JA DA BAYA...

INARAH 🥰

by @meelahbazata978

*JA DA BAYA...*  
*Book 1*  
*Page 7✍️*  
*Meelah Bazata


***

INARAH AHMAD MAI RABO kenan.  
Kwararriyar yar jarida, matashiya Mai sanin makomar aiki.  
Sananniya Kuma a kafafen sada zumunta. Yar jarida ce me matukar kwazo da jajircewa akan binciko gaskiya. 
Sannan basa Saka labari Wanda Bai ingantaba a gidan jaridarsu. 
Matashiya ce Mai dunbin masoya a social media. A duk handle dinta tana da magoya baya sedai ba Kasai tacika Saka abinda ya shafi rayuwar ta ba sedai in abinda ya shafi aikinta.

Tana office tana aiki edita yazo yace tai Maza ta tafi ga abinda ke faruwa a unguwar kwarya sabon layi, Dan samun labari. Da Kuma dakko rahoton abinda yake faruwa.  
Cikin gaggawa ta Isa wurin ita da abokin aikinta. 
Unguwace yanayin ta kamar sabuwar unguwa, duba da yawaitar kangwaye. Kuma unguwace da masu kananan karfi.

Sun tarar yansanda sunkama Mai laifin sedai basu riga suntafi da gawar ba suna jiran motar da aka turo domin tafiya da gawar.  
ID card dinta ta Ciro ta nuna musu hakan yasa mutane suketa kokarin tofa albarkacin bakinsu.  
Duba da cewa ko kafin zuwansu gurin ya. Sanda sun wuce da Mai laifin Amma duk da haka seda suka karasa kusa da gawar. 

Sedai abinda suka gani ya matukar razanasu su, domin kisan da akaiwa yarinyar da alama yayi Muni, don har wasu sassan jikinta ancire.

Saidai game da rahoton da suka samu abakin Jamar gurin shine "gawar yarinya yar kimanin shekara goma Sha daya ce yazo da ita zai yar awani kango.  
Da alama anyiwa yarinyar fyade sannan ancire wasu sassa na jikin yarinyar, Wanda abin ya kazanta sosai. 
Akwakin anata fama da batan yara.  
Yanzu yara kusan talatin da shida ake nema, wasu ana tsintar gawarsu wasu kuwa ko labarinsu.  
Kuma hallau ba'a samuba, hakan yasa kama wannnan ya fusata matasa, har sukayi yunkurik kashe Wanda suke zargi sedai yan sanda sun karaso wurin akan lokaci.

Inarah ce ta bukaci ko zata iya ganin gidansu yarinyar da abin yafaru da ita tunda ance iyayen yarinyar ma har sunzo gurin? 
Hakan yasa aka nuna mata.  
Karasarwarsu ba wuya, suka tadda ko Ina cike a kofar gidan.  
Alokacin gawar yarinyar jami'ai sun tafi da ita domin yin bincike.

Shiga ciki tayi ta samu mahaifiyar yarinyar tana kuka sosai, bazata iya furta komaiba hakan yasa zuciyarta ta karaya, kasantuwarta me saurin kuka. 
Hakan yasa tafita akofar gidan tasamu mahiafin yarinyar, inda sukaji ta bakinsa. Yace mata "yarinyarsa shekararta goma Sha biyu, tatafi makarantane bata dawoba har lokacin dawowarta, bata dawo ba. 
Hakan yasa mukaje ofishin yan sanda muka Kai report, yau kwana uku bamu gantaba se yanzu da muka samum gawarta. Ya fada cikin damuwa mai tsanani.

Inarah tace masa "to yanzu Wani mataki kake bukata hukuma ta dauka?"  
Yace "duk matakin da hukuma zata tadauka anriga an cuceni.  
Mahmah ita kadaice yata, ita kadai gareni, Amma yau ankashemin ita.  
Yana Fadi kuka ya kufce masa, ya goge idanunsa yace "badanni ba kodan rayuwakan sauran yara! 
Ina rokon hukuma tadau mataki akai, Ina neman abimin hamkina. Yakarasa maganar da alamar roko.

Gaba daya jikin Inarah yayi sanyi, tausayin iyayen yarinyar gaba daya ya kamata. 
Juyawa tayi zuwa fita tare da tambayar wadanda sune suka fara ganin gawar, ta tambayesu game da abinda yafaru da Kuma ta yaya suka ga mutumin?

Dayan ne yace "mundawo daga kwallo, to senaji fitsari, senayi kokarin shiga cikin wancan kangon nayi fitsari.  
Kafin nashiga se naga Wani matashi ya dauko Wani buhu abayan mota, kasantuwar unguwar ba yawan mutane, Kuma gashi tsakiyar Rana ne.  
Ayanayinsa naga kamar bayida gaskiya, Dan yanata waige waige, se muka tsaya muka labe daga Gefe. 
Shine mukaga ya fito da buhu abayan mota Yana shiga, mukabi bayansa, se mukaga abinda yake ciki.  

Tace "to yanzu me yasa kukai kokarin daukar doka a hannunku?"  
Yac mata "hukuma bawani mataki datake dauka akai.  
Domin anyi haka yafi Sau nawa, Amma basuga matakin da hukuma take dauka ba.

Numfashi taja tare da waigawa tace "  
"A nan ne muka kawo ƙarshen rahotonmu daga wannan wuri. 
Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano cikakken bayani kan wannan lamari, yayin da jami'an tsaro suka kama wanda ake zargi da hannu a ciki. 
Za mu ci gaba da bibiyar wannan batu domin kawo muku duk wani sabon bayani da zarar ya samu. 
Ni ce taku Inarah Ahmad Mai rabo daga gidan jaridar haske maganin duhu.

Kashe camera sukayitare da shiga mota suka koma, yayin da abinda yafaru yaketa dawo mata arai.  
Tayi matukar tausayawa mahaifiyar yarinyar, inda take kallon fuskar mahaifin yarinyar kamar ta San fuskar a Wani guri.

---