KADDARAR SOYAYYA

30 to 31

by @sheolly

KKADDARAR SOYAYYA 
 by sheolly. 
      🔥🔥
  babban dining hall na gidan Alhaji Bashir ya cika da haske da annashuwa.
An shirya tebur da nau'o'in abinci iri-iri. Kamshin girki ya bazu ko'ina cikin gidan.
Maryam da Amina suka zauna kusa da Mom dinsu, yayin da Alhaji Bashir ke zaune a kujerarsa ta musamman.
Mom ta kalli kujerar da ke gefen Alhaji Bashir.
"Muhammad bai fito ba?"
Alhaji Bashir ya kalli agogon hannunsa.
"Ki kira shi."
Daya daga cikin masu aikin gidan ta haura sama domin kiran Muhammad.
Bayan 'yan mintuna...
Sai aka ji takun sawu daga saman bene.
Muhammad ya sauko a hankali.
Sanye yake cikin bakar slim-fit jeans, farar T-shirt mai saukin zane da bakar jacket mai tsada. A kafafunsa akwai fararen sneakers masu tsabta, yayin da agogon hannunsa da sarkar azurfarsa suka kara masa kwarjini.
Gashinsa a gyare yake cikin salo mai kayatarwa, fuskarsa kuwa tana sheki tamkar an shafa mata haske.
"He looked effortlessly handsome."
Da duk wanda ya gan shi, zai san cewa Allah Ya hore masa kyau.
Amma ko kallon dining table bai yi ba.
Ya daga hannu kawai.
"Good evening, everyone."
Ya juya zai nufi kofar fita.
Nan take Alhaji Bashir ya kira shi.
"Muhammad."
Ya tsaya ba tare da ya juyo ba.
"Na'am, Dad."
"Ina za ka?"
"Zan fita ne."
Alhaji Bashir ya dan hade fuska.
"Ka ga iyalinka suna cin abinci tare, amma kai kana son fita?"
Muhammad ya juyo cikin natsuwa.
"Dad... ba na jin yunwa."
"Ko ba ka jin yunwa, ka zo ka zauna tare da mu."
Muhammad ya dan yi shiru.
Daga bisani ya karaso ya zauna a kujerarsa.
An kawo masa plate, amma bai taba abincin ba.
Ya jingina da kujerarsa kawai.
Maryam ta kalle shi.
"Little brother, at least eat something."
Muhammad ya girgiza kai.
"Maybe later."
Mom ta lura da hakan, sai ta kalli daya daga cikin masu aikin gidan.
"Ku kawo masa shayi mai zafi."
Ta san cewa Muhammad ya fi son shayi fiye da cin abinci.
Alhaji Bashir ya girgiza kai.
"Aisha, wannan ba daidai ba ne."
Ta kalle shi.
"Me kuma?"
"Kina yawan biye masa. Duk abin da yake so shi ake yi."
Mom ta dan yi murmushi.
"Alhaji, ai uwa daban take."
Sai ta kara da cewa,
"No mother hates her child."
"Na haife shi ne. Idan ban tausaya masa ba, wa zai tausaya masa?"
Alhaji Bashir ya sauke numfashi.
Ya san idan ya ci gaba da wannan magana, za ta iya rikidewa ta zama gardama.
Saboda haka ya yi shiru.
Ba ya son yara su ga suna gardama.
A gefen tebur, Maryam da Amina suka kalli juna cikin natsuwa.
Sun san mahaifinsu yana son Muhammad ne, amma yana son ya ga ya zama mutum mai cikakkiyar tarbiyya.
Bayan an ci gaba da cin abinci na wasu mintuna, Alhaji Bashir ya kalli matarsa.
"Aisha."
"Na'am."
"Gobe da yamma za mu yi baki."
Ta dago kanta.
"Su waye?"
"Abokina, Alhaji Umar Farouk."
"Zai zo tare da iyalansa."
Mom ta gyada kai cikin nutsuwa.
"To, Allah Ya kawo su lafiya."
Sai ta juya ta ce wa masu aikin gidan,
"Ku tabbatar an shirya komai yadda ya kamata."
Alhaji Bashir ya yi murmushi.
Ya san duk lokacin da aka ce akwai baki, Hajiya Aisha ba ta wasa da shirye-shirye.
A gefe guda kuwa, Muhammad ya daga kofin shayinsa ya kurba a hankali.
Bai san cewa bakon da zai zo gobe ba...
Shi ne farkon canjin da zai sauya rayuwarsa gaba daya.


    

A gefe guda kuma, cikin Birnin Zariya, gidan Alhaji Umar Farouk ya fara yin shiru bayan kowa ya kama gabansa.
Bayan an gama zaman dare, Abdurrahman da matarsa Zainab (Aunty Zee) suka yi sallama suka koma gidansu.
Haka ita ma Aunty Hauwa, bayan mijinta ya zo ya dauke ta tare da 'ya'yansu biyu, Inaya da Arif, suka bar gidan.
Yanzu a gidan sun rage Alhaji Umar Farouk, Ammi, Khadija, Miemi da kuma autan gidan, Sadiq.
Lokaci ya yi sosai, kowa yana shirin kwanciya.
Khadija ta mike daga kujerarta tana gyara mayafinta.
Da ta hango Sadiq yana ta wasa da remote na television, sai ta tsaya ta kalle shi.
"Kai Sadiq..."
Ya dago kai.
"Na'am, Sister."
"Ka ji fa, kar ka kuskura ka sake shigowa dakinmu da daddare kana damun mutane. Idan ka sake, sai na hukunta ka."
Sadiq ya sosa kansa yana murmushi.
"To Sister."
Miemi ta dan bude baki cikin sanyin murya mai dadi.
"Anty Khadija, don Allah ki barsa mana. Ai ba zai sake ba."
Khadija ta kalle ta.
"Ke dai kullum kina kare shi."
Sai ta nuna Sadiq da yatsa.
"Ni dai na fada maka. Idan ka sake, ka ga abin da zai faru."
Ta juya ta fara tafiya zuwa dakinsu.
A daidai wannan lokacin, Alhaji Umar Farouk ya daga murya.
"Khadija!"
Ta tsaya.
"Na'am, Abba."
"Gobe ki shirya da wuri. Muna da fita."
"To Abba."
Da Khadija ta ci gaba da tafiya, Sadiq ya matsa kusa da mahaifinsa yana murmushi.
"Abbana..."
"Lafiya?"
"Ina za mu je gobe? Shopping ne... ko kuma wajen shakatawa?"
Nan take Ammi ta kalle shi.
"Kai wannan yaron! Ba ka da wani aiki sai tambayoyin banza."
Sadiq ya yi dariya.
Ammi ta ci gaba da cewa,
"Ba shopping za mu je ba."
Sai ta kalli Alhaji Umar Farouk.
"Gidan Daddy Bashir za mu je."
Sadiq ya bude ido.
"Da gaske?"
Miemi ma ta dago kai.
"Abba... har ni ma zan je?"
Alhaji Umar Farouk ya yi murmushi.
"Eh, za ki je."
Sai kuma ya tuna da wani abu.
"Amma fa lesson teacher dinki yana zuwa daga karfe biyar zuwa shida na yamma."
Ya kalle ta cikin kulawa.
"Ina so ki mayar da hankali sosai a karatun JAMB. Burina ki samu admission a babbar jami'a."
Miemi ta dan turo baki irin na shagwaba.
"To Abba..."
Ammi ta dan yi dariya.
"Ba ki da zabi. Za ki bi mu."
"Mun riga mun sanar da malaminki."
Miemi ta saki murmushi.
"Shikenan."
Alhaji Umar Farouk ya tafa hannayensa a hankali.
"Yanzu kowa ya tashi ya je ya huta. Gobe rana ce mai muhimmanci."
Kowa ya amsa,
"To."
Miemi da Khadija suka nufi dakinsu.
Dakin nasu yana daya daga cikin dakunan da suka fi kyau a gidan.
An kawata shi cikin launin fari da ruwan hoda. A ciki akwai gadaje biyu na zamani, babban wardrobe, madubi mai tsayi, teburin karatu da shelf cike da littattafai. Wani kamshi mai dadi ya mamaye dakin, yayin da fitilun dakin ke ba shi annuri mai kwantar da hankali.
Da suka shiga, Miemi ba ta tsaya yin magana ba.
Kai tsaye ta dauki kayan baccinta ta nufi toilet domin yin wanka.
Khadija ta girgiza kai tana murmushi.
"Ke kuwa..."
Sai ta daga murya.
"Ko sallama ba za ki yi ba?"
Daga cikin toilet ne Miemi ta amsa cikin shagwaba.
"Na yi fa, Anty Khadija."
Khadija ta yi dariya.
"Wannan yarinyar..."
Miemi kuwa tana daya daga cikin kyawawan 'yan mata da Allah Ya halitta.
Fuskarta cike take da haske, idanuwanta masu kyau suna kara mata armashi, yayin da kamanninta ke jan hankalin duk wanda ya ganta.
Saboda wannan ne Ammi take tsananin kula da ita.
Ba ta son samari su samu damar kusantarta, domin ta san Miemi yarinya ce mai tausayi, hakuri da kuma rashin wayon duniya.
Sabanin Khadija, wacce take da karfin hali da saurin fadin gaskiya ko da ba kowa zai ji dadi ba.
Duk da bambancin halayensu, soyayya mai karfi ce ta hade su a matsayin 'yan uwa.