KADDARAR SOYAYYA (THE DESTINY OF LOVE)
by @sheolly
Chapter Four: Gidan Alhaji Bashir (The House of Alhaji Bashir)
A wani bangare na birnin, akwai wani katafaren gida da ya fi yawancin gidajen unguwar girma da kyan tsari. Gida ne da ke nuna alamar dimbin arziki da daukaka.
Mai gidan kuwa shi ne Alhaji Bashir Ahmad, fitaccen attajiri kuma babban dan kasuwa wanda ya mallaki kamfanoni da kadarori a ciki da wajen Najeriya. Duk da irin tarin dukiyarsa, ya kasance mutum mai saukin kai, mai son addini da kuma mai tsananin kaunar iyalinsa.
"Family is my greatest treasure."
Matar Alhaji Bashir ita ce Hajiya Aisha, kyakkyawar mace mai hankali da tarbiyya. Soyayya da mutunta juna sun dade suna tsakanin ma'auratan, kuma kowa ya san irin kaunar da Alhaji Bashir yake yi mata.
Allah Ya albarkace su da 'ya'ya uku.
Babbar diyarsu ita ce Maryam, sai 'yarsu ta biyu Amina, sannan auta kuma tilon namiji, Muhammad.
Muhammad saurayi ne mai shekaru ashirin da shida, dogo, kyakkyawa kuma cike da kwarjini. Duk inda ya shiga, mutane kan juya su kalle shi saboda cikar kamanninsa da yadda yake tafiya cikin izza.
"He was handsome, confident, and fearless."
Sai dai Muhammad yana da wata dabi'a da ke damun iyayensa. Ba ya son a yi masa katsalandan a rayuwarsa. Idan ya yanke shawara, da wuya ya saurari ra'ayin wani, ko da kuwa iyayensa ne.
Hajiya Aisha kan yi masa nasiha akai-akai.
"Muhammad, yaro na, mutum ba ya rasa komai idan ya saurari shawarar iyayensa."
Muhammad ya yi murmushi kawai.
"Ammi, don't worry. I know what I'm doing."
Alhaji Bashir yana son dansa fiye da komai, amma ba ya nuna hakan sosai. A ganinsa, nuna tsauri wani bangare ne na tarbiyya.
Ya kan ce,
"A real man must learn responsibility before leadership."
Muhammad bai san cewa mahaifinsa yana boye masa tsananin kauna ba. Shi kuwa Alhaji Bashir yana addu'ar Allah Ya shiryar da dansa, ya sa ya zama mutum mai sauraron shawara da fahimtar rayuwa.
A wannan lokacin, babu wanda ya san cewa kwanaki masu zuwa za su kawo wani sauyi da zai canza rayuwar Muhammad har abada....
Muhammad shi ne auta kuma tilon namiji a gidan Alhaji Bashir. Saboda haka, Hajiya Aisha tana matukar kaunarsa fiye da komai. Tun yana karami take rainonsa da kulawa ta musamman, har yanzu kuma zuciyarta ba ta iya jure ganin an tsawata masa.
A duk lokacin da Alhaji Bashir ya yi wa Muhammad fada saboda wata kuskure, Hajiya Aisha kan shiga tsakaninsu.
"Alhaji, don Allah ka yi hakuri. Yaro ne, zai gyara."
Alhaji Bashir ya kalle ta ya girgiza kai.
"Aisha, wannan shi ne kuskuren da kike yi. Kina kare shi a ko da yaushe, shi ya sa ba ya son sauraron magana."
"You are spoiling him too much."
Hajiya Aisha ta dan hade fuska.
"Ba shagwaba nake yi ba, Alhaji. Ina dai son kada ka yi masa tsauri."
Alhaji Bashir ya sauke numfashi.
"Ni ma ina sonsa, fiye da yadda yake zato. Amma idan ban gyara halinsa ba yau, gobe rayuwa ce za ta gyara shi cikin wahala."
"A father's love is not always soft."
A lokacin ne Muhammad ya sauko daga bene, sanye da bakar wando da farar riga mai matukar kyau. Hannunsa dauke da mukullin motarsa, alamar zai fita.
Da ya hango iyayensa suna magana, ya tsaya na dan lokaci.
"Assalamu Alaikum, Dad...mom ."
"Wa Alaikumus Salam," suka amsa tare.
Hajiya Aisha ta yi murmushi.
"Muhammad, ina za ka?"
Ya mayar da mukullin motarsa cikin aljihu.
"I'm going to see a friend. I won't be late."
Kafin Ammi ta yi magana, Alhaji Bashir ya ce da murya mai natsuwa,
"Muhammad, ka tuna da abin da na gaya maka jiya?"
Muhammad ya dan yi shiru, sannan ya ce,
"Eh, na tuna."
Amma daga yanayin fuskarsa, Alhaji Bashir ya fahimci cewa dansa bai dauki maganarsa da muhimmanci ba.
Ya kalli Muhammad cikin ido.
"Wata rana za ka fahimci cewa shawarar iyaye ba takura ba ce, kariya ce."
Muhammad bai ce komai ba. Ya yi murmushi kadan, ya yi sallama sannan ya fice daga gidan.
Alhaji Bashir ya bi shi da kallo har sai da motarsa ta fita ta kofar gida.
Sai ya ce a hankali,
"Ya Allah, Ka shiryi ɗana, Ka sa ya zama abin alfahari a gare mu."
Hajiya Aisha ta amsa da hawaye kadan a idonta,
"Ameen."
(Muhammad's Lifestyle)
A wani babban lounge da ke cikin birnin, karar kida mai sanyi ta cika wajen yayin da wasu matasa ke zaune a wani bangare na musamman da aka tanada domin manyan mutane.
Su ne abokan Muhammad — yara da suka fito daga iyalai masu arziki, wadanda suka saba da rayuwar jin dadi da kashe kudi ba tare da tunani mai yawa ba.
A tsakiyarsu akwai Muhammad.
Ya zauna cikin nutsuwa, sanye da kaya masu kyau, amma kamar yadda aka saba, ba ya yawan magana. Ko a cikin abokansa, Muhammad ba shi ne wanda zai fi dariya ko hayaniya ba.
Daya daga cikin abokansa ya kalle shi yana murmushi.
"Guy, har yanzu ka zo nan kana kamar bako a cikinmu."
Wani ya yi dariya.
"Wallahi Muhammad ba ya canzawa. Ko muna tare da shi kullum, sai ka ji kamar yana da wani sirrin da ba ya fada mana."
Saboda kamanninsa, duk abokansa suna da wani suna da suke kiransa da shi.
"The Prince"
Wannan shi ne nickname dinsa a cikin abokansa, saboda yadda yake da kwarjini, nutsuwa da kuma rayuwar alfarma.
Amma duk da cewa abokansa suna son hayaniya da nishadi, Muhammad ba ya bin komai da suke yi. Idan wani abu bai masa dadi ba, ba ya shiga.
"I know my limits."
Babban abokinsa, Fahad, ya fi kowa kusanci da shi.
"Bro, ka san kana da matsala?"
Muhammad ya kalle shi.
"Matsala kuma?"
Fahad ya yi dariya.
"Eh. Duk yarinyar da ta gan ka tana son saninka, amma kai kamar ba ka da zuciya."
Sauran suka yi dariya.
Gaskiya kuwa, Muhammad ya kasance daya daga cikin samarin da suka fi daukar hankali. Kyawunsa, kudinsa da kuma yadda yake tafiyar da kansa sun sanya mutane da yawa sha'awar saninsa.
A social media ma, duk lokacin da ya saka hoto, sakonni daga 'yan mata suna yawaita.
Amma Muhammad ba ya daukar hakan da muhimmanci.
A gare shi, soyayya ba wani abu ba ce da yake nema a yanzu. Abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne rayuwarsa, aikinsa da kuma burinsa.
Amma bai san cewa akwai lokacin da kaddara za ta kawo masa wata yarinya da ba za ta yi masa kallon dukiya ko kyau ba
sai dai zata kalli zuciyarsa
Da dare ya fara sauka a birnin zariya, Muhammad yana tare da abokansa a wani wuri na musamman da suke yawan zuwa. Kamar yadda aka saba, sukan taru domin nishadi da hira.
Muhammad yana zaune cikin nutsuwa, hannunsa rike da sigari yayin da yake kallon abokansa suna dariya.
Fahad ya kalle shi ya ce,
"Bro, ka san Dad dinka ba zai ji dadin ganin wannan ba."
Muhammad ya yi murmushi kadan.
"Fahad, I'm old enough to make my own decisions."
Fahad ya girgiza kai.
"Ka dai san Baba naka yana son ka zama daban."
Muhammad bai amsa ba. A gare shi, yana ganin shi ne ya fi sanin rayuwarsa.
Bayan wani lokaci, ya bar wurin ya koma gida.
Da ya shiga harabar gidansu, sai ya lura da wani abu daban. Motar mahaifinsa tana tsaye a waje, alamar yana gida.
Muhammad ya shiga falon yana tsammanin zai wuce dakinsa, amma sai ya ji muryar mahaifinsa.
"Muhammad."
Ya tsaya.
"Na'am Dad."
Alhaji Bashir yana zaune cikin nutsuwa, amma fuskarsa tana nuna rashin jin dadi.
"Zo nan."
Muhammad ya zauna.
Alhaji Bashir ya ajiye abin da yake hannunsa sannan ya kalle shi.
"Shin ka san abin da ya fi bani haushi?"
Muhammad ya yi shiru.
"Ba kudinka ba ne, ba motarka ba ce, ba kuma abokanka ba ne. Abin da yake damuna shi ne yadda kake ganin ba ka bukatar shawarar kowa."
Muhammad ya sauke numfashi.
"Dad, I'm not a child anymore."
Alhaji Bashir ya girgiza kai.
"Haka kake tunani. Amma babban mutum shi ne wanda ya san lokacin da zai saurari shawara."
Sai ya nuna masa sigarin da aka samu a motarsa.
"Muhammad, wannan ne abin da kake yi da kanka?"
Nan take Muhammad ya yi shiru.
"Ban hana ka jin dadi ba. Amma akwai abubuwan da za su iya lalata maka rayuwa idan ba ka kula ba."
Muryar Alhaji Bashir ta dan yi sanyi.
"Na tara duk wannan dukiyar ba domin ka zama mutum mai girman kai ba. Ina son ka zama wanda mutane za su yi alfahari da shi."
A lokacin ne Hajiya Aisha ta fito daga dakinta.
"Alhaji..."
Alhaji Bashir ya kalle ta.
"Aisha, ina sonsa. Shi ya sa nake magana."
Hajiya Aisha ta kalli Muhammad cikin tausayi.
"Muhammad, ka saurari Dad dinka."
Muhammad bai ce komai ba. Ya mike tsaye.
"Okay, Dad."
Ya juya ya nufi dakinsa, amma kalaman mahaifinsa sun tsaya masa a rai.
A wannan daren, Alhaji Bashir ya yanke shawarar cewa dole ne ya dauki wani mataki domin taimaka wa dansa ya canza...