JA DA BAYA...

Abinda ba'a zata ba

by @meelahbazata978

*JA DA BAYA...*  
*Book 1*  
*Page 6✍️*  
*Meelah Bazata*

***


Zaune suke agurin cin abinci. Sunyi sallah sun tsaya suna cin abinci. 
Inarah ce ta Kalli kawarta zarah tace "hmmm wai kinsan edita dazu Kiran dayamin akan me yake kirana?" 
Kallonta zarah tayi tace "a'a sai kin fada. ammma yadda yaketa nemanki nasan akwai wata a kasa. 

Dariya sukai dukkansu. Inarah tace mata "akwai Wani babban Dan kasuwa dazanje nayi Hira dashi wlh nadan firgita dajin sunansa, Kuma ni Allah naso atura Wani, Amma yace ni zanyi yanzu yabani number dinsa da komai zamuyi magana inyabani appointment se Muji yadda za'yi.

Zarah ce tace "shin wanene haka?" 
Inarah ta numfasa tare da fadin "ALHAJI GALI MATAWALLE. 
Tabdijam inji zarah tare da fadin Allah yataimaka lilly. 
Ammafa gaskiya waye baisan alhaji Gali matawalle ba, kwana biyu aiki yadau zafi musamman game da rahoton da mukeso mu hada. 
Dole se mun Kara dagewa gashi mun kasa samun kowani bayanai akai. tafada tare da kallon Inarah.

Inarah tace "zamu samu besty domin ni nasamu number din daya daga cikin yan uwan wadanda abin yafaru dasu. Kuma inada yakinin zamu samu abinda mukeso daga garesa, Amma wannan aikin dazanyi shine kawai. Dana gama zamu cigaba da hada wadancan bayanan. 
Zarah tace "hakan nada kyau tashi mu koma kafin Azo afara mana jaraba. 
Haka suka tashi suka tafi suna Hira suka nufi cikin office din nasu.

Shigarsu suka hadu da abokin aikinsu Wanda aka turasu tare da inarah aikin tare. 
Inarah tace masa insunyi magana da bakonsu zata masa magana sannan kowa ya koma bakin aiki.

---
Mommy wai kina tunanin inyi hakuri? Kiyima daddy magana mana, ni wlh Ina sonsa a haka kullin nayi magana se ki kawo Wani dalili. Mommy bazan iya rayuwa in babu shiba, please! Tafada cikin sigar damuwa da magiya. 
Mommy ce ta kalleta, tace "haba daughter yakikeso namiki tunda kikaga nace Miki kiyi hakuri hakan ba abune dazai yuwuba. Domin ko iyayensa bazasu bari ma ki auresaba, kinsan halin Muhammad bazai yarda ki cutu ba. Sannan Ayzaan ma Babu aure acikin kaddarar sa, tunda hakan ba abune dazai yuwuba.

Kuka tasake fashewa dashi tana fadin "wai mommy meyasa kike fadin haka? Ni dai zanje inyiwa innah magana, ita nasan zata fahimceni.

Mommy kallonta kawai take tarasa me zata ce mata. Tashi tayi tana fadin "ai sekiyi inkin gama kitashi kije kici abinci. 
Amma kisani ni kaina bazan taba yarda ki auri yaronnan ba. Nagayamiki, kuka tafashe dashi tana kwanciya akan gadon.

Mommy fita tayi tabarta agurin ta nufi falo, inda ta zauna akan kujera tare da Kiran yar aikinta. 
Daukar waya tayi tafara dubawa inda take tambayar yar aikin ta ta "ke Kun kammala aikin kokuwa?" 
Tace "angama hajiya saura kadan. 
Tace "to kushirya komai a dining kafin su karaso. 
Da to ta amsa mata tana mikewa ta fita.

---
Hello sir! Kana jina? Yallabai muna bukatar lallai se kazo gurinan, domin abun yanason yafi karfin mu, munyi iya yinmu, Amma da alama matasan gurin a hasale suke. 
Suna taso suyi mana bore akan hakan. 
Sedai shi yaron gashi mun kamasa. 
Yallabai ita ma yarinyar ansamu gawarta agurin, sedai gawar ta munana gaskiya. 
Ina tunanin abinda ya kara hassala matasan gurin kenan duba da irin haka Tasha faruwa, Kuma arasa Mai laifin. 
Sannan yallabai iyayen yarinyar ma ansamesu sedai sun dage akan yan sanda bazasu tafi da gawar ba, sun dage sedai sudau yar su suyi mata sutura. 
Amma mutane sunata ihun se anbasu shi sun kashesa har sun fara jifa.

Amsawa yayi da "karku bari Wani abu yafaru! Kuyi iya kokarin ku yanzu zantura muku Karin jami'ai sannan akwai bukatar lallai adauki gawar domin yin yin bincike. 
Amsawa yayi da "to sannan ya ce "ku Kara Saka Ido sosai akan kowa da ke wurin, yace "ok sir.

Komawa yayi gurin inda gaba daya ya kacame da jama'a ta ko Ina. Matasa kuwa sai hankoro suke suna fadin bazasu yaddaba.

Abinda ake musu yayi yawa, Dan haka dole abasu me laifin, Dan hukuma ba abinda takeyi akai ko ta kama masu laifi. 
Ana haka wata motar yan sandan ta karaso wajan dare da Karin jami'ai haka suka fito daga motar tare da yin harbi sama, Wanda alokacin yan jarida har sun fara zuwa gurin. 
Harbin da yan sandan sukai sama shine yasa matasan suka koma baya. 
Yan sandan sukai amfani da wannan damar suka tafi da Mai laifin. 
Sannan suka Saka gawar a mota suka tafi da ita.  
̶ ̶ ̶ ̶ ̶ ̶