27
by @gureenjoh
Tsaye yake a cikin asibitin, kaman koyaushe irin shigarsa ta labarawa ce jikinsa Grey thobe da black and gold Jubba, Ghutra kawai ya ɗora a kanshi ya zauna mishi da kyau, fuskar nan kaman ko yaushe cike da kamala da tarin natsuwa, hannunsa ɗaya a aljihu ɗaya kuma na dafe da stand da wasu polisawa guda hudu ke tsaye daga gabansa suna mishi bayani.
Na farkon yake kallo yana sauraronsa a sadda yake cewa
"Toh Sheikh mun ƙira ku ne ba don komai ba sai don sanar da ku halin da ake ciki da wannan baiwar Allah dukda mun san taimakonta kuka yi, sannan daga lokacin da muka karɓeta ya kamata a ce hakkin kula da ita ya koma kan gomnati amma wani abin dole ne muna bukatar saka hannu da kuma tallafi Kasancewar mu ma ba access muke da shi da gomnatin kai tsaye ba. Wato halin da ake ciki bayan duka binciken da muka yi mun gano cewa wannan yarinyar an yi kokarin safararta ne wato trafficking victim ce so yanzu case din ya tashi daga hannunmu mu regular police ya koma wurin National Agency for the prohibition of trafficking in persons Wato (NAPTIP) ko da muka dawo nan ɗin mun tarar da ta farka sai dai ba cikin yanayi mai daaɗi ba. Bari Likitan ya sake yi mana gamsashen bayani duka"
Sheikh ya ɗan gyara tsayuwa yana saurarensu ba tare da ya ce komai ba, Likitan da ya ke buɗe file ɗinta ya ɗora da
"Toh Alal hakika binciken da muka yi dai mun sameta da abin da ake kira a likitance Dissociative amnesia a hausa za mu iya kiranta da 'mantuwar kwakwalwa sakamakon tsananin firgici ko raɗaɗin zuciya' ba za'a kira shi da gama garin cutar mantuwa ta (dementia) ba ko bugun jini domin shi illa ne da ke faruwa a lokacin da kwakwalwa ta kasa daukar nauyin wani mummunan abu da ya faru"
Ɗaya daga ciki police din ya kasa shiru sai da ya ce
"Ashshaa! likita daman hakan na iya faruwa?"
Yayi murmushi ya kalli ɗaya daga cikin police na NAPTIP ya ce
"Su da suke hulda da mata ko kananun yara da suke faɗawa victims na trafficking sun san fiye da hakan ma na faruwa idan mutum ya fuskanci abin da ya girgiza rayuwarsa kaman su fyade, azabtarwa ko yawan duka mai tsanani, ganin kashe-kashen rayuka ko ma hatsari mai munin gaske, wani lokaci kwakwalwa da kanta ta kan kulle wasu bayanai domin kare mutum daga faɗawa tsananin ciwon tunani"
Dukkansu suna cikin jimami babu mai kwatantata hakan a kanshi ko wani na jininshi itama kaddara ce ya jefa ta wannan kangi amma duk suna jin cewa za su yi iya yinsu sai dai kuma idan abin ne ya ci tura.
Likitan ne ya cigaba
"Mun fara fahimtar hakan ne bayan farkawarta daga irin ƙwayoyi da aka bata ta fice hayyacinta, bata iya tuna komai da ya shafeta ko sunanta, tana kallon mu duka cikin ruɗani kaman bata taɓa ganin halittu irin namu ba, sai kuma da muka matsa da tambayoyi sai ta tsorata har ta nemi firgice mana dole muka dakata don ta huta ta kuma samu natsuwa"
A lokacin ne Irshad ya magantu.
"Amma Dr. Shin cutar tana daɗewa kan a maganceta?"
Likitan ya ce
"Tambaya mai kyau, a gaskiya ba za mu iya dibar ma wannan cuta wa'adi ba, it depends wasu suna iya ma samun sauki cikin sati guda wasu satuttuka wasu har ma watanni sannan ba lallai ya dawo gabaɗaya ba sai dai da kaɗan kaɗan, ko kuma yawan ji ko sauraren abin da aka saba da jinsa a baya kan wannan cutar kaman muryoyin makusanta, wani waƙa ko karatu da aka saba da saurarensa wata murya ko fuska da za ta iya harba saƙo kwakwalwa cikin sakanni. Yanayinta na iya tafiya da PTSD (post-traumatic stress disorder) Don za ta iya fama da mafarkai, tsoro ko firgita da wuri da yawan son kare kai ko da ba abin cutarwa ba ne ya nufeta."
Babban cikinsu wanda ma'aikaci ne na NAPTIP ɗin yace
"Toh likita muna godiya da wannan bayanai amma akallah zuwa yaushe ku za ku iya rike mana ita anan?"
"Ba Za Ta fi kwana goma zuwa sha biyar ba, sauran sai a hankali so ko a gida za'a cigaba da kula da ita"
Irshad ne ya ce "Wani irin kula take so?"
Likitan yace
"wuri suke bukata mai kyau da aminci, kada a matsa mata ko a gaggautawa kwakwalwarta tunanin komai, sai an haɗa da hakuri da kwantar mata da hankali in Shaa Allah za ta warke"
Godiya suka mishi Likitan ya wuce, Irshad ya kalli babba cikin NAPTIP ɗin da ya shiga yi mishi wannan bayanin
"Za mu yi amfani da kwanakin zamanta a asibiti zamu ƙara kaimi wurin investigation, za mu gwada su fingerprint ɗinta ko tana da wani registered abu da shi, za mu duba duk wani missing person reports da aka samu a ƙasa na kusa ko ma na nesa sannan za mu ɗan taɓa media appeal da mun kama su ne tabbas za mu san yadda za mu matse su su faɗi inda suka ɗaukota amma a yanzu da muka rasa su dole waennan hanyoyi ne kawai za mu iya bi don identifying ɗinta musamman idan bata samu lafiya ba"
Irshad da yake jin tsananin tausayinta da na iyayenta a wannan lokaci yake ji musu raɗaɗin wannan al'amari ya ce
"Idan duk hakan bai yi working ba ba fata ba menene mataki na gaba?"
"A tsarinmu idan an samu irin wannan
mataki da mu ke ɗauka bayan sallama daga asibiti mu kan kaisu shelter dinmu na NAPTIP Inda aka ware musamman don irinsu amma ka san yanayin ƙasar a yanzu kula ba lallai ta same shi 100% a chan ba, akwai shelter na Women affairs ma wanda Minister of women affairs ke kula da shi muna iya kaiwa chan ajiya, ko kuma dai wasu trusted NGO da za mu iya biya su kular mana da ita"
Hakan Sam bai zaunawa Irshad ba amma bai ce komai ba, bills na asibiti yayi clearing har na kwana sha biyar da zata yi, bayan ya gama kuma yayi sayayya mai yawa ya kai har dakin shi da driver tana bacci suka same ta bai wani zauna ba ya fice bayan yayi magana da police din akan shi ba dan nan bane zuwa yayi program kuma zai koma a washegari don haka ko ya tafi zai cigaba da bibiyar al'amarin in Allah ya yarda, sun yaba mishi Sossai sun kuma yi mishi godiya don samun irinsu a yanzu yana wahala masu yi don Allah.
Daga nan wurin program ya isa aka yi closing da shi program ya watse lafiya ƙalau cike da nasarar ƙaruwa da suka samu ta hanyoyi daban daban, hotel ya wuce bayan yayi wanka yayi ordern tea saboda shi fa a duniya idan akwai abinda baya gajiya da shan shi to tea ne, ko wani iri ma in dai tea ne zai sha.
Yana cikin sipping a hankali idanunshi na kan TV da ake haska mataimakinshi na wa'azi a masallacinshi da Imam na ja mishi baƙi, wani farin ciki da natsuwa ne ke ziyartarshi dukkansu training dinshi ne abin da ke mishi daaɗi ba karatun ba ne sai irin ladar da zai samu da yardar Allah a kansu, sai irin nasarar da ya samu na ko ba ya duniya yana da tabbacin babu wani abu nashi naa addini da zai tsaya hatta wannan lada zai kasance mai gudana zuwa cikin makwancinshi.
Yana cikin wannan tunani ya ji Wayanshi na ringing ko da ya duba sai da ya gyara zama saboda wanda ya kira ɗin tamkar Abbiey yake a gareshi, Godfather ɗin shi kuma mentor ɗin shi Sheik Nasser Al-Rasheed, Aminin mahaifinshi ne don an yi zama na amana Kasancewar Sheik Nasser babban malami kuma balarabe da ya yi zaman Kano dalilin kasuwanci na shekaru da dama tun Irshad na ƙarami, he's a very respected person by both Nigeria and Saudi community saboda duka sun amfana da shi ta ɓangarori da dama har yanzu kuma suna kan amfana tunda da taimakonshi Irshad ya zama abin da ya zama a yau har ake alfahari da shi.
Sheikh Nasser Al-Rasheed fitaccen dan kasuwa ne a duka kasashen Nigeria da Saudi Arabia saboda yana fitar da su riɗi, ƙaro, zobo, ginger, gyaɗa da su spices dai daga Najeriya zuwa Saudi kuma yana shigowa Nijeriya da su Dabino iri daban daban, man zaitun, litattafai haka na addini, kayan gine gine da dai sauransu a gefe guda yana sana'ar real estate yana da manyan shopping plazas, warehouses, apartments da hotels a kewayen Nigeria da Saudi, wanda Irshad ya samu asalin dukiyarsa na ƙashin kansa a karkashin waennan sana'o'i na ubangidansa yana da tarin arziki da bai fito fili ba sai wa kalilan na makusantanshi.
Cikin natsuwa da ladabi ya ɗaga tuni ya sauya harshe zuwa larabci suka shiga zubawa tamkar a Saudi Arabia, labari mai daaɗi da Irshad ya samu a gabaɗaya kwanakin shi ne na Shigowar Sheikh Nasser wani satin kwarai yayi murna dole kuma a gobe ya koma Kano zama bai ganshi ba, sun fi awa uku suna magana kan suka yi sallama bayan sun gama tattauna harkar kasuwanci da kuma na hidiman addini da zai kawo shi Kanon.
Miƙewa Irshad yayi ya shige toilet yayi alwala ya zo ya yi karatun da ya saba na suratul mulk kan yayi adu'ar bacci ya kwanta don flight nashi da safe ne.
Ko da ya tashi tsakar dare bai koma ba har yayi sallar asuba da ya idar din ma bai tashi ba yana karatu sai bakwai yayi nafila raka'a biyu kan ya shige bayi yayi wanka ya zo ya shirya dama driver na jiranshi a ƙasa bai damu da ya karya ba ma ya bar hotel ɗin zuwa Airport, Allah ya taimaka bai samu wani delay ba jirginsu ya ɗaga zuwa Kano.
A Airport ya samu Ammar suka yi hugging juna cikin kewar da suka yi na juna kan suka nufi mota kan su isa har Ammar ya fara tsokanar Shehi wai ina ya baro Diva, takaici ya hana ma sheikh magana har ya shiga ya zauna.
"Ka yi wa Allah ka daina haɗani da 'yar daban chan, wanda aka yiyyi a baya ma ya isa"
Ammar yayi dariya
"Gaskiya mutane basu da adalci, ai ko da gami kurna ta fi magarya zaƙi hanyar jirgi kuma daban da ta mota me zai hadaka da wanchan yarinyar da shaye shaye ya zama jininta, zubar da jinin mutane ya zama ado a wurinta kuma rayuwar titi ya zama duniyarta?"
Irshad ya ɗan sauke Numfashi ya ce
"Ni karan kaina ina mamaki Ammar, ko kusa ko alama ba na jin wani ɗabi'a ko halayyarta yayi kamanceceniya da rayuwata bare har a alaƙantata da ni, bayan musulmi da nake ita ma kuma take amsa wannan sunan."
Ammar ya ce
"kawai so aka yi a ɓata maka suna da ita, har ma na yi zargin ko an biyata ne musamman don ta lalata maka mutuncin da miliyoyin al'umma suke kallonka da shi"
*"Ka san mene? Ka fita a sabgata tun ban nuna maka kalolin rashin darajata ba don yanzu ka gama faɗa ba ni da mutunci, kuma a rashin sanin mutuncin kamewar ban ga abin marmari da zan bibiya a rayuwarka ba, kudi kuma sun yi kadan su sa na ɓata lokacina a kanka idan ma zargi kake to tun maza ka daina! A baya ma na bibiyeka ne saboda in ɗau fansar abin da ka min kuma mun gyarota idan ba kana son na janye ma hakurar da nayi ba ne ka daina nuna min fuskarka a tawa don babu abin burgewa a rayuwarka wurin DIVA"*
Kalamanta da suka dawo mishi kai kenan kaman yanzu take jero su gareshi cikin gargadi da kaushin murya, ido ya ɗan runtse yana hango yadda Idanunta da suke lumshewa da maye suke ƙara girma da raguwa cikin nashi da sauri kuma ya buɗe idanun yana ambaton Allah tare da riƙe goshinsa.