JA DA BAYA...

Rayuwar karamar yarinya

by @meelahbazata978

*JA DA BAYA...*  
*Book 1*  
*Page 8✍️*  
*Meelah Bazata*



***

Da komawarsu gurin aiki office dinsu ta nufa.  
Inda tazauna gaban computer dinta taciro recorder dinta da camera ta saurari duk bayanan da ta tattara sannan tafara rubuta rahotonta.  
Bayan tagamane tadauki duk rahoton data tattara da takarda ta nufi ofishin edita.  
Da sallama tashiga ciki.  
Tace "nagama hada rahoton, tare da Mika masa.  
Amsa yayi Yana dubawa cikin natsuwa. 
Bayan yagama yadago ya kalleta tare ta tambayarta "Baki samu Wani bayani daga yan sanda ba?" 
Amsawa tayi da fadin "Ina zuwa jami'ai sun Riga sun wuce, Amma abayanin Da muka samu matasa sun so suyiwa yan sandan bore akan se sun kashe Mai laifin, sedai hakan Bai samu ba.

Jinjina Kai yayi cike da gamsuwa tare da fadin "aikinki yayi kyau." 
Tace "nagode yallabai tare da jiya ta fita.

Shikuma yatura bayanan bangaren wallafawa inda tuni zancan yazaga ko Ina maganar ake tayi.  
Ita kuwa Inarah tana fita mota kawai ta nufa ta tafi gida.

Tana shiga gida tai parking na mota. 
Kasantuwar driver dayake kaita yayi tafiya zuwa garinsu yau.  
Kuma ta makara fita duk yayyenta sunfita aiki dama Mahbub ke kaita ko Kuma Ayzaan, se Kuma Umair to yau duk basanan, sun rigata fita, shiyasa tai driving da kanta. 
Dan Abbie bayaso tana driving.

Tana shiga falon ta tadda Ammie azaune tana kallon television. 
Da sallama tashiga falon Tare da fadin "washh Ammie yau nagaji sosai yunwa nakeji. 
Kallonta Ammie tayi cikin kulawa tace "ai dole kigaji wannan aiki haka kiyi Maza ki kishiga kiyi wanka kizo kici abinci" 
Kwanciya tai ajikin Ammie tare da fadin "Ammie senaci abinci tukun, yunwa nakeji. Tafada da alamar gajiyawa da Kuma damuwa.

Kallonta Ammie tayi tana fadin "ahaka Zakici abincin kinzo kinmin kwance ajiki?  
Sannan Kuma ga damuwa ma a fuskarki. 
Inarah tace "Ammie game da abinda yafaru ne na kisan yarinyar gaskiya abin akwai tashin hankali, iyayen yarinyar sunbani tausayin, ita kadaice yarsu, yanzu gashi an kasheta.  
Ammie yaushe ne abubuwannan zasu Daina faruwa yaushe gwamnati zata gyara? 
Ammie yanzu ana samun yawaitar bacewar yara, abin yafara yin yawa.

Ammie tace "yanzu kitashi kici abinci, sannann dole kiyi taka tsantsan, a yanzu ke yarinya ce bazaki gane wasu abubuwan ba.  
Cewa tayi "Ammie ke nakeso kibani abincin da kanki.  
Tashi Ammie tayi tazo tabata abincin cike da kulawa.

Bayan tagama tashiga daki tai wanka tana sakkowa ta tarar Mahbub yadawo daga wurun aiki. 
Karasawa kusa dashi tayi tace "Yaya kadawo?  
Yace mata eh. 
Cewa tayi "Yaya ya maganar damukayi?  
Yace "karki dameni sarkin naci, Ina sane ai se nacin jaraba kika dameni. 
Sena fasa da sauri tafara girgiza Kai zatai kuka yace "aikine Bai ishekiba Banda lokacin. 
Yasa Kai yashige bangarensa Yana cewa Ammie bari yai wanka yazo yaci abinci.

---
Zaune take cikin dakinta takaddace agaban ta ga Kuma laptop da alama Wani abu me muhimmanci take rubutawa, duba da yadda take ta ciza bakin biro. 
"Inarah! Inarah!!" Kiran Ammie ne yadawo da ita daga tinanin data tafi.  
Na'am ta amsa tana tana sakkowa.  
Ce mata Ammie tayi "Maza zo kidau waccen kular ki kaiwa inna.  
Da to ta amsa tana nufar inda Ammie ta nuna mata.  
"Ahaka Zaki tafi bazaki koma kidauko hijab ba, ni Sam bansan yaushe zakiyi hankali ba Inarah."

"Ammie ni yanzu me nayi?" 
Zaki tafi kosena bata Miki Rai dakinta ta koma tadauko hijab ta dau kular tanufi bangaren inna.

Bata karasaba suka hadu da Umair. Da alama dawowarsa gidan kenan.  
"Yar jarida" shine Sunan da yafada Yana murmushi.  
Kallonsa tayi da murmushi a fuskarta tana fadin "yaya kaima Kazama Dan jarida kawai kullin seka tsokaneni.  
Murmushi yayi tare da fadin "inyi ya da nawa aikin? Wannan aiki aiseku, bazan iyaba." Yafada Yana shigewa.  
Itama wucewa tayi tashiga falon inna da sallama.

Inna ce azaune akan carpet ta mike kafafu da carbi a hannunta tana ja. 
Kallo daya zakai mata ka hango tsantsar kyanta, duk da girma ya boyesa, Amma kasantuwar akwai kudi kallo daya zakai mata kashaida, domin akalla zatakai shekara saba'in da Wani abu.  
Karasawa kusa da ita tayi tare da kwanciya akan kafafunta, tana fadin "inna nayi kewarki gaskiya, yau Sam banganki ba.  
Innace tace "ke kuwa takwara" sunan datake Kiran Inarah dashi kenan "kizo ki kwanta min a kafa ko tausayina bakyaji?"  
"Inna nayi kewarkine fa" tafada cike da shagwaba.

"Inna ga abinci" inji Ammie.  
Da murmushi a fuskarta tace "Allah sarki baiwar Allah, Allah dai yayi mata albarka wai fate dataji dazu nace inaso shine tayi, aikuwa nagode. 
Maza dakko min kwano kizubamin.  
Tashi tayi ta nufi kitchen tare da fadin "wai inna Ina babah adama ne?" Yar aikin inna.  
Innace tace "ohh baiwar Allah jikarta ce tarasu dazu aka kirata ake gaya mata.  
Yarinyar wai kasheta akayi, dama kwana nawa ana nemanta ba'a gantaba, se yau Shima gawa suka samu." 

Cike da sanyin jiki Inarah tace "aina gidansu jikar tata yake?"  
Cewa tayi "Nan garinne can wurin sabo road kafin a karasa kwarya."

Dasauri Inarah ta zaro Ido tana fadin "innalillahi! Kar yazama fa yarinyar da aka tsinci gawartane yau." Tafada cike da rudani.  
"inna har gidansu munje daukar rahoto, maman yarinyar tabani tausayi, abin ya matukar tsaya min arai tsaya min arai, sedai fuskar mahaifin yarinyar yanamin kama da Wanda nasani Amma narasa waye."  
Innace tace "tabbas itace, ohhhh ni sa'ade yaushe wadannan abubuwan zasu Dena faruwane, yanzu batan yara yazama ruwan dare kullin na kunna redio senaji cigiya." Tafada cike da alhini.

Inarah ce tace "Amma inna ni banga babah adama ba awurin danaje."  
"Eh ba'a kirata ba da wuri, Dan bata Dade da tafiyaba, nima kafar ce yau ba dadi shiyasa Amma gobe inshallah zanje nai musu gaisuwa."

Inarah ta koma Gefe cike da nazari akan hakan tabbas wannan yarinya jikar babah adama ce.  
Yanzu Wani mataki hukuma zata dauka akai? 
Dole ma ta bibiya wannan case din.  
Abunda take ta sakawa aran ta kenan ita Kadai, gaba daya se jikinta yayi sanyi, duk in ta tuna yadda mahaifiyar yarinyar ke kuka se hankalinta ya Kara tashi.  
̶ ̶ ̶ ̶ ̶ ̶