Page 6
*SILAR HALLACI*
*Mallakar:Janafty and Aisha Alto*
*Bojuwa herbs*
*By*
*Surayya Dee.*
****.*
*Sanyi flusher!*
*Yana wanko dukkan sanyin mara, mahaifa Har ma da jijiya.*
*Tasirin da karfin maganin sanyinmu ya wuce misali don kuwa duk wacce ta siya sai ta dawo ko ta turo wasu*.
*Alhamdulillahi Allah ne ya yi mana.*
*Tightening set na hade mace ta dawo zamzam tamkar yar budurwa, kuma babu na insert a cikin park din*.
*Tasirin magani idan andafa tamkar yankan wuka ne shiyasa kazar sababi da ciccibin garari na Surayya halin yau suke da kyau da tasirin gaske a jikin mace.*
*Muna da gimbiyar zabuwa da tattabarun alheri.*
*Akwia packages na mussaman ga amare, uwargida, zawarawa da masu jego.*
*Tuntubeta a wannan lambar*
*****
*Don samun ingantattun kayan gyara da babu algush.*
*Nation wide delivery*.
*🅿️6*
"Tafiyar Ahmed Makaranta yasa Gabadaya hankalin Samiha ya tashi ta daina Walwala da cin Abinci Sosai ta fara rama bata da aiki sai tunanin Ahmed kafin wani Lokaci duk ta zama wani iri da ita duk bata da kuzari Hajiya mairo na Lura da ita tun tana Daukan Lamarin na Samiha a yarinta har tafara Tsorata da lamarin Samiha da Ahmed din.
Shima a bangaren Ahmed din hakance ta kasance dashi Shima kewar gida gabadaya ta lullubeshi gefe daya kuma ga kewar Samiha wacce taki barin Zuciyarsa gashi bashi da waya a hannunsa balle ya Kirata domin Tuni Samiha ta mallaki wayar hannu mai kyau da Tsari Dole kishiyar naki ya maida hankalinsa a kan karatunsa ammh ba domin ya iya Cire Tunanin samiha acikin Ranshi ba,Kawu maude ne yake Zuwa Dubashi Lokaci bayan lokaci yana iya bakin kokarinsa akansa Domin baya zuwa hannun Rabbana yar miyan ne da kuli kuli da garin Rogo da Sauransu haka zai riko mishi Babu Abunda ya nema ya Rasa na Makaranta sai Abunda ba'a rasa ba Kudin Handout kuwa yawancin Daliban Ajinsu sun Daukemai nauyin haka saboda yana Taimaka musu bangaren karatunsu yana Kokarin koya musu Fiye da yadda Malaman suka koya musu shiyasa kafin a Rufe wannan Hutun Semester Sunan Ahmed Isma"il Jega yagama Tambari cikin Department dinsu dama Zagayen Makarantan Gabadaya.
Hutun Da su Ahmed suka samu na Farko na Sati uku ne,Gashi bai da kudin mota,Dole ya fara isa gidan kawu maude wanda kuma Shima ba kudi ahannunshi shiyasa sai da Ahmed yaci sati daya a gidan kawu maude kana ya bashi kudin mota ya Taho jega Ranar kaka Ta rasa ina zata saka Ahmed saboda murna ta dinga Taba Wuyansa tana fadin ya Rame Sosai Shima din Rumgumeta yayi yana Dariya mai Cike da Farinciki.
Duk da Farincikin dayake ciki na ganin Kaka bai gama cika Murnansa Saboda baiga sanyin idanuwansa ba Samiha kuma shi ba zuwa gidansu yake ba,in ma yaje toh yaje raka samiha gida ne yana ganin yayi kankanta da zuwa Kofar gidansu Samiha wanda yasani cewa tsakaninsa da ita Abu ne mai tazara,har yayi wanka yaci abinci yana Zullumi Da Tunanin samiha duk hiran da kaka takeyimai baya wani Jinta sosai Ganinshi da jinsa gabadaya suna wajen samiha ne,Ganin bashi da mafita bayan sallar la"asar yazo kofar gida ya tsaya yana Tunanin Tabbas Samiha zata wuce Zuwa islamiya ammh kuma har yagaji da zamansa baiga Motar gidansu ta wuce ba haka yagaji ya koma gida,Sai da Shida na yammah tayi ya dawo ya Tsaya Lokacin ne kuma motar gidansu samiha ta Wuce yakurama Motar ido kamar yana ganin Samihan azahiri wanda kuwa bata ciki maimu ne kadai taje islamiyan yau Samiha na gida batajin dadi,ita Maimu din ta ganshi sai ma tabe baki datayi ta kauda kai domin tasan duk damuwan Samiha harda Rashin Ahmed atare da ita tana mamakin yadda Samiha ta fara son wanda bai dace da ita ba,Sai da ta koma gida take fadama Samihan cewa ga Ahmed chan ya Dawo da Farko Samiha ta Zata karyan Maimu ne sai da ta Rantse mata kana ta yarda,tatashi da gudu mayafi a hannu zuwa gidansu Ahmed,wanda Fitowarsa kenan daga masallaci ya Shigo gida yana Tsaye kofar dakin kaka suna Mgana samiha ta fado gidan tana kiran sunan Ahmed shima jin Siririyar muryanta dayayi kewa yasa ya waigo yana kallonta Fuskarsa cike da Annuri Samiha saboda murna ganin Ahmed batasan sadda ta Fada jikinsa ba tana sakin mai kukan Shagwaba Duk da yaji wani iri sanda Samiha ta fada jikinsa nashi bai sa ya Tureta ba sai ma Rike kanta dayayi yana Sakin Mirmishi Salatin kaka kawai sukaji acikin kansu Da sauri Ahmed ya Rabata da jikinsa yana kallon kaka matse kwalla kawai kaka tafarayi tana Fadin Makarantan da Ahmed yaje ba karatu yaje koyowa ba sai iskanci da lalacewa Duniya tazo karshen yaran zamani sun san Rumgumar Namiji su lokacinsu Ko kallon Idon Namiji bama Basayi saboda iyayensu sunce musu ko hada ido da Namiji mace tayi zata samu ciki mai Samiha da Ahmed zasu yi banda Shekema kaka da Dariya itako Haushin Ahmed ne yakamata tana Tunanin baida Hankali Suna fama da kansu ammh zai kara musu Wahala dama Uban samiha na sakin Hannu ne sai ta yarda ya Aureta ammh haka kurum yadda ta Wahala da uwarshi yanzu ma ta dawo tana Wahala da matar da zai aura bazata sabu ba..Samiha kuwa Taki tafiya gida ga Dare yaayi sai da Ahmed ya nuna bacin Ransa kana ta yarda ya Rakata gida Suna tafe kowannensu na gayama Dan"uwansa yadda yayi kewarsa Wannan Hutun Wata irin Soyayyace mai girma da Tafin Burika ta gudana Tsakanin Samiha da Ahmed,wanda har gidansu ta kaishi ya gaida Hajiya mairo tamai karban Mutumci Sosai ammh bawai domin Tana Tunanin Shirmen Samihan zai iya Tabbata ba Domin Dukkansu yarane kanana akwai Tarin kuruciya tare dasu basu gama Sanin Ciwon kansu ba Shiyasa bata fara kokarin Dakatar da Samihan ba Tun farko.
Wannan karon na 20k Samiha ta kawoma Ahmed tace ya kara inji Ummanta ya rasa da wani kalma zai ma Samiha godiya illah dai ya kara jadadda mata har gaban Abada bazai manta karamcinta gareshi ba dasu yasiya Abunda yake Bukata ya bama kaka saura,sauran kuma yayi kudin mota ya koma Makaranta wannan karon Har Tasha Samiha ta rakashi Tana mai Shagwaban zatayi kewarsa,shi kuma yana kara Jadaddamata ta maida Hankali a karatunta saboda karatowar Jarabawarsu ta amsa da Toh domin tayi alkawarin bazata bama Ahmed kunya ba.
Ahmed ya koma Makaranta cikin kwanciyar Hankali yana Cigaba da karatunsa gefe daya kuma yana Fama da Tunanin Samiha itama anata bangaren Hakane bataji kuma bata gani sai Ahmed dinta wanda Duk wanda yake tare da ita ya san wanene Ahmed awajen Samiha,hutun Zangon karatunsu na karshen Nce1 dinsu ne ya dawo gida daidai kuma Lokacin su Samiha zasu zana Jarabawar Karshen Karatunsu wato WAEC da NECO,Ahmed shine yake Taimaka Samiha kan wasu Darasan,kamar darasin Lissafi Chemisty da physic hatta Maimu Ta sani cewa Ahmed nada kokari itama Dalilin koyama Samihan dayakeyi itama take samun wani saukin in bata iya wani abun ba sun kamallah Waec ba dadewa Ahmed suka koma Makarantan amatakin Zangon karatun aji biyu na Farko ya bar samiha na fama da karatun Neco ahaka dai a daddafe samiha ta kamallah Jarabawarta cike da Nasara da Farinciki sai da bacin ranta daya Ranar da sukayi candy Ahmed dinta baizo wajen ba sai dai yan"uwanta da iyayensu wanda har aka gama suka koma gida bata da wata Natsuwa Shima Ahmed tana Ranshi kuma yana Lissafe da lokacin yadai mata addu"ar samun Nasaran Rayuwa Hutun da suka samu na Farko karatu yadau zafi bai dawo Jega ba Haka samiha zata zo ta samu kaka tana mata kuka Tun kaka na banza da ita hardai ta gane Abun na samiha bana Wasa bane ta koma tana lallashinta dakyar take Hakura ta koma gida,Har Jarabarwar Waec dinsu ta Fito Ahmed bai zo Hutu ba jega kamar yadda Ya saba Ran samiha ya gama baci na Rashin zuwan Ahmed gashi tafi ma maimu samun sakamako mai kyau kuma ta saniba kokarin kowa bane sai na Ahmed hatta da Alhaji muhammed haka ta fadamai bai damu ba illah yana nuna Farincikinshi nan take batare sanin kowa ba ya Biya musu jamb ita da maimu saboda yana son suyi karatu mai Zurfi,Neco itama ta fita wannan karon ma Samiha ce ke gaba tayi murna sosai ammh bata bar Fushi da Ahmed ba,sun zana jamb kuma Dukkansu sun samu Nasara batare da Bata lokaci ba Alhaji muhammed ya nema musu makarantu,Maimu tasamu Nasaran samun addmission a Federal Univerty Birnin kebbi ne ita kuma Samiha ta samu Usman Danfidoyo University sokoto akwai Ranar dataji labari tayi bure akan bataso ita federal collage of Edu take so Birnin kebbi saboda Ahmed dinta tana so su dawo kusa,Alhaji muhammed bai matsa mata ba Hajiya mairo ne ta mata jan ido ammh Samiha taki Tace ita dai nan take so har Hajiya mairo tayi Fushi tana Fadin saboda wannan sakaran yaron kika zabi chan ko.? Duk cikin yan"uwanki uban wa kika ga yayi Nce banda Kin zama Shashasha ana kokarin maida ke Mutum bakyajin mgana toh tun Wuri ki dawo cikin Hayyacinki Domin bazaki taba Auran Ahmed ba..Samiha bata damu da Kalaman mahaifiyarta ba tana ganin Cikin Fushi ta fada ammh ita ta sani ba wanda yakai Hajiya mairo sonta da son Farincikinta Ahmed na makaranta bai san Abunda ke Faruwa ba,suna Zangon karatu na karshe a Nce2 dinsu bashi cikin makarantan ma yana gidan Kawu maude sun fara Teaching pratice dinsu na wata shida,nan kusa da gidan kawu maude ya samu wata primary yana teaching pratice dinsa aka gama ma Samiha komai na shiga makaranta hatta da Hostel ta samu acikin makarantan Tana ta murna zata koma kusa da Ahmed hakama maimu angama mata komai na Tafiya Jami"a bata tare da ta tsaya damuwa da Samiha ba wacce babu Abunda ya dameta ita kawai Ahmed ta sani kuma shi take muradi,lokacin da suka gama teaching pratice ya zo gida Hutu sai akayi Rashin sa"a Samiha bata nan sun Tafi argungun ita da Maimu zasu yi musu kwana Biyu Shima din bai jima ba kwana Takwas kawai yayi ya koma Birnin kebbi ranar daya koma Ranar su samiha suka dawo Tana zuwa kaka tace mata yanzu Ahmed ya tafi Samiha ta ciji yatsa sosai ammh bata wani damu ba Tunda nan da Lokaci kadan zasu kasance tare.
Alhaji muhammed da Hajiya mairo ,da Hajiya hansa"u suka kai Maimu da Samiha makaranta da Tarin kayan zaman makaranta da kuma kudade masu yawa,Samiha suka fara kaiwa kafin su mika maimu,Ahmed baisan samiha tazomakarantan ba ammh Ita samihan su Maimu nawucewa Kayanta kawai ta ijiye cikin Hostel dinsu ta Bazama neman Department dinsu Ahmed domin babu Abunda bata sani ba nashi,komai da komai Shiyasa sanin Department dinsu Ahmed bai mata Wahala ba Tana Fadin sunanshi Ahmed isma"il jega to waye zai ce baisan Ahmed ba,karku manta ko abaya bamu bayyana Ahmed a matsayin namiji mai bala"in kyau ba ammh Ahmed mutum ne daya Tara baiwa Namiji ne mai cikar Zati da Haiba da kwarjini uwa uba kuma Farinjini Ahmed yana da Baiwan Farinjinin mutane karyane ya zauna waje ya tashi bai samu wanda yace yaji ya Burgeshi ba daga manya har yara,yana da baiwar Tsayawa azuciyar wanda yayi mu"amala Dashi duk da ya kasance bamai yawan Mgana ba balle sakin Jiki ammh Duk da Haka ya tara mutane kala dana Kirki dana Banza Kowa Ahmed domin sanin Yaro ne mai Tarin Hikima da baiwa Sanda aka nemo mata Ahmed yana cikin laborary yana karatu bai taba Tsammanin ganin Samiha adaidai wannan Lokacin ba sai gashi yayi Tozali da ita ya tsayawa yayi yana kallonta yana Tamtaman ita ce ko ba itace bace domin ta tababbatar mai da ita ce sai ta Sheko da gudu tazo ta Fada Jikinsa Lokaci daya tana sakamai kuka Saurin Janyeta yayi Daga jikinsa Saboda idanuwan mutane Da ke kansu ya Rikemata hannu zuwa wani Abun zama dake kafe aharaban Department dinsu suka Zauna kura mata ido kawai yayi cike da mamaki kafin ya tambayeta ta fara zayyanamai yadda Abun ya kasance,daga karshe tacemai taso irin Course dinshi ammh bata samu ba sai Biology Chemitry suka bata Idanuwansa sun cika da kwallah yana Tunanin wani irin so ne Samiha take mai,Yakasa bama kanshi amsa sai ya Bige da mata Fadan meyasa bata Tafi Jami"arta ba Tafa sani bakowa ke samun wannan damar ba saboda haka tayi Fushi tatafi ta kyaleshi shima bai Bita ba saboda ba"a barin Maza shiga Hostel din mata Ranar Ahmed ya kwana yana tunanin anya Shida Samiha kuwa zasu samu cikar Burinsu kuwa..? In ita tana da kowa Ubanta wani ne Shi kuma fa bashi da kowa sai kaka sai kawu maude Karatun nan ma daya ya yasamu yake yinsa,Ta ina zai fara..?Bashi da Abunda zai iya fitowa dashi na Auren Samiha yana ji ajikinsa Tamkar ya Zurma jiki da kananan Shekarunsa inda bai dace ba,Duk iya kokarin Ahmed na ya kaucema Samiha Abun ya faskara domin bata iya Fushi dashi Washegari kayan provision dinta ta raba rabi ta kawomai Rabi da kudin da aka bata ta bashi tace ya ijiye musu ko zasu bukaci wani abu,Ahmed bashi da yarda zaiyi da Samiha domin ko yace bazai karba bazata barshi ba,Dole ta sashi ya karba karma kuma ta sani Lokacin bashi da komai sai ya wuni bai ci abinci kuma,gashi bashi da komai a hannunshi kuma yana jin kunyar Kawu bazai iya zuwa yace mai bashi da komai ba Saboda yana iya Kokarinsa akansa.
Shigowar Samiha Makarantar su Ahmed ita takara taimakawa Wajen kara Shakuwansu da kuma Sakankacewa da cewa mafarkinsu da Burinkansu zai zama gaskiya koda yaushe suna Tare indai dayansu baida lecture,Sun zama kamar Cingam Saboda Koda yaushe Suna tare,basu tunanin komai kuma basaji basa gani dama bashi da kowani aboki sai Samiha itama bata da kawa da aboki sai Ahmed Shiyasa kowani Sirrinka Junansu sun sani,karatunta kuma Ahmed bai mata wasa yana Koyamata Abunda ya iya yana kuma kokarin Nuna mata ta maida Hankali akaratunta,in zai Shiga cikin gari tare suke zuwa su Shiga kasuwa suyi Siyayyah bayan ya rakata banki ta Fiddo kudi cikin bankinta wanda Abbanta ke shakemata account duk wata,suna zuwa gidan Kawu maude,in sun samu dama har cikin Jami"a Samiha tasa Ahmed ya rakata wajen Maimu wanda ta zama Babban mace ta kara wayewa Dagawa ta karu batayi mamakin ganin Samiha da Ahmed ba Domin tasan Ahmed Dalilin Nacewar da Samiha tayi na zuwa Fce din Birnin Kebbi Saboda Ahmed ne ta dai karbesu sama sama tana ta ma Ahmed wani yamutsa shikuwa ko Ta kanta Baibi ba Domin Dama maimu bata mishi Kyakyawan Kallo gani take Tafi karfin hulda da iri irensu.
Haka Rayuwar Samiha da Ahmed ya cigaba da gudana in sun samu Hutu tare suke komawa Jega,suka kuma dawo tare wani Lokacin babu Abunda ya fara Dagama Samiha hankali sai Jarabawar Fita dasu Ahmed suka fara duk sai ta shiga damuwa Shikanshi yana cikin Damuwan ne da Rashin Samiha domin ta zama wata bangaern na jikinsa,Samiha tana ji tana gani Ahmed ya kamallah karatunsa ya bar Makarantan dama Already tun kafin su gama yagama project dinsa,Samiha tayi kuka kamar Ranta zai Fita data dawo hutu sai ta saka kuka ita bazata iya da makarantan ba acireta nan fa Alhaji muhammed yace bata isa sai ta karisheta ita maimu din mai yacita data ke chan Hajiya mairo ma tamara mai baya Haka Samiha ta tattara ta koma makaranta bayan Ahmed ya lallasheta da ban baki da kuma alkawarirruka masu yawa da kuma Burin kasancewa Miji da mata,da wannan mganar yasa Zuciyar samiha tayi sanyi ta koma Makaranta tabar Ahmed a jega yana cigaba da zaman banza ba wata sana"a mai karfi.
Ahmed ya buga ya bugo yaga kozai samu wata sana"ar da zai rike kansa ko zai cikama Samiha alkawarinta da kuma cikar mafarkinsu ammh abu ya faskara Result dinsu ya Fito kuma ya Fito da kyakyawan samako Domin Ahmed dai ba baya ba,bai samu ko wace sana"a Ba domin komai na Rayuwar nan sai da kudi toh ina suka ganshi Dole ya koma zaman gida Babu Abunda yake yi sai kwanciya in yagaji yayi karatu a kuma Lokacin ne Yafara zuwa gidansu Samiha Zence in tazo hutu gida,Alhaji muhammed yayi matukar mamakin ganin Ahmed lokacin da Samiha ta gabatarshi a matsayin wanda takeso,bai mishi Wulakanci ba ammh yace yaje zai nemeshi,yaje ya samu Hajiya mairo sunyi mgana ita tace kar ya dakatar da Ahmed ya kyaleshi ya cigaba da zuwa saboda ita Samiham karta shiga wani Hali,ammh mganar Aure bata domin Har yaushe Ahmed din yake da zai ce zai Auri samiha da wannan Shawarar ya kyaleshi kawai yana zuwa wajen Samihan,shima dai anashi barayin Yana ganin Tsabar yarintane ammh Ahmed din nawa yake Dududu da zai Fara mganar Aure,Da kaka taji labari har tayi mita kamar ta daki Ahmed tace bai isa ba Shi yanzu yana Tatsitsin yaronshi har yasan Wani abu waishi aure toh ya Auro samihan ya ijiyeta a ina kenan,bai saurareta ba Domin alokacin baya ganin Mganar Kaka a matsayin wata mtsala ganin haka yasa Kaka ta wanke kafa taje gidansu Samiha ta samu Hajiya mairo da Alhaji muhammed tace karma su tsaya jiran Ahmed in yarsu ta samu miji suyi mata Aurenta kawai Domin dai basu da komai aduniyar nan kuma Ahmed dai ba yanzu zaiyi Aure ba,Hajiya mairo bata damu kanta ba Domin dama ita acikin Ranta ba wannan mganar Alhaji Muhammed ne yaji bacin rai ammh sai Hajiya mairo ta tausheshi wannan Dalilin ne yasa Yama abokin kasuwancinsa Alhaji Bashir wanbai Tayin Auren samiha,baiyi mai gaddama ba ya amince bawai domin yana da Ra"ayin kara Auren ba Sai domin kima da kuma abotaka dake Tsakaninsa da Alhaji muhammed,ammh sai me yana zuwa yaga Samiha sai Zence yasha bambam Domin aganin Farko dayayima Samiha tatafi da dukkan imaninsa Duk ko da takai sa"ar yarsa ta hudu ma in da kuma yana Aurar da ya"yansa suna kananan Shekaru da tuni yayi jika da ita,bai damu da kananan Shekarunta ba Duk ya Susuce akan samiha kuma aka gudanar da neman Aure nan da naa aka kuma sanya Lokacin Aure ba Dadewa Samiha bata da labari sai da Alhaji muhammed ya kirata yana gayamata ga kudin Sadakinta a hannunshi wannan Shine Dalilin Zuwanta gidansu Ahmed da Shawaran su gudu shi kuma yaki yarda da mganarta Suka rabu Zuciyoyi ba Dadi.
Tun Ranar Ahmed bai kara saka Samiha acikin Idanuwansa har aka Daura mata Aure,yayi kuka kamar Ranshi zai Fita babban Takaichinsa yadda ba"a bari Samiha ta karishe karatunta ba Tana Nce2 aka tsigeta aka mata Aure,yayi kokarin yaje ko Daurin Aurentane ammh kuma ya kasa Ranar Wuni yayi amai da zazzabi Tun kaka na Fada har ta dawo Lallashi Ahmed yana labe a kofar gidansu ya ga motocin da suka Dauki amarya da Danginta sun Wuce yana Sharan Hawaye yana jin Kewar Samiha na Mukurkusan Ranshi Tunda Ahmed ya rasa samiha Shikenan Rayuwarshi ta tsaya komai nashi yafara lalacewa Kaka na iya bakin Kokarinta ammh Duk a banza ya Rame ya lalace kamar bashi ba ganin Lalacewar na Ahmed na yawa ne yasa ta kira masa kawunsa Maude yazo ya sameshi yamai Fada Sosai Dalilin Hakane ma Ahmed yaji garin jega tamai kunci ya nemi yana so yabi kawunsa zuwa Kebbi domin ya zauna achan ita kanta Kaka batayi musu ba ta kyaleshi yabi kawu maude ko Zuciyarsa zata Huta haka ko akayi Ahmed ya Tattara yabi kawu maude Chan Birnin kebbi yana tayashi zama a shagon dayake zama na wani Alhaji ne,wanda yana kai mishi Ahmed din baiyi gaddama ba ya karbeshi suke zuwa tare suna Dawowa tare,lokaci bayan Lokaci yana zuwa Duba kaka in ya samu dama,shekara biyu ya kwashe a birnin kebbi wanda kuma yayi daidai da Shekara biyu da Rabuwarsa da Samiha bai kara jin labarinta ba,bai kuma kara ganin wani nata ba ammh ya Hadu da maimu acikin gari a birnin kebbi basuyi mgana ba ammh sun kalli juna cikin Halin ko in kula yana so ya mata mgana ko zaiji labarin Samiha ammh bai samu Fuska ba Shiyasa Shima bai mata mgana ba,ya wuce ta Wuce.
Ashekara ta uku ne suka Tattara suka koma kano da zama Domin Alhajin da Kawu maude ke zama mai a shago ne ya hada kawu maude da wani dan kasuwa Alhaji lere,Mutumin kirki da Arziki Kawu maude yayi wata biyar yana yawo tsakanin kano da Kebbi ganin haka yasa Alhaji leren ya siyamai dan madaidacin gida a kofar kaura yace ya Dauko iyalansa su dawo kusa dashi Cikin Murna kawu maude yazo yagayama kaka yakuma ce ta Shirya su koma tare batayi musu ba tattara komai nata tayi sallama da makota basu bar garin jega ba sai Da aka saida gidan da suke ciki suka karbi kudinsu,Ahmed yayima garin jega kallon Karshe yana Fatan Tunda ya rasa Samiha toh bayajin kuma garin jega zata kara Burgeshi acikin Rayuwarsa ba.
Koda suka koma Kano da Zama Ahmed bai daina Bin kawu kasuwa ba yana Taimakamai Kawu maude nacikin jin dadi Sosai da taimakamai da Ahmed yakeyi hakama Shikanshi Alhaji Lere yana yabon Ahmed din sosai,yaro mai Hankali da Natsuwa,sun shekara biyu suna aiki tare kafin Alhaji lere ya yaba da Hankali da kuma Natsuwar Ahmed ya Daukeshi ya kaishi wajen abokinsa Alhaji bashir wambai,bayan ya nemi yardan Kawu maude nan da nan ko ya amincemai koda Alhaji Bashir yaga Ahmed bai musa ba ya Karbeshi hannu bibbiyu zama na Farko da sukayi ya fara da jin Tarihin rayuwar Ahmed,shi kuma ya sanar dashi komai Alhaji Bashir ya Tsausayamai Sosai kuma nan da nan yaji yaron ya Shiga Ranshi bayan ya zaunar dashi yamai dukkan bayanan kasuwancinsa sai kuma ya Daukesa ya kaisa kasuwar kwari inda manyan Shagunansa suke da na kasuwar wambai da kuma manya Shopping mall dinsa Abun yazomai adaidai saboda Shima Ahmed Business education ya karanta,Ahmed ya fara aiki da Alhaji bashir amatsayin Manaja2 dinsa bayan Nura Babban Iman manaja1 kenan,Alhaji Bashir baiyi kasa agwiwa ba yace Ahmed ya kawo Takardunsa,yana kawomai kuwa ko Wata biyu ba"ayi ba ya samarmai gurbin karatu a jami"ar BUK aka bashi Level2 saboda Sakamakonsa yayi kyau sosai Business Admistartion yake Karanta zuwa Lokacin tuni Rayuwar Ahmed ta fara inganta kuma acikin iyalan Alhaji Bashir ba wanda bai sani ba sai Amaryansa wacce ke gombe da zama.
*Aisha alto..*
*Janafty*