ƙunchi , soyyaya, farinciki

Page 2

by @saadatukaraye441


ƳAR MAKAHO

NA

SA'ADATU KARAYE

(MRS FAISAL)


PAGE 2 ««


Tafiya take cikin sauri sabida makarar da tayi na islamiyya, tasan yau kam zata sha rashin mutuncin prefect, dan suma ba wani santa sukeba ita fa dama ta saba da kiyayyar da mutane suke nuna mata tako ina makarantar boko, islamiyya uwa uba kuma gida mama kande ta uzzura mata. islamiyya ne kaɗai take ɗanjin nasu saffa! saffa! suma dan ana faɗakar dasu ne da abun da zasuyi mata saiya fi haka.


Shi ma isalamiyyar kamar mujiya haka take rayuwa a cikin dalibai, saida Allah ya taimaketa aka kawo wata sabuwar zuwa ta dinga shisshigewa Fatima.


Amma Fatima samm'' bata san tana kulata sabida ita gani take kamar cutar da ita zatayi, saboda bata taba ganin wanda yayi ma ta irin wannan shisshiginba kamar ita.


A cikin ranta tana faɗin wannan sabuwar zuwan anya kuwa tasan koni wacece da take yimin irin wannan shisshigin haka.


Suma yan makaranta haka suke cewa kila ko tayi tinan nin yar masu kudice ta ganta fara mai kyau tubarkalla.


Amma ina ba haka abun yakeba a zuciyar Nafisa, tunda ta shigo makarantar taga yadda ake yiwa Fatima, ta dauki alkawarin zama aminiyarta kuma bazata sake bari a wulakanta taba. duk da batasan wacece Fatima ba amma taji ta kwanta mata a rai sosai.


Abunda Fatima ke gudu shiya faru kuwa domin tana zuwa bakin shi ga makaranta taga an tara dalibai da yawa a kofar shi ga alamun dai makararrune a wajan jikina a sanyaye ta karasa bakin kofar ta tsugunna kamar yadda sauran daliban sukayi.


''Keee! zonan'' daya daga cikin prefect ta faɗa tana wurgawa Fatima wata muguwar harara,jikinta na rawa ta karasa wajan wadda ta kirata.


Bazan tambayeki maiyasa kika makaraba dan nasan amsa ɗaya ce kullum kike faɗa,kin tafi raka babanki unguwa. ta faɗa tana wani yamutsa fuska kamar taga kashi a wajan.

Wato ke bazakice kin tafi bara da tsohonkiba ko waike kin waye ko, to bari kiji in gaya miki duk randa kika kara makara a islamiyyar nan ki kuka da kanki. dan wallahi saina baki purnishment dinda ba'a taba baki irinsa ba a rayuwarki.


Itadai Fatima jinta kawai take domin kuwa dama aita saba da muguntar da suke mata sabida haka ko sanda ta hango cewar ta makara ta riga ta sallama kanta, kashinta ya bushe kuma ita babu wata purnishment da zata ji tsoransa a halin da take ciki, ita wata kalar izaya ce bata ganiba a arayuwarta shiyasa bata fargabar duk wani abu da za'a mata sabida a hukuntata.


Kai kowa ya tashi ya tafi aji amma banda ke, ta nuna Fatima sannan tace duk wani hukunci da zanyi musu akanki zanyisa. sabida haka kije ki ajiye jakarki ki dawo tana magana tana hade rai.


Nafisa ce take tambayar daya daga cikin makararrun ajinsu taga duk sun shigo aji amma banda Fatima.


Kewai dan Allah ina ruwanki da Fatima ne duk kinbi kin daga hankalinki akanta, sai kace wata yar mai kuɗi ana ƙawance da yaran masu kuɗi amma ke kin nacewa ƳAR MAKAHO, ga talauci!!! ya isa Amira'' ya isa ta faɗa cikin daka tsawa,ashe dama dalilin da yasa aka tsaneta kenan,sabida kawai ta kasance ƳAR MAKAHO'' shekenan batada wani galihu a wajam mutane,lallai dan adam kun manta da cewa Allah daya ɗorawa mahaifinta makanta zai iya ɗora muku koya dorawa wani naku.


Wannan sam ba daidai bane ku sake rayuwarku gaskiya, tana gama magana ta fita a ajin domin taje taga mai yake faruwa,aiko tana zuwa ta iske Fatima ta zage tanata kwashe wata ƙasa a kofar makarantar ga prefect din a kusa da ita, tana bata umarni.


Duk wannan abun da ake malaman basa kusa ballantana asamu wanda zai mata magana.to amma dayake sunsan malaman nasu na musu wa'azzi akanta, sai suke yi a boye cikin hikima yadda bazasu ganiba.


Haba wannan wani irin rashin imanine haka!Nafisa ta faɗa tana karasawa wajan,fuskarta a haɗe.

Kee ni kike faɗawa haka ina wasa dake ne, prefect din ta faɗa tana karasowa inda Nafisa take a tsaye,lallai yau kema zaki kwashi rabanki zonan tana kokarin jawo mata hijabi. karki kuskura ki tabani'' Nafisa ta faɗa tana dalla mata harara sannan tace Fatima zomu tafi aji kinji.


Keeee! ina wasa dake ne in sakata aiki kice tazo ku tafi.Okay tam shikenan bari inje in fadawa malam inusa abunda yake faruwa kila in yazo ki barta ta tafi ajin. aiko kamar an kira mata sunan wani mala'ikan mutuwa ba shiri tace Fatima ta tattara jakarta ta tafi aji.


Malam inusa wani malaminsu ne da suke bala'in tsoransa. kuma yana daya daga cikin malaman da suke yi musu faɗa akan uzzurawa Fatima da sukeyi, shiyasa tanajin sunansa ta shiga taitayin.


Gatanan uwar shisshigi taje ta tawo da ita. Amira ta faɗa tana wani yatsuna fuska alamun abun bai mata daɗi ba.

Amma sabida ta ƙware a munafunci suna karasowa saita wayance da cewa'' kai Nafisa sannunki da kokari wallahi da kika tafi inata addu'a Allah yasa karta miki rashin mutunci kema'' wata harara ta mata irinta ki shiga hankalinki dinnan aiko saita kama bakinta tayi shiru.


Nafisa nagode da taimako'' amma dan Allah inaso in roƙeki wata alfarma ta faɗa fuskarta a raunane, inajinki Fatima! ''dan Allah dan Annabi Nafisa inaso ki daina saka kanki a cikin duk wani case dina, banaso ki shiga matsala sabida ni dan Allah, ki barni kamar yadda kikazo kika ganni ni kaɗai nake rayuwata babu kowa a cikinta, hakan yafi min daɗi banaso kema ki shafi baƙin fentin dake jikina.

kinga ke daga ganinki yar babbar gidace to dan Allah karki hada kanki da ƳAR MAKAHO please! ta faɗa tana haɗa hannunta biyu alamun bada hakuri, ga idanunta ya cika da kwalla kamar zatai kuka.

Tunda Fatima take magana Nafisa kawai kallanta take tana murmushi, tana girgiza kai irin alamun abinda bazai yiwuba kawai.


Fatima duk naji abunda kikace amma wallahi kiyi hakuri bazan iyaba wallahi, ta faɗa da confidence dinta tana murmushi amma bana farincikiba irin wannan murmushin mai kamada farin ciki. suna cikin magana wani malami ya shigo ajin dole suka hakura da maganar da suke.Kowa ya bude Alkur'aninsa mu daura karin karatu malamin ya faɗa yana bude nasa Alkur'ani shima.


Fatima! Fatima!! Fatima!!!

Nafisa ce take ta kwalla mata kira an tashi zasu tafi gida,amma Fatima tana jinta sai sauri take yi.

Nafisa kara saurinta tayi damun ta tadda Fatima, ''haba Fatima sai kiranki nake kinmun banza.

Wallahi Nafisa indai aka tashi a makaranta hankalina gida kawai yakeyi sabida baba. murmushi nafisa tayi sannan ta dafa fatima tace wallahi harkin kara shiga raina Allah ya karawa baba lafiya, ta amsa da amen nafisa tace to muje in rakaki gidan inaso inga baba mu gaisa.da sauri Fatima ta katseta a'a ki barsa kawai ki bari wata rana sai muje.

Kinga antashi daga makaranta ba'ason biyawa ko ina ki bari kikai ladanki gida dan Allah. ta faɗa fuskarta cike da damuwa, Nafisa tace tam shikenan tunda rowar gida kikemin na tafi ta faɗa ranta a bace alamun taji babu daɗi.itako Fatima abunda yasa taki yadda ta bita, sabida tana tinanin kila yau mama Kande ta dawo,kuma tasan halinta sarai ba ruwanta da wata ƙawa a gabanta zata mata halin nata, zata ma iya haɗawa da kawar ba ruwanta.


''Salamu Alaikum'' a shi go! gabanta ne ya faɗi rass! babu wanda yake faɗan wannan kalmar sai mama Kande.ita ce bata amsa sallama saidai tace ''a shigo'' Shekenan wahala ta dawo.

Fatima ta faɗa a ranta jikinta a sanyaye ta shiga gidan, aiko tana shiga tayi ido hudu da wasu uban kayan wanki a gaban mama kande. ta haɗiye wani mugum yawu a maƙoshinta, sabida ko ba'a faɗa mataba tasan ita aka ajewa ta wanke, ga kayan masu uban yawa kamar Wadda ta shekara batayi wanki ba.

Sannu da zuwa mama'' andawo lpy! ko kallan arziki bata ishetaba ta wurga mata uwar harara sannan tace yanzu ake dawowa Daga makaranta. ta buɗe baki zatai magana ''mamaaa! bakinta ta buge fabbb kafin kace wani abu har jini ya futa abunka da farar fata, rufemin baki munafuka da fuskarki kamar ta aljanu. wuce ki ajiye jakarki kizo ki wankemin kayan nan, lallai mama Kande ta cika azaluma jibi irin tarin uban wankin data tara kilama tunda taje garin nasu bata taba wankewaba.

Kawai sabida mugunta ta kawowa Fatima gida ta wanke mata.

Duk abunda suke baba na zaune baice mata komaiba sai murmushi yake yana juya kai.


Haka fatima ta jawo kayan nan ta hau wankewa tanayi tana share hawaye, aranta kuma tana faɗin wallahi sabida baba ne kaɗai zan zauna a gidan nan, inba dan haka ba guduwa zanyi inje duk inda zanima dan wallahi zaman wani gidan yafi gidanmu daɗi. tana cikin wannan tinanin taji wani mugun duka a bayanta ''ke wace irin yarinyace haka ake wanki ba zani ake fara wankewa ba, sannan riga. ''kaji muguntafa kawai dole saita kamata da laifi inba haka ba ya za'ace zani ake fara wankewa sannan riga Allah ya kyauta.

Tana ji tana gani ta koma wanke zani tabar rigar.


Tana cikin wankin ne kawar mama kande Jummai tazo, sai taji sanyi a ranta sabida tasan yanzu zata shiga ɗaki tabarta. haka kuwa akayi suka shiga ɗaki abunsu daga ni sai baba a wajan, na kalli baba yana sauraran radio nace baba kaci abinci kuwa?murmushi yayi yace Fatima kenan naci abunci kinga kwanan a ɗakina.ban ƙarasa ciba kije ki dauka kici kema.


Murmushi tayi sannan a ranta tace mama kande kenan duk muguntarta bata hana baba abunci, koda yake dole ta dinga basa sabida tana zuba masa maganin mallaka yanaci. ''to baba bari in karasa sai inci. ta faɗa tana ci gaba da wankin a ɗaki kuwa mama Kande da kawarta Jummai suna ta hirarsu ta duniya, inda Jummai ta katse hirar da faɗin waini kande maiyasa bakya tausayin Fatima ne.nasan wallahi wankin nan da kika bata kina sane kika tara, dan kizo ki bata tayi. banasan munafurci ina ruwanki mama Kande ta faɗa cikin masifa.''to daga faɗar gaskiya jummai ta faɗa tana riƙe baki. ''eh banasan gaskiyar ki riƙe abunki.

jummai tace aiko dole in faɗa miki gaskiya.


Duk rashin imani na nikam bazan iya irin wannan azabar da kike yiwa yarinyar nanba. kar kiga kodan nina rakaki kika je wajan wancan malami ni abuna a iya nan ya tsaya.



Jummai aminiyar mama kande ce, tare sukai ƴammatan cinsu kowa yasan halin kowa.jummai tuntuni tayi auranta itace ta bawa Kande shawarar ta auri malam ibrahim makaho.


Sabida damunta da ake a gari dayaki amincewa ta rakata sukaje suka masa asiri, ya yadda amma ta inda halinsu yasha bambam da kande ita jummai tana tausayin fatima. sabida ita macece mai san taga tana taimakon maraya duk da halinta ba wani mai kyau bane.

Amma kwara ita da kande ita jummai matsalarta bin malamai.




To tunda bakyasan gaskiya bari in tafi,toki tafi mana ai dama nace ki tashi ki tafi. to ai shikenan jummai ta faɗa tana mikewa abunta. tana fita taga fatima harta kusa gama wankin sannu fatima Allah ya miki albarka ta faɗa tana fita. a hanya kuwa tana tinanin hali irin na kande harta fara ma dana sanin rakata da tayi wajan malaminta,aka yiwa malam asiri koda yake ai nice sila sabida haka zanyi kokari inga bata citar da yarinyar ba dan yarinyar tana bani tausayi sosai.ga rashin uwa ga uba makaho ga kuma matar uba muguwa haka taita saƙe saƙe harta isa gidanta.


Sai bayan sallar isha'i fatima ta gama wankin, tunda sanda ta dawo makaranta ankusa magriba aka sata yin wanki. da yake tana period shiyasa bata tsaya yin sallah ba wankin taitayi harta gama.aiko a gajiye ta gama gaba daya jikinta yaita ciwo ga yinwa. ba shiri ta shiga ɗakin baba ta ɗakko abincin daya aje mata,dayake wunya na cinta bata lurada kadan baba yaci abincinba tahau ci kawai. ta gama tasha ruwa abunta aiko bacci ya dauketa a dakin.


Mama kande kuwa kota kanta bata karabiba, ta samu wata sabgar ta manta da fatima ko tinanin wai taci abincinma batayiba.Fatima a ɗakin baba ta kwana ranar aiko asubar fari ta tashi ta shiga yin ayyukanta. ta samu taje makaranta da wuri yau alhamis ba islamiyya amma inta dawo da yamma zasuje bara da baba.


Aiko kafin mama kande ta tashi ita harta tafi makaranta ma. sabida inta tashi ta ganta zata iya hanata zuwa tunda baso take taga tana karatuba, wai ita a ganinta inta barta taje zata iya zama wata a rayuwa sabida ta gane yarinyar nada ƙwanya.


''Jamila ga yar makaho nan Zuwa ɗaya daga cikin ƴan group din jamila ta faɗa. dama zuwanta suke jira sun haɗa group ''ke zonan jamila ta faɗa tana hararar ta, mariya na gefanta jira take kawai a bata umarni ta aiwatar da abunda takeso.


Karasowa tayi jikinta a sanyaye ''gani'' ta faɗa kanta a kasa ke dago kai dan ubanki idonta harya dau ruwa ta dago.tana dagowa jamila tacewa mariya aikata abunda ya dace mubar wajan nan. aiko Mariya dama kiris take jira ta daga hannu da karfin ta zata mari fatima. taji an rige hannu kamm ta bayanta sannan an murɗoshi ya lanƙwasa ''wayyo Allah'' hannuna ta faɗa da muguwar ƙara. gaba dayan su hankalinsu ya koma kansa ba kowa bane sai sir aminu ashe duk abunda suke yana sane dasu, haba sir maiyasa kake takura mana ne haka'' ka barmu muyi abunda mukeso indai baso kake kaima ka rasa aikinkaba a makarantar nan.


Jamila ta faɗa tana murguɗa masa baki'' ransa ya baci sosai ya saki hannun mariya ya yo kan jamila da bulalar hannunsa, ya shiga zuba mata a jiknta da karfinsa aiko saita fara ihu tana cewa wallahi saiyasan wadda ya daka a makarantar nan, yai mata shegen duka saida ya gama dukanta yaji sanyi a ransa.


Sannan ya fara magana'' idan kin tashi sawa a koreni'' kisa a koreni gaba daya a garin ma ba iya makaranta ba stupid girl. ke kuma ya nuna mariya data riƙe hannunta tana kuka yace'' wannan kaɗan kika gani naso ace hannunki karyewa yayi, gobe ma ki kara gwada marinta kika abunda zan miki. ku kuma ya nuna sauran yace'' ku ci gaba da biye musu kune zaku sha wahala ku tafi ku bani waje. jikinsa na rawa sukabar wajan itako jamila tunda aka zaneta ta tafi tana kuka tana cewa zaisan wadda ya daka.


Fatima na tsugunne a wajan ta kasa kwakkwarar mosti kanta a ƙasa. fatima tashi ki tafi aji banaso kisa wannan abun a ranki ki kwantar da hankalinki,babu abunda zai faru dake kinji ko tashi ki tafi. bata ce masa komaiba, bata kuma kallesaba ta miƙe tashiga aji.ranar dai karatun kawai jinsa take,amma bata fahimtar komai sai tunanin abunda ya faru tsakaninta dasu Jamila da sir Aminu.


mu hadu a page 3







Kai ! kai ! wani irin kamshine haka ban taba jin irinsaba. kai kawata akwaiki da zolaya turaran wutar company asuf empire kenan, haka yake da mugun kamshi kawata. sannan company asuf emoire ba iya turaran wuta sukeda shiba akwai kabbasa spray, oil perfume, vip spray da sauransu. domin neman ƙarin bayani ku tuntubi nember nan kamar haka ''***'' saimun jiku.