JODAH

27

by @sadisakhna


______👑 *JODA* 👑_____

             

Na 

*Sadi-sakhna*

Ƴar mutan Jama'are



THE TRIO OF TALES 
(3⃣ minds, 3⃣stories,1⃣Journey) 


@sadisakhna on Arewapen
@SAKHNA03 On Wattpad
*** on Whatsapp


LITTAFI NA 1


👑*Warƙa ta (27)*👑


Haɗe haɗen magani nashiga yimata ina bata,na kashe zafine,na tsaida jinine da kuma na ƙarin kuzari,lokaci guda ta samu wani wahalallen bacci ya ɗauketa. Bayi suka shiga gyara wajen da kuma hidimar ɗora mata abinci masu gina jiki na masu jego. 

A zaune nake bayan nayi sallah magriba,ina jin yadda Mutane keta kai kawo suna magana,wanda wasu hira sukeyi akan salon dana nuna na karbar haihuwar Gimbiya Asmah. Wata mata ce tashigo kawomin abinci,tana ajiyewa ko kallon inda nake batayi ba ta fita,nasan rashin gaisuwar bai wuce na an sakata kawowa baiwa abinci ba. Kai mutane mune matsalar kanmu. 

Banso nakai dare ba amma abin yazomin a haka,ji nakeyi kamar nayi tsuntsuwa na koma gida domin haɗuwa da Hammar,nasan a duk inda yake to lallai ya nemeni har ya gaji zuwa wannan lokacin.

Wani baccin wahala ne ya ɗaukeni lokacin danayi sallahr isha kuma naci abinci,alamar bubbuga cinyata danaji shine yasakani farkawa ina kallon waye. Wata baiwa ce amma ba wacce takawomin abinci jiya da daddare ba. 

"Kitashi kizo yanzunnan ungozama tana nemanki"

Kallon tagar ɗakin nayi na hango sararin samaniya akwai sauran duhu a tattare dashi. 

Tashi nayi banyi musu ba kana ban tambayeta dalilin ƙiran ba,koda naji dalilin ai banida zabi daya wuce nabi bayanta,a zatona jikin Asmah ne ya rikice amma sainaga ba ɗakin datake muka biba,wani wajenne daban. 

Muna shiga na hange ta riƙeda tsumma a hannunta,alamar tana ɗauke da jariri,ƙwan aci bal bal na fitilar dake ɗakin yabada haske wadatacce. 

Muna shiga ta miƙomin tsumman hannunnata,Jaririya ce a ciki idonta a rufe tamkar mai bacci.

"Kiyi haƙuri nasaka an tasoki duk da kuwa cewar kinyi aiki kin gaji,Jaririyar da gimbiya Asmah ta haiface,tun da tazo duniya batayi kuka ba, nayi tunanin hakan babu matsala tunda da ranta,to amma kuma jikinta jijjiga yakeyi tana fizga kamar mai borin haihuwa sannan gabobinta sai su riƙe daga baya saisu sake kamar basu ba,shine nace a ƙirki kigani"

Ƙare mata kallo nayi,banga tayi fizgar ba amma tana riƙe hannunta sai naji yariƙe sosai kamar na gawa,ɗan buɗe idonta tayi ta gefen hasken fitilar ina hango yanda ƙwayar idonta sukayi tamkar sun juye. Rass naji gabana yayi,Allah yasa ba wahalar da mahaifiyarta tasha bane a goyon cikinta itama ya tabata......

"Ni nace to ko mayune ko masu gubar baki suka mata,in hakane akwai kakana yana maganin daya shafi mayu bari zan saka a ƙirashi. Tsorona kar Ahalin gidan suga mai yake faruwa da jinjirar,nasan mu kanmu bazamu taba tsira ba,tun ɗazu nake nan da ita na gagara miƙata garesu,a cewar ina dubata ne. Nayi dan dabaruna amma na kalli abin yafi ƙarfina shiyasa na ƙiraki"

Jimm nayi ina jinta,meyasa komai yafaru sai a laƙabawa maye ne,wannan abinda yake faruwa da ita tabbas yanada alaƙa da yanayin goyon cikinta da kuma wahalar datasha lokacin haihuwa. Zanso na taimaka mata amma a yanzu banida ilimin yin hakan. Tausayinta ne naji ya tsargu a cikin raina lokaci guda.

"Bana tunanin mayu ne suka kamata,koma mai yasameta da sannu zamuyi bincike mi gano,amma kafinnan dolene mahaifiyarta da danginta su ganta domin su san halinda take ciki,abu ne ai bana boye ba"

Ina gama faɗin hakan nayi hanyar fita zuwa inda gimbiya Asmah take kwance. Lokacin masallacin cikin masarautar sun fara ƙiran sallahr assalatu.

A zaune na sameta da ƙoƙon kunu a hannunta,mahaifiyarta tana gefe tanayi mata sannu. Zuwa nayi gabansu na miƙawa mahaifiyar tata ƴar. Karbarta tayi da murmushi akan fuskarta,amma yayinda ta kai hannu ta riƙe hannun jinjirar nasan sandarewa da kuma karkarwa da takeyi itama taji.Sai dukkan wani abu na fuskarta ya sauya zuwa wani abu daban mai wuyar fassaruwa.

Jikina ne yayi sanyi ganin kallon da takeyiwa yarinyar,wacce ko kwana ɗaya bata gama cikawa ba a duniyar.

"Ke mai yasami yarinyar haka jikinta tamkar na gawar da tayi kwanan keso ko mayune suka kamata kai?"

Itama Gimbiya Asmah ajiyewa ƙoƙon hannunta tayi tana kallon ƴar kuma tana kallona,burinta shine taji wacce amsa zan bayar domin na fiddata daga tantamar da take ciki.

Jimm nayi kafin na farayimusu bayanin abinda nake hasashen yake faruwa kokuma yafaru.

"Ehh to a zahirin gaskiya kamar inaga goyon cikin dayaxo a wahale,kana kuma da shima kansa doguwar naƙudar da tayi shine ya taba lafiyarta har ya kaita gayin haka. Sannan kuma a duba ta danayi da alamar jijiyoyin kanta basa aiki yanda yakamta,akwai yiwuwar ta samu wani naƙasu nayin abubuwa a gaba. Amma dai ku bani wani lokaci idan na koma makaranta xanyi binciken dazan iya akai,idan ma akwai magani ko wani taimako duk zan yi ƙoƙarin wajen ganin na taimaka"

"Naƙasu,da hauka fah kike nufi,kuma a cikin gidan sarauta,inaaa bazai yiwu tana ƴar sarki kuma mai jiran gado ta fito a haka ba,ki nemo magani kokuma asan yadda za'a yi,ni babu nakasashshe a danginamu saidai anan ta kwasa"

"Mai nakejine haka hayaniya mai ya farune Joda?"

"Sunkia madina ta faɗa da shigowarta kenan ɗakin,ganin ta a sarauniya Abida tayi yasa ta miƙimin yarinyar tareda tashi tana karkade zaninta"

Damƙe yarinyar nayi a hannuna ina jin yadda take maidawa Sunkia madina abinda nace mata harda ƙari.

Haɗa ido mukayi da gimbiya Asmah wacce itama wani kallo ta watsawa Jinjirar mai wuyar fassara kafin ni ta bini da harara.

"Ranku ya daɗe idan babu damuwa inaso nayi magana"

Baiwar data kawo abincin bata fitaba ana wannan chakwakiyar tayi magana.

Dukka kallonta mukayi domin muji mai zatace.

"Ranki ya daɗe matar da take kulada Sultan ta taba bamu labarin cewar ƴar ta itama haka ta haɗu da wauta da ta haifeta a lokacin yaƙi. Amma kuma ta bamu labarin cewar ƴar ta tawarke kamar batayi ba,ni inaga a ƙirata tayi bayanin maganin dasuka jarraba ko idan anyi irinsa za'a dace."

"Ohh wai Aminatou kike faɗa,ni ai harna manta da ita,danace taje abinda ta kulada Sultan,ɗaxunnan kuwa tashigo dashi a hannunta har tana tambayar ya jikin Babarsa,maza jekiyi ƙiranta"

Tashi baiwar tayi da sauri ta nufi waje domin ƙiran Aminatou,nikuma haka kawai naji ƙirjina yana bugawa bansan daliliba.

Muna nan a yanda muke,su suna tsaye kamar gumakai sai sauƙe ajiyar zuciya suke,ita kuma Asmah tana sheshsheƙar kuka akan gado,yayinda ni kuma ina zaune gavan gadonta da Jaririya ƙyam a hannuna.

Da sallama tashigo ɗakin,zuwa lokaci gari yafara haske amma an rasa mai tashi yayi sallah,wani dokawa gaban yayi,nikuwa ina zan manta da wannan matar ai har duniya ta naɗe,itama idonta akaina ya sauƙa tana zareshi kamar taga mutuwarta.

Sakin sultan tayi ya sauƙa ta ƙafarsa,kamar surar mikiya haka tayi saurin zuwa inda nake tsugunne itama tayi zaman dirshan.

Rawa bakinta yakeyi,amma sauran jikinta sun tsaya kyam tamkar an bata umarni.

Nice Allah yabani iko na buɗi baki da ƙyar nace.

"Ummahhhhh!!"

Kaman jira take tayimin wata runguma gabaɗayanmu nida Jaririyar.

Kuka muka sake a tare kaman sannnan akayi mana mutuwa mai zafi,saida mukayi ya ishemu kafin tasakeni tana sharemin hawayena.

"Jjjjjodah Joda kece,kece daga ina Allah ya jefomin ke yau ɗaya ya karbi addu'a ta?"

"Ummahh,ba faɗowa nayi ba nice mai maganin da aka kawo na karbi haihuwar Gimbiya Asmah"

"Kina nufin kice kece dama mai maganin da bakin kowa ya kaure da amsa sunanki?"

Tayi maganar cikeda mamaki da al'ajabi,ganin hakan yasa na ɗaga mata kai ina murmushi mai ɗauke da kuka,amma ba kukan baƙin ciki ba saina farinciki dana hango tsantsar alfahari dani a idon ummantawa.

"Nice Ummah,Baba yakub 
Ba mugunta yayimin ba Jami'ar Al'azhar yakaini wajen Babban malaminsu a hannunsa na tashi nayi ilimi mai yawa,ko nace ina kanyi ma"

Wannan karon murmushi tayi dataji abinda nace,hannu tasa tana sharemin hawayena,farinciki yaƙi barin kan fuskarta,kallon a haka ji nayi tamkar na daskarar da lokacin ya tsaya a haka har abada.

"Aminatou ina fatan kinji dalilin ƙiranki da akayi,amma kuma sai mukaga keda Joda kuna wani abu da bamu gane kansa ba."

Juyawa ummah ta tayi,lokaci guda ta dawo daga duniyar ganina zuwa duniyar Bauta,domin kama kanta tayi tareda sunkuyar dakai kamar kowanne Daƙiƙa za'a iya fille mata kai,wani abu da bansan menene ba naji ya caki cikin zuciyata.

"Ehh ranki ya daɗe Joda itace ƴata danake bada labarin an rabani da ita,kuma itace wacce tayi lalurin tabin ƙwaƙwalwa tana yarinya. Sannan tana jinjira bata kuka,kuma jikinta sai ya dunga fizga. Tadayi wayo kuma sai batayin abu na daidai shekarunta saina ƙasa da ita sosai"

Dukkansu Da mamaki suke kallona jin bayanin da ummah ta takeyi.

"To idan itace Joda ya akayi kenan ta warke,tunda kowa ya kalli Joda yasan idan akwai rashin lafiyar ƙwaƙwalwa a gareta to saidai ace kaifinta ne ma yayi yawa ba dusashewarta ba."

"To hakane kam,amma sauyawar rayuwarta dama tamu gabaki ɗaya ta farune watarana data shiga cikin daji,munata neman ta bamu ganta ba,daga ƙarshe muka sameta a kwance ta suma. Mahaifinta ne ya sameta,yace baiga wani abu a kusada ita ba dayake nuna yayi mata illah. Bayan ya kawota gida kwananta goma tana cikin doguwar suma kafin ta farka. Tana farkawa kawai muka ga ta warke,bayan warkewar ma saita tashi da wata irin baiwa na ɗauke dukkan abinda aka faɗamata. Wannan shine kawai abinda nasani"

"To ke Joda baki tuna komai ba na abinda yasameki a jejin ba?"

Sunkia madina ta tambaya.

Jijjiga kai nayi kamar wata wawuya kafin nace.

"Ban tuna komai ba bayan tashi danayi na ganmu a cikin teku zamu nufo ƙasar Goa,wannan kawai na tuna sai buɗewar danaji ƙwaƙwalwata da tunani na sunyi"

Nazartar fuskarsu nakeyi lokacin da ummah take bada labarin da kuma wanda na bayar,kaman sun fara maida abin al'amara wanda suma zai faru kan ƴar su nan gaba. Ban gama nazari na ba kuwa naji muryar sarauniya abida tace.

"A shekara nawa tashiga Cikin dajin"

"A shekara sha biyu lokacin"

"To muma yanxu zamu jira Saita cika shekara sha biyun kenan kafin Al'ajabi ya kasance a garemu "

Da mamaki nake kallonsu,wai waɗannan mutanen kansu ɗaya kuwa,to amma hakan wata dabarace idan suka ɗauketa a hakan,domin shine kaɗai hanyar da yarinyar nan zata tsira daga Fi'ilancinsu.

A haka akayi ta yayata cewar yarinya ƴar baiwa zata zama nan gaba,ni dai ban sake tofawa ba,amma a raina na guɗuri niyyar yin bincike akan abinda yasameta,sannan kuma zanyi ƙoƙarin tuna ni mainene yasameni harna warke.

Muna nan zaune bayan anci karin kumallo Jakadiya tashigo yiwa Yerima Kabeer Iso zaiga jikin matarsa da kuma ƴar da aka haifa masa,nashiga duba jikinta kenan wannan tsautsayin ya tareni,ji nayi kamar na buɗe ƙasa na shige ta binne dani. Amma babu damar hakan domin sauran manyan matan harma da wasu suna wajen.

Kafin na ankara ko nayi wata dabara har ya shigo turakar, wani damm damm gabana yake bada luguden duka Da muka haɗa ido dashi,yayi mamakin ganina a wajen amma kuma sai yayi saurin wayancewa irinnasa na ɗan duniya. Nidai na koma gefe ina sunkuyar dakai. Ganin ya matsa suna magana da gimbiya Asmah wacce take ta cicci masa magani yasa nasamu damar ficewa daga ɗakin da sauri.

Kai tsaye bangaren da ummah tacemin suna zama na nufa,a raina ina dana sanin zuwa duba jikinnata,saboda haɗuwa ta da wannan mutumin ko kaɗan ba alkhairi bane.

A zaune na kalleta tana bawa Sultan kunu da wani ƙaramin ludayi, a hankali take ɗiba daga cikin ƙoƙon tana bashi cikin kulawa. Wani hawayene naji ya taru a cikin idanuwana,tausayinta da kuma shauƙin kasancewa da ita suka gauraye Zuciyata,nasan itama nice a ranta domin daga kallo tana bashi kunun ne amma kuma hankalinta ko kaɗan baya kansa. Inama zasu barni na tafi da ita,da babu wanda yafini farinciki a wannan duniyar kuwa.

"Waye kike nema kika tsaya daga nan,bazaki shiga ba?"

Juyawa nayi na kalleta,wata budurwace wacce zamuyi shekaru ɗaya da ita. Da fara'a a fuskarta tayimin maganar,lokaci guda naji ta kwantamin a raina. Ganin ina ta kallonta ban bata amsa ba yasa ta cigaba da cewa.

"Hala ko ke baƙuwa ce kai,kada ki damu mu ba masu cutarwa bane, Sunana Nuratu, canne Bangarenmu inda kike kallo,akwai Kaka ta Inna mairo,wacce kike kallo kuma Sunanta Inna Aminatou ina ce mata Babar Joda.........."

Labari kaɗan tabani na yanda suke rayuwa,da kuma yabo da takeyi na halayen mahaifiyata,lokaci guda naji wani shauƙin yasake kamani,banga amfanin ƙarisawa wajen ta ba a yanzu,bai kamata tunda nasan tafiya zanyi ba nashiga jikinta sosai,hakan ba komai zai ƙara mata ba sai Begena na kuma ɗumbin tunani.

"Nuratu nikuma sunana Joda,nagode da kulawar da kuke bawa mahaifiyata,dan Allah nabaki amanarta ki cigaba da kulamin da ita har zuwa lokacin dazan dawo kinji"

Zaro ido tayi tace ....."Jodaaan Inna Aminatou" da karfi.

Ganin zata jawomin jama'a nayi saurin rufe mata baki. Hira muka ɗan taba kafin na kamo hanya na dawo,bansanta ba sai yau amma sai jita a jikina kamar ƴar uwata,rayuwata da tata naji sun bani tausayi.


Bakina naji an rufemin an fizgeni cikin zafin nama,zaro ido nayi inaso naji waye amma na kasa har saida muka shiga wani lungu. Matseni yayi da bangon kafin ya sakemin bakina,jikina yana rawa nake kallonsa,baki na buɗe zan kurma ihu naji ya ce.

"Kada ki kuskura kiyimin ihu,domin hakan zaisa ki fuskanci hukuncin da bakyaso daga gareni,kuma bazai taba ƙwatarki ba domin nan sansanina kikazo,nikeda iko anan kuma na faɗa a ji.

Joda ina sonki,wai miyasa bazaki bari na sameki ta sauƙaƙƙiyar hanya bane,na faɗamiki bazan cutar dake ba,hasalima zan baki ƴan ci da kuma duk wani abu na jin daɗin duniya,amma na rasa miyasa idan kin gani saikiyi tamkar kinga mutuwarki,wancan ɗan iskan dame yafini ko mai zai nunamin dashi bakya tsoron sa saini,na tabbata wannan abin danake nema a wajenki kin bashi babu adadi"

Hannu ya ɗaga zai tabani nayi saurin zamewa ina komawa gefe,haki nakeyi tamkar naga mutuwata,shima kamar mayunwacin zaki ya nufoni,ina ganin haka na kwasa da gudu nayi Turakar Sunkia madina,domin nasan a halinda nake ciki yanzu ita kaɗaice zata iya cetona Bayan ubangijina.

Kaman an harboni suka ganni akansu ina rarraba ido,da mamaki suke kallona,kafin suce wani abu nayi saurin zubewa tareda cewa.

"Ranki ya daɗe dan Allah kiyimin rai ki gafarceni,inaso na koma Makaranta da hanzari akwai wani abu mai muhimmanci dazan gabatar"

Murmushi tayi kafin tace

"Haba Joda to dan zaki koma shine saikinyi wannan roƙon,da ni a bangarena cuku cukun takarda nakeson aikawa na a bar mana ke anan,Fasihmman da ga mahaifiyarki a tare damu,amma tunda kinada babban uzuri dayasa zaki koma bari na shirya wanda ya ɗaukoki ya maidaki,amma ki sani ko yaushe kikazo ƙofarmu abuɗe take. Muna matuƙar godiya da taimakon mu da kikayi. Bari zan haɗaki da kyautar da mukayi miki a maidaki yanzunnan."

Wata ajiyar zuciya nayi danaji mai tace,har ga Allah inaso na zauna ko domin mahaifiya ta da take wajensu,duk da ma naga tana cikin ƙoshin lafiya,to amma wannan dodon bazai taba barina nayi a rayuwa a wajennan ba sam.

Cikin sauri na haɗa kayana danaxo dasu,ko mahaifiyata banyiwa sallama ba na hau keken dokin dazai maidani muka kama hanyar Jami'ar Al'azhar,hawaye yana fitomin ina sharewa na rashin samun cikakken lokaci muyi magana da ita. Amma ban fidda rai ba tunda naga inda take ko watarana zan iya satar hanya naxo na ganta batareda kowa yasani ba,kokuma na nemi alfarmar Sunkia madina ta kawomin ita na ganta. Da kayana na alfarma amma irinna bayi masu matsayi. Sannan da kayan ado masu kyau suma.



Sadi-sakhna ce ✍🏼

Comment 
Like 
Share 
Follow