Muguntar boye
JA DA BAYA...
Book 1
Page 4✍️
Meelah Bazata
***
Nemanta suke, basu ganta ba. Kowa na mamakin, to ina ta shiga? Tun ana nema da wasa har abu ya fara girma, hankalin yan gidan duk ya tashi. An karade ko'ina ana nema.
Ayzaan hankalinsa yafi na kowa tashi. Duba ko'ina yake tare da tambayar, "Ina Inarah ta shiga to?" , gurin garden ya nufa. Can ya gano ta a garden din gidan ba alamar numfashi a tare da ita, kanta yana ta tsiyayar da jini cikin matukar kaduwa yakarasa ya dagota . Take a wurin Ummee ta yanke jiki ta fadi.
Ammee kuwa, ko motsi ta kasa, kamar ma dai ta suma a tsaye.
Haka aka dauke ta da gudu aka kai asibiti da ita. Ba wanda yayi tunanin zata rayu, domin kowa ya dauka ta mutu.
Ayzaan kuwa, a ranar ne yayi kuka, kukan da ya ba kowa mamaki. Domin kuwa sam baya kuka, ko da yana yaro mawuyaci ne ka ji kukansa.
Emergency aka yi da Inarah, inda cikin ikon Allah bata mutu ba. Sedai ta samu mummunan rauni a kanta.
Wanda seda tayi sati guda kafin ta farfado. Wanda likitoci sun bada tabbacin, indai ta farka da wata matsala, to sai an yi mata aiki a kanta. Hakan ya ba kowa tsoro, domin likita yace kodai ta samu matsala a brain dinta, ko kuma zata tashi kamar doluwa. Hakan yasa duk hankalinsu yake tashe.
Ayzaan yafi kowa shiga tashin hankali, wanda har lokacin babu wanda yasan menene ya faru da Inarah. A karshe seda suka fita da ita kasar waje aka duba ta.
Alhamdulillah, ta farfado ba tare da matsalar da ake gudu ba. Sedai likitoci sun ce akwai allurai wadanda za a dinga mata duk bayan wata daya, wadanda sune zasu daidaita komai. Sedai ciwon kai mai tsanani wanda duk lokacin damuwa, ko tsoro, ko tashin hankali, to hankalinta zai iya gushewa na wani lokaci ko kuma ta fada doguwar suma. Sun shiga tashin hankali ba da wasa ba da jin wannan bayanin na likita.
Amma haka suka dangana suka dawo gida. Se kuma ta fara tsoron mutane. Sam bata iya shiga cikin yara, haka makaranta da kyar aka samu.
Ayzaan ya cigaba da zuwa makaranta, se ya zamana Inarah koyaushe tana gurin Ummee. Bata yarda da kowa, indai ba Ayzaan ba. In kuwa ya tafi makaranta, to sedai in tana bacci, ko bacci se ya zamana sedashi zatayi. Sannan in suna tare, takanyi nuni da hannu ko tayi alamar zata yi magana, amma maganar bata yuwuwa.
Hakan yasa suke magana da Ayzaan da wani irin salo wanda shine ya koya mata a lokacin. Ayzaan ya fara girma, domin kuwa sun kammala secondary. Duk da sun koma asibiti, amma likitoci basu fahimci dalilin rashin maganar ta taba.
Aunty Sameerah itace wacce ta fara lura da wani abu. Hakan yasa ta samu Ummee sukayi magana, aka fara yiwa Inarah magani na Hausa.
Cikin ikon Allah se gashi an samu nasara, domin kuwa bakinta ya bude. Budewar bakin Inarah bai sa an san me ya faru a waccen ranar ba. Sedai akwai mutanen da hakan yake cin zuciyarsu sosai, sedai basu da yadda zasuyi, domin Inarah ta kasa tuna abinda ya faru a waccen ranar.
Duk da kasantuwarta yarinya yar shekara biyar, Inarah sun fara girma, inda kowa akwai bangaren da yafi ganewa.
A wannan lokacin ne kuma wani tsautsayi yasa ciwon Reehal ya tashi. Lokacin su Ayzaan na shirin tafiya makaranta, sedai tafiya a wannan lokacin ya fasu. Bayan kaita asibiti, bincike ya nuna tabbas allurar da aka yi mata ce ta jawo hakan, domin allura ce mai lalata kwakwalwa da kuma gangar jiki gaba daya.
To a lokacin ne Hajiya Inna hankalinta ya tashi, haka itama Hajja. Domin komai a gidan yake faruwa, kuma ba wanda zai iya cewa ga wanda zai iya aikatawa. Se kuma kowa ke tunanin, shin wai me yake faruwa ne? Menene abinda ke faruwa a gidan? Wani dalili yasa ake farautar rayuwar yarinyar? Akwai yara da yawa a gidan, wanda a lokacin ma kusan itace karamar yarinya a gidan.
Duk da kulle likitan, magana daya yake fadi, "Besan komai a kai ba. Allura dai itace wacce yake mata." Wani dalili da wanda Abbie shi kadai ya barwa kansa sani yasa aka kyale wannan likita.
Tun daga nan Mahbub ya dage akan lallai likita zai karanta, ko dan yar uwarsa. Hakan yasa aka tsaurara a kanta. Sannan ya zamana Dad (Umar) shine kadai wanda zai dinga yi mata allurar, kasantuwarsa likita.
Babu abinda ya canza. Karatun da zasu fita yi kasar waje saidai aka yi sa ba da Ayzaan ba, domin yace bazai iya barin kasar ya bar Inarah ba. Hakan yasa sauran suka tafi, shi kuma ya fara karatunsa anan. Har lokacin kuma duk inda zai sa kafa, to Inarah zata dire tata. Tanada surutu na hakika, ga shagwaba, ga tsokana kamar me.
Tun tasowarta tana son harkar bincike ko kuma jarida. Hakan yasa tacewa Abbie, in ta girma irin aikinsa zata yi, wato lauya, ko kuma irin aikin da Yaya Ayzaan yake karanta, wato aikin jarida.
Abbie ya kasance lauya ne mai zaman kansa. Hakan yasa tace in ta gama karatu yar jarida takeso ta zama. Kuma tun a wancan lokacin Abbie ya bata goyon baya. Haka suke karatu, inda rayuwa ke tafiya, wanda Alhamdulillah zuwa lokacin manyan duk sun kammala karatunsu, kowa kuma da abinda ya karanta.
Sauran matan ma duk sun girma, wasu ma sunyi aure, ana shirin aurar da wasu. Jauhar tayi aure, ba ma sa kasar, ita da mijinta suna Saudiyya. Wani aiki ya kaisa can.
Haka Khalid yayi aure har da yarsu guda daya, Iman. Se kuma Haidar, shima yayi aure ba dadewa.
Se Hanifah itama tayi aure. Ta auri wani dan abokin babanta.
Najmah anfara maganar aurenta.
Sauran Kuma duk wasu sun kammala karatunsu, suna aiki,wasu basa kasar ,wasu Kuma sunanan suna aiki.
Ayanzu Inarah cikakkiyar yar jarida ce,
Mahbub likitane inda Yana da asibitin Mai rabo hospital.
Haka Shima Umair likitane.
Ayzaan kuwa ada Dan jarida ne sedai faruwar Wani abu da ya tauye rayuwarsa,Kuma yabar masa tabo Mai girma,shine dalilin barin aikin jarida Wanda yanzu hakan shi Dan kwallon kafe,tun Yana yaro Yana da baiwar kwallo n kafa inda tasowarsa kungiyoyi da dama sunso yayi aiki dasu Amma ya zabi aikin jarida, sabida shine burinsa.
Amma bayan faruwar abinda suke dangantasa da kaddara, ya aje wannan aiki,yashiga wata kungiyar kwallon kafa kasantuwar yashiga wasu kungiyar Kuma yaci gasa ba daya ba hakan yasa bayan barinsa aikin ya shiga kungiyar kwallon, inda yanzu shi din kwararren Dan kwallon kafane.
Wanda se da akakai ruwa Rana sannan suka bari Inarah itama tazama yar jarida domin kuwa sun tsorata da abinda yafaru abaya.
(Asannu zamu warware komai.)