JA DA BAYA...

The family

by @meelahbazata978

*JA DA BAYA...*  
*Book 1*  
*Page 9✍️*  
*Meelah Bazata*

***



Zaune suke a falo gaba dayansu, ummee jauhar da Kuma afeef. 
Yaro ne Dan kimanin shekara uku, wasa yake tayi afalon Yana banna, yai Nan yai nan se wasa yake.

Jauhar ce tace "ummee wai har yanzu abubuwannan basu Dena faruwa ba? 
Duk da abinda yafaru a shekarun baya? 
Kuma Ayzaan ya hakura da aikinnan, Amma abubuwa basu daina faruwa ba? 
Yanzu inba Dan Allah yatsare ba, da yanzu Ayzaan baya Raye. 
Amma Kuma duk da haka sunbar masa tabo Wanda bazai goge a zuciyarsa damu baki daya har abada. Tafada kuka na kufce mata.

Ummee ce tace cikin matukar sanyin jiki itama muryar ta da alama kukan Yana so ya kubce mata "komai zai wuce,Amma ita Kadai tasan irin kuncin datakeji a zuciyarta duk sanda ta tuna abinda yafaru,abu daye ke sassauta mata in ta tuna cewa Ayzaan Yana raye,Amma tana matukar tausaya masa.
Tana Kuma jinjina yadda zasu warware sirrin da suka kulla aboye,yanzu Kuma Taya zasu fahimtar da mutane?
Anya basu sa rayuwar wasu a hadari ba kuwa?Shi aduk sanda abin ya bayyana dawani Ido zasu Kalli mutane?
Wannan tunanin take tayi a zuciyarta,dakyar ta iya Bude Baki tace"
Amma ahalin yanzu Babu wacce nake tausayawa akullin kamar Inarah.  
Wannan aiki nata sam banso ba, Sam tafara aikinnan ba. 
Amma shiya daurata akan aikin sannan Abbienku shi ma yabada goyon bayansa, Kuma gashi da alama itama irinsa ce. 
Bai duba illar da aikin yabar masaba, Amma komai zai wuce da iKon Allah. 
Inshallah.

Haka jauhar tace "tare da fadin "Afeef taso a wurinnan. 
Ummee ce tace "kinsan shi akwai son wasa. 
Suna cikin magana sukaji anbude kofar falo.

Bude kofar yayi da sallama ya shigo falon.  
Aikuwa da gudu Afeef yakaraso wajansa ya rungumesa Yana fadin "uncle. 
Wani murmushine ya kufce masa, murmushi Mai tsananin kyau hakika kyakykyawane na hakika,yanada Wani irin kyau Mai sanyi,daga yanayinsa zaka fahimci miskiline,yanada tsawon ba laifi matashine Wanda zaikai shekara 30, daukar yaron tare da shafa kansa.

"I miss you" yafada Yana karasawa falon ya zauna.  
"Didi barka da Rana, yawwa bobo, yakake? lfy" shine abinda ya furta Yana yiwa Afeef wasa.  
"Ummee barka da gida" kallonsa tayi tai murmushi "barka Zaki katashi kenan?"  
"Eh ummee"

Ummee tace "ga abinci can katashi Kaci"  
"A'a ummee bazan iya cin abinci ba, Amma zansha tea."  
Didi ce tatashi ta hada masa tabashi.  
Ya amsa tare da fadin "nagode Didi." 

Hira suka cigaba dayi inda shi Kuma yake Shan tea dinsa a hankali duk da baisa musu Baki Amma Yana sauraransu.  
Wannan ba sabon abu bane agaresu, tunda sunsan halinsa na rashin son magana.

Jauhar tace "bobo yaushe ne wasanku?  
"Nan da karshen wata, inshallah zantafi."  
"Masha Allah, Allah yabada nasara akai."  
"Ameen" ya furta.

Jauhar tace "ummee wai lilly bata dawo ba? tunda nazo bangantaba, da tana nan da yanzu gurinnan yacika da suturu.  
Kinsan bangaya mata yau zandawo ba, mamaki nakeso na bata. 
Kuma danashiga gun Ammie tace min yau ta fita da wuri.

Ummee tace "yanzu Zaki ganta indai Inarah ce."  
Aikam basu gama maganar ba suka ji sallamarta tare da karasowa falon da gudu. 
Tafada kan jauhar tana fadin "Didi I miss you so much, shine Baki gayamin Zaki zo ba, Ina Afeef?  
"Gashin can ajikin Bobo."

Dasauri tawaiga tana fadin "laaa Yaya dama kananan bangankaba, nadauka baka dawo ba."  
Kallonta yayi da miskilallun idanuwansa Yana fadin "to seki ajiye."  
Tabe fuska tayi tana kallon ummee tare da fadin "ummee kingansako."  
Murmushi ummee tayi tare da fadin "ba ruwana."  
"Karna Shiga nazo naji kunya."  
Dariya Didi keyi sosai sabida tasan halin Ayzaan bakar magana abakinsa kamar me.  
Waigawa tayi tace "Didi kingansako."  
Itama Didi rufe bakinta tayi tana fadin "ba ruwana nidai."
Sanin halin dukkansu su biyun yanzu daya zaiwa daya abu Amma inka shiganma daya kaine zakaji kunya,shi Kuma Ayzaan indai bakar maganace kamar nikan mahauta haka yake,bazaka taba cewa Yana magana ba,Amma in ya yanko magana se ka rasa me zakace.

Mikewa yayi Yana kwantar da Afeef tare da fadin "zanje Wani wuri ummee."  
Adduar dawowa lfy sukai masa Baki daya.  
Inda Inarah ta Mike tare da fadin "yaya zan rakaka."  
"A'a" ya furta.  
Takara cewa "Dan Allah fa Yaya."  
Jinjina Kai kawai yayi, Dan yasan kadan daga aikin ta inyatafi ta dasa kukan rashin dalili, shikuma a duniya baya kaunar kukanta.aikam da gudu ta ruga tabi bayansa tare da fadin"yawwa Yaya kasan me?
Ni da ba akuya ba Taya zansan me? Yabata amsa"
Haba Yaya Dan Allah fa"ta fada cike da shagwaba.
Tare suka jera suka fita,Inarah na bashi labari.

Dariya kawai Didi tayi tare da fadin "lilly dai bata girma kullin cikin shirme, nayi mamakin ma ta yadda ta iya aikin jarida, Kuma take komai cikin kwarewa."

Murmushi kawai ummee tayi tana cewa "wannan shirmen datake nunawane yasa kowa yake ganin bazata iya komai ba. 
Amma inka karanceta tana da matukar basira da wayau Amma ahaka mutane zasuga kamar tana da shirme amma komai nata a lissafe yake,Nan Zaki Gane haka."

Mikewa jauhar tayi tare da fadin "ummee bari naje gurin innah."  
Da to ta amsa mata tare daukar Afeef tana shigewa bedroom dinta.  
̶ ̶ ̶ ̶ ̶ ̶

1. *Me ya faru da Ayzaan a baya?* Me yasa Jauhar ta ce "inba Dan Allah yatsare ba da yanzu baya raye?