KADDARAR SOYAYYA

KADDARAR SOYAYYA

by @sheolly

Miemi tayi dariya tana gudu a hankali tana waige_waige don ganin ko sadiq yana biye da ita. Sadiq kowa yadaga kafafunsa da sauri, yana kokarin kamuta amma duk da haka bazai iyaba, domin miemi tanada kwarewa a wajan gudu sosai.
Tajuya cikin sauri tana cewa "you are still behind me,sadiq!
Yayi murmushi yana girgiza kai"just wait, miemi. I will catch you one day."
  A lokacine wata  farar mata da a shekaro bazata wuce  59 amma jindadi ya buye shikarunta. Ta fito daga kitchen  domin tana taya yan aikin ta girki domin yau mai gidanta zai dawo Nigeria.
Tadaga murya cikin tsawa" Miami! Sadiq! Come back here now" 
Sai suka tsaya cak, suna kallon juna da firgici, domin sunsan idan aka kamasu, za'amusu fada sosai