Hs 13
by @legendspen
_Page 13_
A guje suka haura upstairs har Juraij na buge Momi dan sauri, buga k'ofan suka shiga yi Momi na kuka tana fadin. " Senate kar ka kashe kan ka dan Allah."
Magana ya soma musu yana kuka. " Kun ce HASASHEN SOYAYYA na ke, gashi ina ji ina gani za'a kwace min ita, dukan ku babu wanda zai iya kwato min ita."
" Senate ka bud'e kofan nan, ka daina fashe-fashen nan, ka kasa zuwa ka tunkare yarinya ka fada mata kana sonta, wai kai tsoro." Cewan Anas kamar yayi kuka dan haushi.
Bai kula su ba ya cigaba da buge-bugen da yake yi.
Salman ya dube su ya ce suyi baya, suka matsa da karfi ya buga kofar sai gashi ya fadi, inda yake tsaye suka nufa duk dakin kwalba ga hannunsa din da yake digar jini alamun ya tsage.
Cikume rigarsa Juraij ya yi yana cewa. " Mad kawai, akan mace kana k'ok'arin halak'a kanka da rayuwarka." Kafin ya sake shi yana shafa gashin kansa ya ce. " Ka je ka same ta kace kana sonta mana."
Bai bari yaji me zai ce ba ya kama hannunsa suka fito daga dakin, suma suna mara musu baya.
Idanunsa yayi ja har da hawaye a ciki ga hannunsa dake zubar da jini, ganin zasu fita daga falon ne yasa ya ce. " Where?."
" Gurinta." Cewan Juraij yana jan shi.
Turjewa yayi yaki tafiya ya ce. " Me zan ce mata?."
" Kana son ta."
" Tana Makaranta ai."
" Muje gidan idan bata nan sai muje school din."
Juyawa yayi yaga Momi da su Anas yana cewa. " Bazan iya ba, I can't Momi."
Momi ta gyada masa kai ta ce. " Zaka iya, kuje zaka iya."
Jan hannunsa Juraij yayi suka nufi get masu aiki na kallon su, ta karamin kofa suka fita, tafiya kadan suka yi suna tsayawa a bakin get din gidan, kwankwasawa Juraij yayi mai gadi ya bude musu, ganin Senate ne ya saka shi cewa. " Alhaji da kansa."
Murmushi ya kwakulo ya masa Juraij na tambayan shi. " Bhatool tana nan?."
" Eh Yallabai yanzu ta shigo tana masifa."
Basu kula shi ba suka nufi cikin falon.
*Bhatool*
Mai machine yana ajiye ta ta bashi kudinsa ta nufi get, bugawa ta shiga yi tana fadin. " Zaka bude ko sai na balla get din."
Da gudu mai gadi ya bud'e yana cewa. " Ina band'aki ne ayi hakuri Hajiya."
Hararan shi tayi tana cewa. " Yanzu zaka matsamin ne ko sai na buge ka?."
Da sauri ya matsa mata ta shige tana masifa, a falo ta wurgar da handbag dinta tana kwalawa Yaya Karima kira. " Yaya Karima!!."
Yaya Karima tana daki ta kwanta kenan taji kiran, da sauri ta fito tana cewa. " Bhatool lafiya?."
Fashewa tayi da kuka tana zama a k'asa, da mamaki Yaya Karima ta iso gurin ta tana dafata ta zauna ta ce. " Me ya faru?."
Kasa tsayar da kukan nata tayi tana fadin. " Yaya ni na hakura da Makarantan nan."
Cike da mamaki ta ce. " Me kuma ya faru? Me aka miki?."
Nan ta bata labarin komai bata boye mata ko daya ba, ta karashe tana kuka.
Shuru Yaya Karima tayi, gefe guda na zuciyarta na tuna mata da Senate, kafin ta sauke ajiyar zuciya ta ce. " Dago fuskarki ki kalle ni Bhatool."
Da idanunta da suka danyi ja ta dago tana kallon ta.
Yaya Karima ta ce. " To ke waye kike so?."
" Yaya burgeni kawai yake yi."
" Waye ne shi din?."
Shuru tayi kafin tayi magana suka ji sallaman Juraij da Senate, lokaci daya zuciyarta ya tsinke ta kalli Yaya Karima wacce ke sakin murmushi tana fadin. " Yau Senate ne a gidan."
Murmushi ya mata suna k'arasowa cikin falon, gaishe da ita suka yi ta amsa tana tambayar su Momi suka ce tana lafiya.
Idanunsa na kan Bhatool da taki juyowa dan kukan da tayi ya saka idanunta ja.
Yaya Karima ta ce. " Bari na dauko muku ruwa ko." Ta fada tana nufan fridge.
Juraij yayi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa. " Anuty da kin bari daga gida muke fa, dama gurin Bhatool muka zo."
'Dum-dum' haka taji zuciyarta na bugu, yayin da Senate yayi saurin dafe saitin zuciyarsa yana karanto addu'a duba da yanda lokaci daya ya harba masa.
Yaya Karima ta ce. " Laifi ta muku ko?." Ta fada tana dariya.
" A'a mun isa ta mana laifi."
Dubanta Yaya Karima tayi tare da cewa. " Bhatool baki ji ance anzo gurin ki ba."
Jinjina kai tayi tana cewa. " Naji Yaya." Kafin ta mike ta ce. " Ina zuwa bari na shiga daki na fito." Tayi sauri ta yanda kar a ce ta tsaya.
Yaya Karima ta zauna tana duban su ta ce. " Me ya faru?."
Kallon Senate Juraij yayi kafin ya ce. " Anuty wannan na rako fa." Ya nuna Senate kafin ya cigaba da cewa. " Wai Bhatool....." Saurin katsai shi yayi ta hanyar buge k'afarsa yana marairaya ido.
Tsaki Juraij yayi yana cigaba da cewa. " Wallahi Anuty hauka ya fara yi akan Bhatool."
Runtse ido Senate yayi saboda kunyan da yaji lokaci daya ya kama shi, Yaya Karima ta ce. " Ikon Allah, wai Senate har yanzu tsoron ne da kai? Tsoron ma na Bhatool?."
Juraij ya ce. " Hmmm!!! Shi ne yau na jawo shi nace yazo ya fada mata ko zamu samu sauki."
Yaya Karima ta dubi Senate da kyau ta ce. " To idan kana tsoron ta taya zakuyi zaman aure kenan? Ko ka taba ganin inda miji ke tsoron mata?."
Girgiza mata kai yayi, ta cigaba da cewa. " Ka cire tsoro ka ajiye shi a gefe ka tunkare ta da zancen."
Gyada mata kai yayi kafin ta mike ta ce. " Bari na kira ta." Ta nufi dakin da Bhatool ke ciki.
Da sauri ya dubi Juraij zai yi magana ya ga ya ciro waya yana tashi da alama kiransa aka yi.
' Inna'illahi!! ' Ya furta a zuciyarsa kafin yaji wani bangare na zuciyarsa na ce masa. ' Zaka iya, idan baka fada mata ba wani ya rigaka fa kamar yanda wancan ya rigaka' Ji yayi wani kishi ya tokare masa makoshi lokacin da yaji ta ce. < Ce masa nayi ina da wanda nakeso>.
Ko da Yaya Karima ta shiga dakin ta same ta zaune da waya a hannu tana dannawa, kusa da ita taje ta zauna tana cewa. " Bhatool!!!." Ta kira sunanta.
Mayar da hankalinta tayi zuwa gareta baki daya tana amsawa.
" Bhatool baki fadamin wanda kikeso ba?."
" Yaya burgeni kawai yake yi."
" Waye ne shi din?."
" Dan Momi ne." Ta fada tana turo baki gaba ta dauke kai.
" Ke bana son shirmen kin nan fa, dan Momin bashi da suna ne."
" Yaya Karima Senate ne fa."
Sakin baki tayi tana kallon ta. ' Shi sonta yake, ita kuma burge ta yake, me hakan ke nufi?.' Sanin babu mai bata amsa ne ya saka ta dubi Bhatool me kyau ta ce. " Ke ko dai son shi kike?."
Da sauri ta juyo tana girgiza kai.
Yaya Karima ta yi murmushi tana rike hannunta ta ce. " Bhatool kin san Senate baya surutu, kuma baya kula mata ko?."
" Yoo to ni Yaya taya zan sani."
" Ungo naki🖐 ai fada miki nake yanzun ba wai kin sani ba."
" To ina ji." Ta ajiye wayanta ta zuba mata ido.
Tsaki Yaya Karima tayi tana tashi ta ce. " Ki je falo yana neman ki."
Dariya tayi tana cewa. " Allah yasa outing zamu fita ya kashe min zuciya da kudi."
Kallon ta Yaya Karima tayi tana tsaki ta fita.
Mayafin Abayan jikinta ta yafa ta fito falon.
Yana zaune yayi shuru kamar maraya, kamar mutuniyar kwarai ta iso da sallama a bakinta.
Amsawa yayi ba tare da ya dago ya ganta ba, a kujeran dake kusa da nashi ta zauna bayan ta gaishe shi ya amsa.
Shuru ne ya biyo baya babu wanda yayi magana tsawon mintuna, kafin da kyar ya dago da kai ya kalle ta yana fadin.
ku yi following domin samun notification da zarar na yi posting, akai akai zan dinga posting just follow. Free book ne
Legend's pen ***