JA DA BAYA...

The case

by @meelahbazata978

JA DA BAYA...
Book 1
Page 10✍️


Inarah ce tafe a hanyar ta ta zuwa ofishin yan sanda, Dan tattaunawa game da case din daya faru jiya.
abin ya matukar tsaya mata arai sosai. barin data tuna yadda mahaifiyar yarinyar taje kuka se taji gaba daya tausayi ya kamata.
gashi Kuma jikar babah adama ce matar datake kallo amatsayin kaka.

domin baba adama tana kaunar ta sosai, tun tasowarta ta Wani sa'in itace wacce take zama da ita tayi ta bata labarin da da  tsuniya shiyasa suka Saba da baba adama.
Hakan yasa tadau damarar duk yadda za'ayi setaga karshen case din, sannan Kuma  taga Wani mataki hukuma zasu dauka akan al'amarin.

Sedai zuwan ta batakai ga shiga ba taci birki,Dan ganin gawar da aka fito da ita daga station din ,Kuma da alama gawar Mai laifin ne, kamar hadin Baki take yan jarida sun hallara agun inda suke daukar abin da ke faruwa.

Fitowar d.s.p ne yasa hankalin yan jaridar ya koma kansa, inda kowa ke kokarin daukar abinda ya samu,da sauri inarh ta Ciro wayar ta ta saita camera ,inda kowa ke kokarin tambayar yan sandan akan abinda ke faruwa.
Yallabai mezaka iya Fadi game da wannan al'amari? duba da yadda aka kama Mai laifi sannan Kun kawosa gurinku yanzu Kuma ga gawarsa? Shin me yafaru ne?

d.s.p ne yabudi Baki tare da fadin mun kawo Mai laifin Kuma mun kullesa a ofishi sedai kuma lafiya lau yake ,Amma wayewar gari muka ga gawarsa ,yanzu haka za'a tura gawar gurin bincike Dan ganin menene musabbabin mutuwar in mungama bincike, zakuji bayani.

Yafada tare da wucewa agurin yan jarida na yallabai Karin tambaya daya yallabai,Amma Ina yawuce inda sauran suka dauki gawar suka sa amota suka wuce.

Jiki ba kwarin Inarah ta juya tare da shiga mota ta koma gurin aiki.

Tana Isa ta tarar da zarah azaune. karasawa kusa da ita tayi tazauna a kujerar ta.
zarah ta dago ta kalle ta tare da furta"lilly yadai naga jikinki duk yayi sanyi?
Hmmmm "ta furta tare da fadin"kibari kawai besty jikina duk yayi sanyi.

Kinsan case din yarinyar danaje jiya Wanda aka tsinci gawarta?tace "eh
To yarinyar jikar babah adama ce,yanzu naje Dan Jin ya ake ciki game da case din, se natarar da gawar Mai laifin da aka kama wai ya mutu a station din,gaba daya jikina yayi sanyi.
Zarah tadago da kalle ta da mamaki tace "ya mutu Kuma?how?tayaya ma za'ace ya mutu?

hmmmm kibari kawai Inarah ta furta "tare da da fadin"nafara tunanin akwai Wani abu abayan wannan case ,gaba daya kaina ya kulle besty.
Zarah tace"gaskiya nima nayi tunanin haka besty Amma bazamu bar abin ahakaba, muci gaba da bibiyar case din mugani,amsawa tayi da"Inshallah Sena binciko gaskiyar wannan lamarin, tare da mikewa ta nufi ofishin edita.

Zaman dai a gurin aiki aranar Sam baiyiwa Inarah dadi ba,hakan yasa da wuri ma ta k⁸oma gida ranar.

Tana shiga falon,  Ammie ce a zaune kayataccen falon tana shan shayi.  
Mace ce mai kwarjini da Kamala , kallo daya zaka mata kaga natsuwa atare da ita ga glass a idonta ga Wani Dan karamin littafi tana Karanta wa,kamar dai littafin adduo'i, sanye da sutura ta alfarma mai tsada. 

Kallon Inarah tayi tace "Lilly kin dawo? Me yasa fuskar ki ta canja haka?"  
Inarah ta yi murmushi ta ce "aiki ne kawai Ammie. Na gaji kadan,tafada tare da shigewa daki."

dakinta tashiga tare da aje jakarta tare da fadin washh tana kwanciya akan gado
Daki ne mai girma, dagani kasan dakin yar gata ne,Gefe guda kuwa littattafaine a aje, da alama tana da son karance karance.

Inarah ta ajiye jaka ta zauna a kan gadonta. 
Tunanin gawar da ta gani a station bai bar ta ba mamaki takeyi sosai suk da tasan hakan abune Mai sauki agurin ubangiji Amma setakejin aranta Taya za'ace ya mutu bayan lafiya aka tafi dashi station din?. 
Ta ciro wayarta ta duba hoton yarinyar da aka kashe. Hoton ta daukesa ne aboye,  ta dauka ba tare da an Lura ba.

Koface ta bude. Tare daShigowar Mahbub .  
yana sanye da wando da riga na Shan. Sai kamshin turare yake.  
Kallonta yayi ya ce "lilly me ya faru? Naganki so silent?"  
Inarah ta ce "komai lafiya. Ayyuka ne kawai a ofis."  
Mahbub ya zauna kusa da ita ya ce "kin san, idan akwai matsala ki fada min. Ni dan uwankine banason ganin kina damuwa."

Inarah ta girgiza kai. "Nagode  yayana. Zan iya kula da kaina,kana damuwa game da rashin lfy nane nasan,ai naji sauki baka ganiba yaushe rabon ciwon ya tashi tafada cike da shagwaba."  
Jinjina Kai yayi tare da fadin" duk da haka kisake kulawa kinji lilly.
Ta amsa da inshallah.tashi yayi ya fita. Tana tsokanarsa Yaya "Yaya Ina auntyna dariya kawai yayi tare da fita.
Bayan ya fita, Inarah ta koma ta kwanta. 

Kwance take a kan kayataccen gadonta,tanajin yunwa,Amma ba ta da sha'awar cin abinci komai Bai Mata dadi sam,dama Ayzaan shine mai taimaka mata a irin wadanda abubuwan insun shige mata duhu yau Kuma bayanan.  

Ammie ta zo dakin ta zauna kusa da ita. 
shafa gashin ta tayi tare da  cewa "Inarah, tun bayan dawowarki yau Sam Baki da sukuni,Kuma kinsan damuwa abinda take haidar Miki,meyake damunkine?

Inarah ta tashi  tare da gyara zama ajikin Ammie tana cewa" Ammie babu komai. Kawai aiki ne, yadan cakude,kinsan nabaki labarin case din jikar babah adama,to Ammie yau nakoma station din Shima Mai laifin ya mutu shine duk jikina yayi sanyi narasa Wani tunani zanyi akai."
Ammie tace"to kibi komai a sannu ita Kuma kiyi mata addua naga labaran ai abin baiyi dadi ba,baba adama mutuniyar kirki ce Amma kidena damuwa kinji Rabin Rai.
Murmushi tayi tare da jinjinawa Ammie Kai tana Kara lafewa ajikinta.
Tashi Ammie tayi ha hada mata tea ta zauna tana bata abaki tanasha cikin kulawa.
Bayan tagama Sha tace"Ammie yausha Abbie zaidawo?
Gobe inshallah "ta fada tare da tashi ta gyarawa Inarah kwanciya ta rufe ta tare da sumbatar goshin ta.

Kwanciya tayi tana tunani har zuwa Wani Dan lokaci, abubuwan sunfara caza mata Kai,kanta har yasoma ciwo gashi tana da fita 
Gobe Lahadi  Tana da hira da Alhaji Gali. 
Ta dauki notepad dinta ta danyi wasu rubuta ta Dan jima tana rubutu,kafin ta rufe notepad din.

Sannan ta kashe fitila ta yi addu'a ta kwanta bacci.

Alhaji Gali matawalle shaharren dan kasuwa ne,mutunne Mai dukiya, sosai yanada yara uku babban dansa shine haisam se ameerah da husnah.
Yarane fandararru marasa kunya Wanda gata yai musu yawa.

Alhaji Gali matawalle Yana da son Mulki shiyasa ya shiga harkar siyasa sedai Allah baya basa nasara akan duk takarar dazai shiga,yayansa duk ba a Nigeria sukayi karatu ba,haisam kusan duk a turai yayi rayuwarsa shiyasa duk wasu dabiunsu ya kwashe hadda Kari shaye shaye 
bin mata yamai dasu kamar ruwan Sha ,haka itama ameerah sai bin kawaye da yawon club club.
dama dama husnah acikinsu haka Kuma Bai yarda kagaya masa aibun yayansa ba Sam basa laifi komai sukayi daidaine.

Ayanzu haka yashiga siyasa Dan takarar gamnan jaha yake nema, sedai a mu Amalance ,ta Wani fannin mutunne Mai sauki ga jama'a, baya kasar,Dan yadau dogon lokaci bayanan dawowarsa ne yasa gidan jaridar haske maganin duhu suka bukaci yin Hira dashi.Kuma yabasu wannan damar Wanda aka tura Inarah domin yin Hira dashi.
Yanzu haka yayansa duk sun dawo Nigeria,Kuma matar sa daya itace hajiya kaltum.

Ayanzu sunyi magana da Kuma yabawa Inarah lokaci da komai inda zata har gidansa domin tattaunawa Wanda tattaunawar tasu zata kasance ranar sunday,jibi kenan.