BA SO BANE?

Chapter 18

by @hafsatwaziri1122

A hankali ya juya yana shafe gemun fuskarsa, zuciyarsa cike da tunanin inda zai je ya samu wayar da zai yi kira a yanzu da lokaci ya tafi sosai.

Gashi ba ya so ya yi amfani da na Adamu ko balle. Hakan ya sa ya tsaya a wajen, yana tunanin mafita. ya ɗauki wajen minti biyu tsaye a wajen.

Kafin ya yanke shawarar shiga cikin companyn.
A hankali ya shiga tafiyar tamkar wanda baya son taka kasa. A harabar companyn ya tarar da Baba Maigadi tsaye shi da wata mata. Yana isa wajen, matar na wucewa.

Ganin ta wuce ya sa ya tsaya suka gaisa da Baba Maigadi. Kamar zai wuce, sai kuma ya tsaya.

Baba Maigadi, cikin jin daɗi da ganin girman Abdul ɗin saboda sadaukarwar da ya yi musu, ya ce,

"Yallabai, lafiya kuwa? Na ga ka tsaya, ko wani kake so a kira maka a ciki?"

A hankali ya ɗaga kansa yana kallon Baba Maigadi tareda nazarinsa.

Ya kai kusan dakika goma yana kallonsa kafin ya dauke kai kamar ba zai yi magana ba, sai kuma cikin deep voice nasa mai fita a tausashe ya ce,

"No, Baba, wayarka za ka ara mini."

Da sauri, cikin rawar jiki, mai gadin ya zaro ƙaramar wayarsa kirar Tecno daga gaban aljihun rigarsa. 


Bayan wayar a ɗaure da roba, yayin da keyboard ɗin gabanta kusan rabinsu suke a zube.

"Ai kuwa ma ka yi sa'a, saboda ɗazu da safe yaran nan suka saka kati a cikin wayar. Sai dai ka bi da ita a hankali, don kana cikin maganarka za ta iya daukewa. Ka san wayar tamu, mu talakawa, sai a hankali, ba irin naku ba da tabawa kawai ake yi."

Ya ƙarasa maganar yana dariya cikin raha.

Murmushi kawai Abdul, da ke tsaye, ya yi masa tare da karɓar wayar yana masa godiya. Bai tsaya yin magana a gabansa ba, ya juya. Sai da ya ɗan ba da tazara sosai a tsakaninsu kafin ya tsaya yana daddawa. Can kuma sai ya ɗaga ya kara wayar a kunnensa.

Ta saitin tagar ofishin babu abin da bai gani ba, tun daga fitarsu, har tsayuwarsu, har zuwa tafiyar Mammy, da yadda ya tsaya ya bi motarta da kallo, har kawo yanzu da yake waya da wayar mai gadi. Duk da bai ji me yake tattaunawa a kai ba, amma yana ganin komai da idon fahimta.

Yana nan tsaye yana kallonsa ba tare da ya ɗauke idanunsa a kansa ko na daƙiƙa ɗaya ba, har sai da ya kammala wayar. Sannan ya ga lokacin da ya sauke nannauyar ajiyar zuciya, yadda mutum yake yi idan ya samu cikar burinsa, ko kuma ya yi wani abu da ya jima yana son ya aiwatar.


"Gashi, Baba. Na gode sosai."

Ya miƙa masa wayar tare da kuɗi.

"Ha'a, Yallaboi, wannan fa?"

Baba mai gadi ya faɗa tare da kokarin ya miƙa masa kuɗin da ya damƙa masa, a tunaninsa kuskure ne.

Ba tare da ya tsaya ba ya ce,

"Ka saka kati da shi."

Yana kaiwa nan ya shiga Napep ya wuce, ya bar Baba mai gadi baki a sake da kuɗi a hannunsa.

A hanzarce ya iso gaban Baba mai gadi ya dire kamar wanda aka jefosa ya na huci a dalilin gudun da ya yi.

Sosai jikin mai gadi ya ɗauki rawa tare da tunanin ko dai ya yi wani laifi ne. Ganin ogansu tsaye a gabansa kamar mayunwacin zaki za a sake shi daga tsare.

A tsorace ya shiga kokarin faɗin,

"In... ina yini, Yallaboi?"

"Ba ni wayarka yanzu nan."

Kafin Baba mai gadi ya samu damar miƙa masa wayar, ya wafce da ita da sauri.

A zafafe ya shiga dannawa wayar. Sai dai duk inda ya duba babu komai sai wasu lambobi da ba su fi uku ba. Cikin hanzari ya danna lambar ƙarshe da ya ga an kira.

Bugu biyu kuwa aka ɗaga. Kafin ya daidaita wayar a kunnensa, ya ji an ce,

"Alo, Baba Uzairu ne? Umma ta fita ba..."

Cikin tsananin jin haushi da takaici ya yi jifa da wayar a hargitse. Nan take kuwa wayar ta ƙara tarwatsewa.

Har ya juya zai tafi, sai kuma ya tsaya cak kamar wanda aka ƙwalawa kira.

"Menene na ga ya ba ka?"

Ya yi kamar yana tsattsare shi da idanu.

Da sauri Baba mai gadi, jikinsa na rawa, ya miƙa hannunsa yana buɗe shi. Fuskarsa babu annuri, tamkar wanda aka aikowa da mutuwar uwarsa. Haka yake kallon dubu ukun da ke dunƙule a hannunsa.

Cikin rashin yarda da abin da yake gani ya ce,

"Wannan shi ne abin da ya ba ka? Idan har ka kuskura ka yi min ƙarya, har da kai zan haɗa na hukunta."

Cikin rawar jiki ya shiga girgiza kai da sauri.

"Wallahi, Oga, wannan ne abin da ya ba ni yanzu nan. Ya ce na saka kati. Ga su nan ma."

Ya ƙarasa maganar tare da warware kuɗin.

"Me ka ji yana faɗa a wayar da ya yi?"

Ya ƙarasa maganar yana kallon cikin idon mai gadin, a ƙoƙarinsa na son tantance gaskiya saboda rashin yarda da zargin da zuciyarsa ta yi wa Abdul. Gani yake kamar yana shirya musu wani abu ne, domin shi bai yarda da cewa Abdul talaka ne ba, lura da abubuwa marasa adadi da ya yi a tattare da shi.

"Wallahi tallahi, Yallaboi, ban ji komai ba saboda ba a nan ya yi maganar ba."

---

Mammy

A jere motocin suka iso. Ba tare da ɓata lokaci ba, mai gadi ya buɗe musu gate suka shiga.

Suna parking, Japhat ya fito da sauri ya buɗe mata ƙofar bayan da take zaune a ciki. Ba tare da ta jira su Ajmal da ke ciki ba, ta fice da sauri zuwa ciki.

"Ummuuuu!"

Ta furta cikin ƙara, tana nufar babban falonsu da ke cike da kayan alatu na more rayuwa.

"Mammyn Daddy kenan. Ni dai ban san sai yaushe za ki girma ki daina wannan shagwaɓar ba. Ko zaman ƙasar waje ne ya mayar da ke haka?"

Kyakkyawar matar da ke tsaye, jikinta sanye da blue lace, ta faɗa yayin da fuskarta ke washe da murmushin jin daɗin ganin Mammy.

A hankali ta saki kyakkyawan murmushin da ke nuna yadda take jin tsananin son matar har ranta. Cikin annurin da ya gagara ɓacewa da sauri, ta je ta rungume matar tare da ɗora fuskarta a kan kafaɗarta.

A shagwaɓe ta ce,

"I missed you so much, Ummu. Yaushe rabon da ki je ki gan ni? Kusan one year fa."

Ta ƙarasa maganar tana lafewa a jikinta.

"To, my daughter, ba gani yanzu na zo ba."

"Hey, Mammyn Daddy."

Muryarsa mai cike da kamala da nutsuwa ta ratsa dukkan falon, yayin da kyakkyawar fuskarsa ke washe da murmushi.

A hankali ta ɗago kanta daga kafaɗar Ummu ta ɗaura idanunta a kansa.

Yana zaune a kan ɗaya daga cikin kujerun alfarma da ke cikin falon. Fari ne, kuma kyakkyawan da duk wacce ta kalle shi sau ɗaya, dole ko ba ta so sai ta sake kallonsa.

Sai dai ita, tana kallonsa, ta ɗauke kai da sauri kamar wacce ta ga ƙashi... ✍️✍️