page 5
*SILAR HALLACI.*
*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*
*HIJABS CORNER BY JANAFTY*
*Muna da Hijabai masu kyau da inganci, ɗinki cikin kwarewa da* *mabambanta design, muna aikawa da kayanmu ko'ina a Nigeria, muna maraba da masu siyan ɗaya ko sari.*
****, tuntuɓa ta wannan lambar*
*KADUNA/ZARIA*
*🅿️5*
Mafarin komai...
1981
"Sama"ila Zakariyyah Jega Shine Cikakken Sunan mahaifin Ahmed Wanda ya kasance Haifaffan garin Jega ne dake karkashin Garin Birnin kebbi,su biyu ne awajen iyayensu Mallam Zakariyyah da Kuma matarsa da sukayi Auren Saurayi da Budurwa da ita wato Bara"atu,wadanda ke zaune a anguwar sabon garin jega.
Sama"ila ne Babba sai kaninsa mai Bi masa,Ahmed wanda suke ma Lakabi da Bafashi,Zakariyyah ya kasance Talakane mai karamin karfi Kowa dai yasan Garin jega gari ne na kasuwanci da Neman na kai,Shiyasa Zakariyya ya gwada kananan Sana"o'i ba iyaka ammh basu karbeshi ba Daga karshe sai ya koma sana"ar gini kawai itace ta Tsayamai yake Rike da kanshi da iyalanshi harzuwa Lokacin daya bar gidan Duniya.
Sama"ila da Bafashi Tun taso Tamkar yan Biyu ne saboda basu da Tsareyan Haihuwa Sannan kuma Bafashi yana da girman Jiki Shiyasa ya kamo Sama"ila da Tsahon kafa,komai nasu tare suke Gudanar dashi,Duk da shi Sama"ila bai da Hayaniya kamar Bafashi da yake da Surutu wanda kaf Halayyar mahaifiyarsu ya Dauko Haka Allah yayi ta da Shigen Surutu da Shige Shige da kuma Fadi ba"a Tambayeka ba Sabanin Sama"ila da ya dauko komai na Mahaifinsu Zakariyyah wanda kowa ya sani bashi da Hayaniya.
Ba"a sanyasu a makarantan Boko ba sai da sukayi Sauka a makarantan Allo,Wata makarantan gwannati aka sanyasu Saboda Rashin Kudi Sakamakon yanzu Zakariyyah girma ya fara kamashi ciwon baya da Ciwon jiki bai iya Juran Daukan kankare,akai Saboda Halin Yau da gobe karfinsa yafara karewa,ahaka dai sukayi ta gungurawa don ma Bara'atu, bata zama mace ce mai neman na kanta yan kulle kulle da Sana"ar cikin gida tanayi wani Lokacin dashi suke samu suna Rufama kansu Asiri.
Haka dai Rayuwa tayi ta tafiya da dadi ba Dadi Har sama"ila suka kamallah Babban Sakandiri a Daddafe,Dama aji daya aka sanyasu shida Bafashi,sunyi girma sosai domin a kallah Sama"ila lokacin zai kai ma Shekara Ashirin aduniya bafashi kuma Sha takwas,gama karatunsu yayi daidai da kasawar mahaifinsu wannan Dalilin ne yasa basu ci wani Burin Cigaba da karatu ba suka Dukufa taimakon iyayensu Sama"ila dai ya karbi gadon Sana"ar zakariyya na gini bafashi kuma ya fara Sana"ar Faci kuma Ahmadulillah Allah ya sakama Abun albarka kafin su Rufe Shekara sun zagaye gidansu da ginin kasa,suka kuma Fitar da wani daki inda zasu dinga kwana domin ada daki dayane tal acikin Gidan,Sama"ila ya hada Bulon Bafashi ya taimakamai sukayi ginin atare.
Saka albarkan iyayensu yasa suke cigaba cikin Sana"arsu ana haka kwatsam suka Zakariyyah Ya amsa kiran mahallaci sunyi kuka Sosai da kukan Rashin nagartattacen Uba kafin su Dangana,ashe wani rashin na tafe Tsakanin Rasuwar zakariyya da Bafashi wata goma ne shima yace ga garinku ne motace ta takashi har lahira wajen Tsallaka titi zuwa wajen dayake sana"ar Facinsa wannan karon mutuwan ta taba sama"ila harda saida ya kwanta Asibiti Bara"atu tayi ta kuka ya tashi shima kar yamutu ya barta sun dade basu dainakukan Rashin Zakariyyah da Bafashi ba kafin a hankali komai ya sakesu bata zauna ba, yan sana"narta ta cikin gida bata daina ba Shi ma Sama"ila ya dake da aikin Karfi Tukuri domin Dogara dakai Yafara karfi a harkan ginin har daukansu ake gari gari domin zuwa yin ginin cikin Hakane suka tafi wani Kauye dake kusa da garin jega,achan Allah ya hada Sama"ila da Zaliha wacce ta kasance marainiya ce bata uwa bata da Uba sai yayanta guda daya mai suna Maude shima baiyi Aure ba lokacin tana wajen Dangin mahaifiyarta ne suma neman kai suke da ita sama"ila na bayyana babu wani bincike da Bin Diddigi suka aura mata shi sai dai inda Hankalin Zaliha da yayanta Maude yakwanta ganin Sama"ilan mai hankali ne da neman na kanshi haka aka kawota garin jega aka kuma sakata cikin Dakin da ada yake matsayin nashi shida bafashi ko Abunda ba"aso dangin Zaliha basu kawota dashi ba Aikuwa Bara"atu tayi Surutu da mitar kamar me,Sai da sama"ilan yayi tabata baki ganin Zalihan tana kuka Dakyar ta bar mganar ammh kuma bashi zai hana ta chabama Zalihan gori ba.
Zaliha tafara sabuwar Rayuwa agidan Mijinta Sama"ila,Bata da mtsalan ci da sha da Sutura,balle na wajen kwana tana cikin kwanciyar hankali har tafara maida Jikinta,dama kuma bata da muni macece mai dirin jiki dana Fuska,Bata da wata mtsala sai matsalan Bara"atu maman mijinta kenan wanda daga baya ta Fahimci Halintane Yawan mita da Surutun Abunda ba"a sakata ba ga saka ido kan duk wasu al"amuransu ita da sama"ila bata damuwa tunda dai bata takura mata kamar chan gida,Tunda akayi Auren ba wanda ya taba zuwa Dubata yayanta maude ne ke Zuwa Lokaci bayan Lokaci in ya samu dama Shima yana hannun wani malami ne,wanda ba dangin iya bana baba ya Daukeshi yana cidashi ammh fa yana mai aiki gona da duk wata walaharsa Shiyasa shima baya samun Lokaci sosai.
Rabon Haihuwa dai dama ita ta Hada Zaliha da Sama"ila domin Wata uku da Aurensu ta fara laulayi Nan fa Bara'atu ta saka Mitan,sama"ila ya kwaso musu aiki suna zaman zamansu gana dawainiyar Zaliha gata yaron Cikinta ammh ganin sama"ila na Murnan samun karuwan dayayi ne yasa sai ta rage Mitan datake yi ammh sai dai in bataga Zaliha ta gifta ba sai ta tabe baki ta saki wata mgana mara dadi,sama"ila da Zaliha basu damuwa saboda sun saba in tafara mitanta kulewa suke cikin daki suyi mata kunnan Uwar shegu in tagaji da kanta take shuru itama ta kule kanta Cikin Daki tashafa ma kanta Lafiya.
Haka Dai Zaliha tacigaba da Renon Cikinta Sama"ila na matukar son yaga Zaliha ta haihu,saboda yana ganin bashi da kowa sai Abunda Zaliha zata haifamai cikinta na Shiga wata tara ta sunkuto kyakyawan yaronta mai kama da Ubansa sak,Wanda Bara"atu da kanta ta karbi Haihuwan ita ta gyare Maijego da Jinjiri,wanda tunda ya Fado Duniya yake Chanchara ihu Nan fa bara"atu ta dagashi samat tana fadin Daga ganin yaron nan za"ayi Fitinanne daga zuwa Duniya sai damu mutane da kuka daganan kuma sai neman nono yana mamulan baki Sama"ila dawowa kawai yayi yaga zaliha bisa gado ita da yaronta bakinshi yaki Rufuwa nan take ya Dauki yaron ya Rumgumeshi yamai Huduba da AHMED,yanayi yana kukan Farinciki dana Rashin kaninsa Bafashi.
Daga Dangin Zaliha bayan Sama"ila ya kira maude ya gayamai kuma ya tababbatar da ya gayamusu ba wanda ya lekota mauden ne yazo ya kawomata atamfa daya da Rigan yaro guda Biyu masu kyau,yazo ya dauki Ahmed ya sakamai albarka Shima wannan karon dai Bara"tu sai da tayi mitan ganin ko tayi mitan ba biyan bukata yasa ta kama kanta Ranar suna Sama"ila ya yankama Ahmed Shakika ya kuma yima Zaliha kayan Fitar suna anyi Suna daidai na marasa karfi,makota da abokan Arziki,sunzo sun tayasu murna Cikin kwanciyar Hankali Zaliha ke Cigaba da Jegonta dole dai Uwar naki Bara'atun ce komai na Zaliha ita ta mata wankan jegon da gyaran mata sai kuma Allah ya hada Jininta dana Jikanta Ahmed tun yana jajirinsa zata kama ta goya ta cigaba da ayukanta,Gashi Ahmed da kukan dare da kuma Tsotso wanda Cikin kankanin Lokaci Zaliha ta fara rama saboda Nonon yayima Ahmed kadan sai da Bara"atu a dinga Hadamai da kunun Waken Soya itama Zalihan tana sha,shiyasa tafara maida Jikinta har shima Ahmed din ya cigaba da samun Ruwan Nono wadattace.
Rayuwar dai tana Gungura yadda Allah ya Tsara,Ahaka har Ahmed ya Shekara hudu aduniya ba inda baya Zuwa,sai kiriniya da kin jin mgana ammh akwai miskilanci irin na babanshi,tun yana karaminsa suka fara takun saka da Bara"atu wanda Da sunan kaka bakinshi ya fara Budewa gari na waye zai gudu dakin kaka yafara mata bare bare,su dinga Fada kenan ta kamashi ta zaneshi in ya mata barna ya koma wajen Zaliha yana kuka ammh bazai hana anjuma ki gansu tare ba tana mai hira yana Bangala mata dariya gaskiyan kakane Tun Duka iyayan Ahmed nada rai take cin kashinshi da Fitsarinsa domin wani Lokacin wajenta yake kwana yayi fitsari ta wanke komai dai,ta wahala dashi Fiye da mahaifiyarsa Zaliha,wacce ta daukema kaka Hidimar girki shiyasa Sai Ahmed ya koma dan gidan kaka,sama"ila komai ya samu Zaliha da Ahmed da kaka ne,lokacin kuma yana gabar samu Allah ya sakama Abun albarka.
Ahmed sai da ya Shekara Shida kana Sama"ila ya sanyasa awata private sch dake nan kusa dasu Kullum da safe kaka ke kai Ahmed makaranta ta kuma je ta Daukoshi suna zamansu Lafiya cikin Rufin Asiri basu da mtsalan komai Zaliha kuwa tun bayan Haihuwan Ahmed sau daya taje garinsu bata kara komawa ba tunda ta lura ba wanda ya damu da ita Yayanta maude kadai ke kula da ita Wanda yake zuwa Dubasu lokaci bayan lokaci kuma baya zuwa Hannu Rabbana sai yazomana da Ahmed da Zaliha wani Abun,kuma gashi jininsa ya Hadu da kaka in yazo dakinta yake Sauka suyi ta Hira in zai tafi ya cikata da sabulai da omo su Rabu Tana tamai addu"a da Fatan Alheri domin Kaka akwai son mai kudi irin mai hannun kyauta din nan kullum cikin Zagi da mitan masu kudin anguwansu take tana Mitan basu Fitar da zakka.
Tsausayi baya wuce Ranarsa kuma Mutuwa dayace ammh kowa da sanadin mutuwarsa,Ahmed na aji biyu a matakin karamar sakandiri Da jajircewan Maihaifinsa da kakarsa akansa,watarana Sama"ila sun fita wajen gini ya dauko kankare asaman kanshi ya Hau bene tunda chan sama nesuke aikin,jiri ya kwasheshi ya Fado daga sama zuwa kasa sai gawa domin ko Shurawa baiyi ba kansa dai ke Zubar Jini ya Fita lafiya da kafarsa ammh sai aka shigoma dasu kaka gawar Sama"ila Kaka ta Rude iya Rudewa ammh bata kai Zaliha da Ahmed ba wadanda suka sume sai da aka danganta Sama"ilan gidansa na gaskiya kana suka Dawo Cikin Hayyacinsu sunyi kuka Sosai kamar Ransu zai Fita kakace ta koma lallashinsu Duk da itama taga Rashi mutuwar miji data zaratan ya"ya har guda Biyu.
Mutuwar Sama"ila itace ta kara Fito da Talauci da Rashin samun Wadata,Kaka ce ke tsaye kan komai da yar sana'arta da Cikin gida na goma da Hamsin,Zaliha kuma Sai ta fara sana"ar Surfe da wankau saboda karatun Ahmed Ita da Kaka suna tsaye kan Ahmed iya bakin kokarinsu Ahmed ya taso da Zuma da Burin yayi Ilimin ko domin ya Taimaki mahaifiyarsa da kaka data Wahala Dashi in ya dawo makaranta baya zama yana zuwa Cikin gari gwangwanaye yana tarawa in ya taru ya saida ya kawo kudin gidan a kara a cefene Kaka kuwa tayi ta Shimai albarka,haka dai sukayita gunguwara rayuwarsu har Ahmed ya shiga Babbar Sakandiri cikin ikon Allah ba"a ciresu a makarantar dayake ba Kaka da Zaliha suna Tsaye kan karatunshi.
Yana aji biyu a matakin Babban Sakandiri Alhaji muhammed Argungu ya dawo anguwarmu da zama kuma kusa damu Domin gida biyu ne tsakaninmu wani katon gidan Bene ne mai kyau da Tsari wanda yaji kayan alatu rayuwa na jin dadi,Tun ana ginin anguwa ta dauka cewa Alhaji muhammed argungun ne zai dawo nan anguwar domin kaf Garin Jega ba wanda baisan Waye Alhaji muhammed ba Saboda Kudinsa Dan kasuwa ne Sosai wanda ya Tara Abun Duniya kan kasuwanci bassakawce ne na gaba da baya mai neman na kanshi ammh Alhaji muhammed irin mazan ne mugaye wanda basu san Taimako ba Hannunsu a damke yake,ga son Abun Duniya dagashi sai yayanshi da matanshi ke Cin Dukiyarsa,ammh ko cikin yan"uwansa kowa ma ya kama kanshi Saboda ko kazo da kukan ba bazai taba Share maka Hawaye ba Tunda kowa ya Fahimceshi bamai Rabanshi Shima bai damu ba ba,haifaffan garin argungune uwa da uba,kasuwanci ya kawoshi garin jega sai ya Shafe shekaru bai je sai anyi mutuwa ko kuma wani abun ya faru, yake zuwa ya jefasu da dubu biyar ya kara gaba kowama ya kama kanshi da hangen kudinsa Tunda bazasu ciyoba,Shima baya harka da kowa sai yan kasuwa yan"uwanshi daga kowani jaha musamman kano Domin yana Harkan saida atamfofi ne da Shaddo da kayan yara toh ya wanci yana da Alaqan kasuwanci da Kasuwar kwari dake cikin garin kano.
Alhaji Muhammed agurgun yana da matan Aure guda Hudu ne Cif bayan wadanda ya aura kuma ya saka saboda ba wani sakin Hannu yake ba ana bushashan kudi ba,badai a zama da yunwa kuma ba laifi yana musu Sutura,toh wasu in sunzo sunga sabanin Abunda suka zata sai zaman lafiya ya kare daganan sai Rabuwa,Ya"yansa na haihuwa Ashirin da biyar Mata da mata wasu iyayensu na gidan wasu kuma basu da iyaye acikin gidan,Hajiya mairo itace uwargidansa wanda sukayi Auren Saurayi da Budurwa,yar"uwansa ce suna da alaqan Zumunci sai Hajiya Badariya,sai Hajiya Hansa"u sai da karshensu Hajiya Marwa,kuma dukkansu shi ya kaisu makka suka sauke Farali,Samiha tana daga cikin ya"yanshi wanda iyayensu suke gidan ita din tana Jerin yayan Karshene wato yara kanana,Autar Hajiya mairo ce wanda daga kanta ne ta Dauke Haihuwa Samiha nada yayyi guda Takwas mata Hudu maza hudu matan kowacce tayi Aurenta hakama Mazan wanda ba wanda ya Dogara ga ubansu abu daya yayi musu daya ingatasu shine ya Turasu karatu kasashen waje suna tsaye ga kafafunasu,Samiha sun taso lokacin Kuruciyarsu da diyar Hajiya Hansa"u Maimatu,tare suka taso kamar kansu daya,komai tare suke sun tasowarsu Samiha yarinyace mai son Takama da wadaka cikin Arzki gashi ta fito gidan kudi ammh kuma ba kamar yadda Taci Buri ba tana da Faran faran da jama"a sabanin maimu datake da karancin fara"a ga Wulakanci da dagawa Duk da itama Samihan tana da dagawan Wani Lokacin ammh bata kai maimu ba.
Dawowarsu anguwar su Ahmed da kuma maidasu makarantarsu ne silan Haduwarsu da juna Lokacin suna matakin Aji daya a babban Sakandiri dayake suna da Saurin karatu,alokacin shekarar samiha goma sha Biyar ne,aduniya sai dai tana da tsawon kafa sai ka ganta kamar Babba,Farkon Haduwarsu da Ahmed ya samo asali ne da koda yaushe suna yawan ganinsa ahanya in zashi makaranta Su suna motane ita da maimu direba ke kaisu shikuma akafa yake Zuwa,Samiha tana yawan ganinashi bata dai taba mai mgana bane sai da labarinsa yafara Fitowa a makaranta Allah yabama Ahmed Baiwar Basira da Hazika makarantan tana matukar alfahari dashi,Ita kuma Samiha tana bala"in son Taga mutum mai kwakwalwa da Kuma Basira sai tafara neman Hanyar da zata saba da Ahmed da Farko,ta fara zuwa har ajinsu ne ta mai sannu in yana Zaune yana karatu in an fita break,bai damu ba ya amsa saboda mata dadama suna Hurdashi saboda Baiwarsa,ganin samiha Bata samu Fuska ba sai ta fara mai mganar ko zai rika koyamata karatu,baiyi gaddama ba,yace kullum in an tashi break ta rika zuwa zai dinga koyamata Jiki na Rawa Samiha take zuwa Suna karatu da Ahmed a gaban ajinsu Maimu tayi ta ma Samiha Mitan meya hadata da Ahmed daga ganinshi yaron Talakawane kila ma Alfarma yake ci a makarantan,samiha dai bata jita ba Domin Haka kurum taji komai na Ahmed ya mata yanayin maganarshi da komai nashi yana tafiya da imaninta uwa uba kuma Basirarsa yadda komai yake kanshi komai na Ahmed na baiwa ne.
Cikin Hakane tayi ta Shigemai har ta gane anguwarsu Daya kuma Ma Makota suke da wannan Tayi amfani in direba yazo daukansu sai tace su dauki Ahmed da Farko yaki sai da Samiha ta nuna bataji dadi bane kana ya yarda,yake shiga maimu kuwa,kamar zata mutu saboda bakinciki har gulma takai gida ba wanda yabi takanta Saboda dai Samiha yar gatan Hajiya mairo ne bata laifi komai tace ta zauna,Shiyasa Ahmed ya cigaba da Rabawa a motar gidansu samiha kullum da Safe zasu Biya gidansu su daukeshi kuma in an tashi makaranta sudawo Dashi Ahmed bai wani yarda ya saki jiki da Samiha ba ammh ita ba Ruwanshi bai yarda yayi ma kowa Hirar samiha ba tun bayan daya taba mganarta Kaka ta tasomai tace ubanta ko hakkin makota baya fitarwa ya kama kanshi Zaliha kuwa fada tamai kan Shigema ya"yan masu dashi.
Fara Shigar samihan gidansu Ahmed Rasuwar Zaliha ce wanda ta kwanta Lafiya gari na wayewa sai gawa hakika Ahmed yaji wannan Mutuwa mai Farat daya Hakama kaka tayi kuka Sosai Sai bayan Rasuwar Zaliha ne danginta sukazo bayan anyi bakwai suka koma kawu maude ne kadai ya Zauna da Ahmed na Sati biyu yana bashi baki Rasuwar Zaliha ta saka samiha takarajin Tsausayin Ahmed ita ta matsama Hajiya mairo tazo tamusu gaisuwa,Alhaji muhammed ko lekau kuma ta kofar gidan Direba ke Wucewa dashi amota baitaba Tsayawa ba dama ba wanda ya damu dashi sanin Halinshi tunda ya dawo anguwan ba wanda yataba karuwa dashi ko na Naira Biyar Ahmed ya dade agida bai koma Makaranta ba Samiha duk ta damu kusan kullum gidansu take Wuni wajensa Tun yana Nuna bayaso har ya hakura ganin bazata Daina ba Kaka ma ta koreta ammh ko tatafi sai ta dawo har tagaji ta kyaleta,Yana kokarin koyama Samiha karatu harda na bangaren Addini domin shima ba bayaba yana da sani sosai,Samiha yarinyace karamai mai Shiga rai Cikin Lokaci suka shaku da Samiha sosao itace ke zama Dashi tana mai hira in taganshi yana Zaune cikin damuwa bata sukuni sai ya saki Ranshi,a daddafe da taimakon kaka ya koma Makaranta yana cigaba da zuwa kwatsam kuma sai aka fara biyan kudin jarabawa,gashi kaka bata dashi itama yanzu ba sana"ar saboda dashi suke ci su sha yau da gobe bata bar komai ba kawu maude kuwa yayi ta nemansa ta waya bai sameshi Ya zauna yayi kuka Kaka tace sai dai yayi hakuri in da Rabo kila gaba sai ya zana Samiha itace ta Fahimci damuwar Ahmed ta koma gida tana ma Hajiya mairo kuka dole ita tazo har gidansu Ahmed suka tafi makarantar tayimai Rigistration din Jarabawar WAEC da NECO, godiya kuwa Ahmed harda kwallah kaka ma har gida taje tana ma Hajiya Mairo godiya ita ko Maimu tana ganin Samiha tana kokarin jawo musu Raini kula irinsu Ahmed.
Wannan Abun da Samiha tama Ahmed shiyafara samata wani gurbi acikin Zuciyar Ahmed wanda ita dama Tuni ta Fahimci tana Cikin mayen son Ahmed,ko da bata fadamai ba Shima ya sani kullum tana hanyar gidansu komai ta samu na Ahmed ne kaka tagaji da mitan ta kyaleta ammh samiham da tazo zata Shiga dakin Ahmed sai kaka ta hana tayi ta bala'i tana bamai maida ita yar iska acikin gida Shiyasa datazo zai fito kofar dakinshi ya Shinfida Tabarma su zauna da samiha su gama karatunsu su koma Hira koda maimu takai gulman Samiha wajen mahaifinta wajen tana Bin Ahmed gida yaso yaci kaniyarta ammh sai Hajiya mairo ta Rufemai baki da cewa yaron yana koyama Samiha karatu ne da wannan Mganar ya kyaleta tana Cigaba da zuwa gidansu Ahmed.
Kwanci tashi babu Wuya awajen Allah gashi har su Ahmed sun kamallah Jarabarwarsu duka sai jiran sakamako Samiha ne suka Shiga matakin ajin akarshe shi ya Dage yana kara koyar da ita Wasu abubuwa duk da Haka bai Zauna ba yana Fitan neman na kanshi Saboda yana da Burin Karatu mai Zurfi yaso yayi aikin gini kaka ta hana tace Tunda yayi sanadiyar mutuwar sama"ila baxata kara bari wani nata ya kara sanar"ar gini ba sai ya koma yin Jari bolansa da Abunda ba"a Raasa ba Samiha ta na matukar kaunar Ahmed shima haka ammh bazai iya Furtamata ba, saboda Tazaran dake Tsakaninsu kaka kuwa ta ganesu kyale Ahmed din tayi taga don Ubanshi iya Gudun Ruwanshi.
Result ya Fito kuma Alhamdulillah Ahmed ya samu kyakyawan sakamakon cikin ikon Allah ya kawo kawunsa Maude wanda ke Zaune acikin Birnin kebbi yanzu yana dan Taba kasuwanci,sama sama yayi Aurensa da matarsa Naja"atu,shi ya karbi Takardunsa yamai alkawarin nema mishi babbar Collegin garin Birnin kebbi,ta hanyar baban wani abokinshi jin haka yasa Ahmed ya dake da addu"a da neman zabin Allah kaka da Samiha na tayashi Cikin ikon Allah kuma ya samu Admission na zama daya daga Cikin Daliban Federal collage Birnin kebbi murna wajen Ahmed ba"a mgana Sai Shirin Tafiya Allah yasa kawunsa maude ya taimaka da taimakon kaka dana Samiha wacce Duk Duniya bashi da Abunda zai saka mata da ita bayan Kauna,domin itama tabada gudumuwaa wajen inganta Rayuwarsa 20k ta kawomai tace in ji mamanta Ahmed yaji kamar yayima Samiha kuka da su suka hada ya siya yan kayan Bukata tunda cikin makaranta yace zai zauna ba gidan kawu maude ba saboda yana son ya maida hankali ga karatu kuma ma gidan kawu mauden yayi Nisa da makarantan
Samiha ta tada Hankalinta lokacin dataga Ahmed zai tafi ya barta Ranar da zasu tafi Chan Birnin kebbin shida Kawu maude da kaka datace ko da Bala"i sai taje taba idanuwanta abincin,Samiha na kuka tana Rike Ahmed wai karya tafi Domin taso sakama Hajiya mairo Rigimar zata raka Ahmed ta dakatar da ita da fadin kar ma ta fara,Kawu maude yana kallon Ahmed da Samiha cikin Tsausaya musu na fadawa Soyayyar Juna cikin kananan Shekarunsu Domin Ahmed duka duka lokacin shekaransa Ashirin da daya ne aduniya samiha kuma sha Shida kaka kuwa gefe ta koma tana tabe baki aranta tana fadim kyayi ki gama ki barmin jikana bazan iya da dangin matsolanci ba Haka ta Dinga gayama maude da sukayi gaba suka bar su Ahmed din baya bai Taho ba sai da ya lallashi samiha da alkawruka da dama bai kuma yarda ya tafiba sai da ya jadaddamata Kalmar ina sonki Samiha haka ta koma gida tana kukan Damuwan Rashin Ahmed dana Farincikin Soyayyar daya Furtamata alokacin data kusa sarewa da zai Furta mata yana Sonta.
Shi ya Rufe gidansu da kwado yacimma su kawu maude, kaka sai Hararansa take shiko batama ta ita yake ba Har suka isa Tasha suka samu motar Birnin kebbi suka Shiga Ahmed ya kasa Mgana kewar Samiha ta Isheshi kaka kuwa sai da ta damu kowa acikin motar haka take daga murya Sama Kawu maude na gabam mota ammh Dole sai tayi Hira dashi hiran ma mara Dalili,acikin mota ta hadu da wani tsoho shima Irinta masu Surutun Fadi ba"a tambayeka ba,suka addabi kowa acikin mota kuma ba damar kayi mgana sai yamzu kaka ta taso maka Ahmed dai ba baki har suka isa Gidan kawu maude suka fara sauka yammah tayi nan suka kwana Naja"atu matar kawu maude na ta Haba haba dasu,gari na wayewa kawu maude da kaka suka Raka Ahmed cikin makaranta yayi Rigistration da sauran cike ciken Hostel,ta hanyar Baban Abokinshi dake Tuka motar makarantan,wato yana daya daga cikin Direbobin cikin makarantan Kenan,basu tafi ba sai da suka rakashi har Hostel dinsu na maza,dama tun achan jega yagama siyan abubuwan abinci da kuma Risho wanda zai Bukata,su kaka suka tafi suka barshi da kewa gata bakunta gata kewar gida gata kewan Samiharsa,kaka kwana daya ta kara ta koma jega ta bar Ahmed a birnin kebbi,itama dole taji gidan yayi mata Dabam.
Hakanan Ahmed ya saki jiki yacigaba da karatunsa Ahmed bai da sakin Jiki da mutane Shiyasa har ya dau Tsawon Lokaci amakarantar bai da aboki kwara daya ammh abokan Arzki suna da yawa barinma da Basiransa ta fara bayyana cikin Deparment dinsu na Business education.
*Aisha alto..*
*Janafty*