Cigaban labari
JA DA BAYA...
Book 1
Page 5 ✍️
Meelah bazata
***
CIGABAN LABARI
"Wai waye wannan MARK SHADOW ɗinne? Kana cikin hukumarku amma ace ka kasa gano ainahin waye shi? Yaron nan yana mana illa sosai fa."
Dattijon mutumin, wanda akalla zai kai shekara saba'in, yake faɗa cikin tashin hankali.
Manyan mutane ne a cikin falon, wanda akalla za su kai mutum sha biyar, kuma duk manyane masu faɗa a ji. Sai dai akwai guda ɗaya wanda shi kuma matashi ne. Sai dai kallo ɗaya za ka yi masa ba za ka so sake kallonsa ba. Jikinsa ma abin tsoro ne, bare fuskarsa. Idanunsa kuwa, ɗaya a akanne yake, ga kansa kwal-ƙwabo. Yadda ka gan sa, ka ga cikakken shaidani.
Wani daga cikin mutanen ya waiga ya ce, "Kai UBAN TSIYA, ya ake ciki? Yanzu ka ga wannan, har kallar wancan tsinannen yaron ya bata mana ita. Amma yanzu me kake tunanin za a yi? Sannan na san wannan aikin ba zai gagare ka ba. Muna buƙatar sanin waye wannan, ka na ji ko?"
Mutumin wanda aka kira da Uban Tsiya, tabbas ya ci sunansa, domin muryarsa ma kawai ta tsiyarce. Dagowa ya yi yana faɗin, "Sai ka sha, Mai gida. Shi ɗin banza, dole zan binciko waye shi."
Mutumin ne ya furta"
"Na san hakan ba zai gagare ka ba."
Uban Tsiya ya ce, "Cif, Mai gida."
Wata mata ce a gefe ta ce, "Gaskiya haka ya kamata, amma akwai buƙatar mu sake sabon shiri."
Wannan dattijon da ya yi magana a farko, shi ne ya ce, "Kafin mu yi wani shiri na gaba, ya kamata mu aiwatar da plan B. Amma za mu fara wani shiri a kan haka. A wannan karon dole ku san waye wannan MARK SHADOW ɗin."
Kallon Uban Tsiya ya yi yana faɗin, "Kana iya tafiya, zan neme ka zuwa dare."
Tashi ya yi yana faɗin, "Sai ka sha, Mai gida."
Bayan fitarsa ne, ɗaya daga cikin mutanen ya ce, "Kuma game da wannan gidan jaridar, na ga wani program da suka fara. Dole zai kawo mana cikas a tafiyarmu. In hankalin jama'a ya karkata a kai, shima akwai matsala. Kuma da alama shirin yana samun magoya baya."
Ɗayan ne ya ce, "A'a, wannan ƙaramar matsala ce, ba zai zame mana matsala ba."
Da haka taron ya tashi, kowa ransa ba daɗi, sai dai sun ɗauki damarar sake sabon shiri.
MAI RABO ESTATE
Ummee ce a zaune a kusa da Abbah tana haɗa masa shayi. Magana suke, inda take cewa, "Abubuwan da suke faruwa sun fara daure min kai. Na rasa gano bakin zaren."
Abbah ne ya ja gwauron numfashi tare da faɗin, "Kar ki damu, Insha Allah babu abin da zai faru. Na fi tausaya wa mamana (Inarah), saboda ita mace ce. Sannan yarinyar nan har yanzu abubuwan suna bibiyarta. Sai dai na rasa gano abin, amma a yanzu dole na yi bincike, don sanin me ke faruwa.
Sannan yanzu ga yanayin aikinta, aiki ne na hatsari, duba da abin da ya faru da Ayzaan. Amma na tabbatar, Insha Allah, ina ji a jikina ba wanda zai ci nasara a kan Inarah.
Ga kuma labaran da suka wallafa jiya, hakan zai iya jawo musu damuwa.
Kuma ba yanzu suka fita ba daga hukumar mu. Ni babbar damuwata, ban san ta ina wannan saƙo da aka turo jiya ba. Amma ko da ma wanene, yana mana barazana ne akan tsoratar da mu game da yin wani abu. Ni na fi tunanin daga gareni suke buƙatar wani abu. Amma ko menene, ba zan taɓa ba su abin da suke buƙata ba."
Ya faɗi hakan ne don ba ya so hankalin Ummee ya tashi. Amma ya tabbatar da abin da suke buƙata a garesa ba za su samu ba. Wannan alkawari na ne,Ko da ace za su ɗau rayuwata kuwa, dole a wannan karon mu yi wani abu a kai.
Ummee dai gaba ɗaya a tsorace take. Gani take kamar wani abu zai iya faruwa.
Abbah ne ya kore shirun ta hanyar faɗin, "Mun yi magana da Jauhar jiya. Yau, Insha Allah, za su dawo."
Ummee ta ce, "Eh, ta gaya min. Ubangiji Allah ya dawo da su lafiya. Ai sun yi ƙoƙari, shekara uku ba sa ƙasar fa.
Kusan shekararsu huɗu kenan a can. Yanzu za su dawo gida. Ya gama abin da ya kai sa, yaronsu ɗaya mai kimanin shekara biyu, mai suna Afeef."