The mark shadow
JA DA BAYA...
Book 1
Page 11✍️
Meelah bazata
***
A safiyar yaune Kuma akatashi da labarin tsintar gawar mutane har guda hudu wadanda akayiwa mummunar kisan gilla,sedai ankasa gano gawar su waye. Wanda yan sandan bincike sun karasa gurin domin yin bincike akan hakan.
Isarsu gurin da aka zagaye da kyalle,sun karasa suna nazarin komai agurin tare da daukar hotuna.
ansamu Wani kati ko sheda da zaa iya gano ko mutun dayane aciki?
"A'a yallabai "baa samu komaiba.
Yallabai"wannan mummunar kisane ,sannan anyi amfani da wasu sinadarai sannan aka jefa gawarwakin a ruwa irin kisa haka Yana da wuyar samun shaida.
Kisa irin wannan ana matukar Shan wahalar samun wata hujja ajikin wannan gawar domin bazaa iya samun hujja ba ma acikin sati daya.
Dagowa yayi tare da fadin ku dauki gawar ku kai morgue domin yin bincike.
za:a cigaba da bincike domin gano ko su waye sannan zamu gano Wanda ya aikata laifin.
D.I.G Muhammad Mai rabo,zaune acikin ofishinsa Yana nazari akan file din da aka kawo masa,dagowa yayi ya kalle sa tare da fadin yanzu ya ake ciki game da binciken?
Yallabai har izuwa yanzu bamu samu ko wace irin hujja akai ba Amma muna cigaba da bincike akai.
Shikenan kaje nasan yadda zanyi zan damka case din a hannun mark.
yes sir ya furta"tare da fita daga ofishin.
Fitarsa yasa d.i.g ya daga wayarsa ya kira wata number. dauka akayi tare da fadin yes sir.ina bukatar ganinka shadow.domin kuwa akwai Wani case Mai daure Kai , shiyasa nake bukatarka.
banji me akace a dayan bangaren ba,ya amsa da fadin shikenan tare da aje wayar ya Kara dauko file din tare da Kara dubawa.
Zaune suke a cikin Wani office na sirri.
mutane biyu ne aciki Amma mutun daya zan iya karas da kamanninsa wato Mai girma d.i.g. dayan kuwa Wani saurayi zan kira ko mutun,domin dai gaskiya ya wuce a kirasa da saurayi sedai mutun haka Wanda zai iya haurawa shekara ar'ba'in.
Zaune suke ga computer agabansu ga Kuma wasu takaddu gabansu.
Shadow Ina da wata tantama akan wannan case din da dole akwai bukatar taka tsantsan,aikin ka na sirri ne Amma wadancan mutanen sun matsa akan sanin waye kai,dole mu Kara kulawa.
har zuwa lokacinKuma Wanda ake kira da shadow din baice komaiba.
Jawo Wani file yayi ya Bude wasu hotuna ne aciki da Wani Dan karamin abin zobe da alama irin kwalliyar azurfa ne.
Wadannan sune kadai abinda aka samu atare da gawarwakin Wanda har ila yau bamu Gane ko suwaye ba Ina bukatar samun cikakkun hujjoji Nan da sati daya mikewa yai tare da Sara masa ya dau file din ya fita.
Abinda yaban mamaki har suka gama magana bance ga abinda Wanda ake kira da shadow yace ba.
abinda zan iya karaswa ajikinsa kawai shine Yana da Dan jiki Sannan yanada tsawo Amma Babu Wani abu daya Dana iya gani ajikinsa.
Yana fita yashiga mota tare da wuce wa. Wani matsakaicin gida naga ya nufa Yana zuwa aka Bude masa gate ya shiga.
Wani matashine yakaraso gurinsa da sauri tare da amsar abinda yake hannunsa,tare suka shiga falon gidan inda wata dattijuwa ce azaune akan kujera,rike da carbi a ahannunta tana tasbihi.
karasawa yayi kusa da kafarta yazauna inda ta shafa kansa tare da fadin babana andawo?
daga mata Kai yayi tare da fadin" eh mama.
to Maza Allah yayi albarka. Ameen ya amsa tare da shigewa Wani ɓangare da ke cikin falon.
Wannan matashine kuwa Dana ji wacce suka kira mama ta kira sa da bilal,da alama kaninsa ne, mama ce tace Maza bilal kadau abincin yayanka katafi ka Kai masa daki to mama ya furta tare da daukar farantin yashiga ya aje masa.
alokacin shi Kuma yashiga ban daki,jawo kofar bilal yayi tare da fitowa,inda wannan daki nasa ko mama ,mawuyacin abune ta shigesa,bilal ne kadai yake shiga wannan daki se Kuma mamallakin dakin Wanda har yanzu banji ankira sunansa ba.
Yana fitowa daga bandaki ya gyara jikinsa tare da sa wasu kayan Shan iska to ananne fa zan ce muku nayi gaskiya da bankirasa da matashi ba,domin kuwa sedai akirasa da matashin dattijo,domin zai iya Kai shekara ar'ba'in zuwa ar'ba'in da Wani abu.
Zama yayi abakin gadon tare da Bude computer Yana dube wasu bayanai waya yadauka ya danna wata number tare da yin kira ana dauka yace akwai wasu hotuna da zan tura maka yanzu Ina bukatar bayanai akansu,daga Nan zuwa gobe.
inshallah yallabai",daga dayan bangaren aka amsa.
Kashe wayar yayi tare da Kara duba hotunan da kyau tashi yayi naga yashiga Wani daki Wanda Kai bazaka taba tinanin daki bane agurin Amma Yana sa yatsun hanunsa kawai kofa ta Bude yashiga.
Da alama dakine na bincikene,
Dakin da duhu sosai,hasken dakin ya kunna.
Haske ne ya gauraye ko Ina na dakin,dakin Babu kura da alama ana yawan amfani dashi.
Tebur ne dauke da hotuna akai da alama hotunan wasu case ne ya dayaba warware wa koyake kan warwarewa,ga Kuma whiteboard Wanda ya ja wasu layika ajiki,Gefe Kuma Wani safe box ne Wanda ya Bude yasa Wani abu a ciki sannan ya daura wannan file da yashigo dashi akan teburin.
Computer dinshi ya Bude tare da fara duba aiki acikinta,yadau lokaci Yana nazari kafin ya dauko wata waya ta sirri tare da danna wata number ,bayan an dauka yace"ka bincika min dukkan bayanan Dana tura maka daga yau zuwa gobe,kituramin report din"
Ya katse Kiran.
Kwashe komai yayi ya aje tare da kashe fitilar dakin yayi duhu.
Kulle dakin yayi Yana fita ya danna Wani makunni kofar ta rufe kamar bata agurin.
Fitowa yayi farfajiyar gidan Yana tsaye Yana kallon guri guda Yana nazari,wayarsa yadauka tare da Kiran wata number,ana dauka"coffee kawai yace ya katse number din".
Bayan mintunan da basu gaza biyar ba bilal ya karaso gurin tare da Mika masa Wani Dan karamin cup Mai kyau,amsa yayi tare da jinjina masa Kai,juyawa bilal yayi ya koma ciki inda shi Kuma yabarshi a gurin Yana Shan coffee din a hankali.
Ya dau Wani dogon lokaci agurin yana Shan coffee dinsa,iska ce ta fara kadawa yanayin Yana masa dadin nazari.
Wayarsa ce tayi vibrating ya dakko tare da karawa a kunne.
"Sir ajikin wannan hoton zoben daka turomin tabbas zobe ne na Wanda zamu iya binciken maishi domin kuwa nasamu Wani me irin zoben sedai ya Sanar Dani cewa tabbas wannan zobe anbashi a wata kyauta ta gidan jaridarsu Wanda akalla mutane goma aka bawa wannan zobe,sedai zamu cigaba da bincika muga sauran aka fada cikin girmamawa"
Good job "ya fada tare da cewa zuwa gobe da safe ku bincika sauran mutane Taran Wanda suke da wannan zobe Dan tantancewa".
"Ka turamin bayanan yanzu Hadi da hoton zoben na ainahin ya katse wayar".
Mikewa yayi awurin ya shiga cikin falon,bilal be Wanda har zuwa lokacin baiyi bacci ba ya na zaune a falon ya taso tare da fadin"Yaya akwai abinda kake bukata ne?
A'a"kaje ka Kwanta gobe zaka fita aiki.
Jinjina Kai bilal yayi tare da shigewa daki.
Dakin sirrinsa ya koma Wanda lokacin kusan 1:30 am na dare hotunan da aka tura masa ya sake duba da bayanan.
Tabbas yasan wannan zoben domin yagansa a Wani guri Amma a Ina? Tabbas Yana bukatar Kara dogon naxari akai .
Aiki ya cigaba dayi Wanda Bai bar wannan daki ba har kusan karfe uku na dare,bayan ya rufe dakin ya koma dakinsa ,ban daki ya shiga yayi alwala tare da fitowa ya shimfida sallaya ya tada sallah.