na gabanshi yace
"Koma dai menene ni dai layi kawai nake so Malam"
Yayi murmushi yana ji Ammar na mishi barazanar idan yayi tsiya sai ya fasa samowar shi dai bai ce komai ba suka yi sallama.
Aikin da yake yi duk dare ya cigaba da yi yana mamakin yadda har yanzu ya kasa gano daga ina matsalar take, duk yadda zai yi bincike akalar akan Ammar ne amma zuciyarshi kwata kwata ta kasa yarda cewa zai aikata abu irin hakan kuma tare suke idan yana spending irin wanchan kudin dole zai sani ne, ba zai sare ba zai cigaba da binciken har sai ya gano gaskiya.
Tunanin yarinyar chan ta asibiti ya tsarga mishi hakan ya sa dole ya tuno da Diva, sai ya ɗan girgiza kai yana ƙaramin murmushi bai san me zai kira yarinyar ba samm, tana bashi mamaki komai nata ya bambanta da na mata 'yan uwanta, yadda take tsayar da Idanunta kansa kadai mamaki yake bashi har harara da mitarta sai da ya tuna ya tsinci kanshi da tunanin ko ta koma asibitin ne ko bata koma ba! Don shi bai koma din ba kaman kuwa jira yana cikin tunanin ya ji ƙira ko da ya duba number ne.
Ɗaga wa yayi da sallama bayan sun gaisa yake sanar da shi daga police station ne idan babu damuwa suna son ganinsu a gobe, shi dai bai san ta yadda zai samu Diva ba amma bai ce komai ba bayan Allah ya kai mu gobe ɗin bayan katse wayan ma bai tsaya tunanin neman ta ba ya cigaba da abin da yake.
****
Dagacin cheɗiya ne ya kalli mutanenshi da suke zazzaune ya muskuta yace
"Toh ni dai don kun ɗaga hankulanku ne amma har yanzu ban ji kaman akwai matsala kan yaranmu ba, amma saboda kawar da zargi za mu wakilta Malam Musa zai bi wannan adireshin na jikin fom ɗin ya tafi har chan Kanon ya dubo mana lafiyarsu da yardar Allah"
Kowa a wurin ya gamsu kuma ya yi na'am, Malam Musa na da ɗan ilimin boko don har NCE ce da shi yana kuma harkar tafiye tafiye shi ne kadai zai iya yi musu wannan, guzurin kudin mota da na abinci da suka hada mishi aka damka mishi ya karɓi fom ɗin yayi musu sallama ya nausa inda zai samu machine ya haye don kai shi ga inda zai samu motar shiga cikin gari zuwa Kano.