Hs 14
by @legendspen
Page 14_
Da sauri ta d'aga kai ta kalle shi, jinjina mata kai yayi yana cigaba da cewa. " Za ki iya aure na?"
" Uhm.... Uhm.... Ni wai?." Ta nuna kanta tana kallon shi.
Gyada mata kai yayi yana mikewa tsaye ya zuba hannunsa a aljuhun wandonsa ya ce. " Kiyi shawara kafin ki yanke amsa, na baki daga yau har zuwa lokacin da kika ji kin amince." Ya ajiye mata kudi da bai san nawa ba ya tafi.
Da ido tabi bayansa har ya fita kafin ta kalli kudin, dariya kawai tayi dai-dai lokacin da Yaya Karima ta fito.
" Yaya wai fa tambaya na yake zan iya auren shi, can't believe it wai wannan handsome guy din ke cewa zan iya auren shi, to ai ko baya gani ne sai na aure shi balle kuma yana kallo." Ta karashe da wani murna a tattare da ita.
Dariya ita ma Yaya Karima tayi tana fadin. " To ke me kika ce masa?."
" Yaya me zance masa kuwa, barshi na dan wainasa a tunkunyar masa tukun, na ja masa aji sosai kafin nayi accepting."
Murmushi kawai Yaya Karima tayi ta ce. " Kar ajin dai ya tsinke."
Tashi tayi ta nufi dakinta bayan ta bawa Yaya Karima kudin ta ce ta ajiye mata.
*Senate*
Yana fitowa a falon ya sauke wani lafiyayyar ajiyar zuciya yana dafe saitin zuciyarsa, lumshe ido yayi yana jin wani karfin guiwa.
Dafa sa da akayi ne ya saka shi bude ido ba shiri yana sauke su akan Juraij, dariya Juraij ya fara masa yana cewa. " Wani irin tsoro ne haka Senate."
Hararan shi yayi yana nufan hanyar fita, shi ma ya mara masa baya yana tsokanan sa amma ya mantar dashi har suka shiga gidan su.
A falo suka tarar da Momi, Anas da Salman sun zuba tagumi suna jiran me zai je ya dawo.
Momi na ganinsa ta mike ta iso gurin shi tana zuba masa ido alamun tanaso taji karin bayani.
Dariyan da Juraij ke yi ne ya saka Anas cewa. " Ya kwafsa ko?."
" No bai kwafsa ba." Ya fada yana dariya kafin ya ce. " At last ya fada mata yana sonta."
Lokaci daya suka saki murmushi, Momi bata san sanda ta rungume shi ba tana cewa. " Babana ya zama jarumi."
Murmushi kawai yayi yana fadin. " Momi dama jarumin ne tun a baya, kuma In Sha Allah ta sanadiyarta na canza, na zama jarumi."
Sakin shi Momi tayi tana jan kumatunsa ta ce. " Better."
Salman yayi murmushi ya ce. " Shikenan ai yanzu sai kar ka kashe kanka ko."
Rarumo filon kujera yayi yana wurga masa, da sauri ya matsa yana dariya da fadin. " Senate na Bhatool."
Dariyan da ya dade bai yi ba yayi yana shafa sumarsa ya ce. " Fadi da k'ara Senate na Bhatool kuma Bhatool na Senate."
Dariya falon suka saka kafin aka zauna ana hira ana zolayan shi, har su Salman da Juraij suka tafi
*Washe gari*
Rawar kai, ya mantar da Bhatool tashin hankalin dake makaranta. Hakan yasa ta shirya tun wajen ƙarfe bakwai, so take taje ta kaiwa ƙawayenta gist ɗinan.
Ƙarfe 7:45 a bakin gate ɗin YSU tayiwa Bhatool, tana tafe tana danna wayarta. So take takira wata cikin ƙawayenta taji ko sun ƙaraso cikin school. Horn din taji anayi mata a baya, hakan yasata waigawa a fusace, wa zata gani?.
Dr Hashim. "Ya Allahu." ta furta kaman tayi kuka, a hankali ya kawo motar kusa da ita. "Bhatool. Ya maganar mu." Murmushin dole ta jawo tayi sanan tace. "Nayi shawara, zanzo office ɗinka anjima."
"Okay." kawai yace yaja motarsa, da harara tabi motar tasa. Wayarta ce tayi ƙara alamun kira.
"Wai Suhaima ina kikasa wayarki ne."
"Ina kan mashin. sai yanzu na sauka, Kinzo school din ne?."
"Da banzo ba, zan kiraku?."
"Okay gani nn shigowa."
Kashe wayar tayi ta nufi wajen da suke zama kafin su shiga hall. A wajen ta tarar da su Janah suna zaune, dan su tsarin su sai sun hadu baki daya zasu shiga class tare, yanzu ma takirasu sabida tayi tunanin ko sun shiga. Sabuda bata ce dasu zata zo ba.
Ƙarasawa tayi ta zauna, tare da fadin. "Amarya wace zatayi miki make-up?."
Da kallo suka bita, su sunanan cikin tashin hankali da fargaba, ita tana nan tana musu zancen make-up.
"Kikace bazakiyi make-up?."
Wata uwar dariya Bhatool tayi, sanan tace. "Ai yanzu banza ta faɗi, arziƙi yazo, gayu sai yaci uban na daa."
Legends pen ***
karku gaji da ni, ku yi following. labarin nan akwai suger nan gaba. Ku yi following kunji.