Hs 15
by @legendspen
_Page 15_
Da ido suke kallonta, ita kuwa sai zuba take.
"Yanzu ba wannan Bhatool da kuka sani bace, ƙanwar Abdul, yanzu yayar Abdul ce. Ko yaya karima ma sama nake da ita."
"Bhatool. Bamu labari me ya faru?."
Suhaima da bata dade da ƙarasowa ba ta faɗa, gyara zama Bhatool tayi sannan ta ce.
"Ashe Abba, ba iya Yaran can yabawa amana ta ba?, can you girls remember that cold, giant, handsome and classy guy dake zama inda muke a garden?."
Ɗaga kai suka yi duka, tare da faɗin."Yes!." cike da mamaki.
"To shima Abba ya bashi amanata, jiya nan ya ajiyemun kudi. Ban dubasu ba sai yau naga 150k."
"150k!." suka fada gaba dayan su cike da mamaki.
"Yes, 150K." Bhatool ta maimaita.
"Bhatool, kina cikin Alheri dumu-dumu."
"Wallahi faa, and guest what?".
"What?!." Suka sake fada.
"Wai yana sona."
"Ayirrrrr, Bhatool tayi goshi." Jannah ta fada kamar tayi rawa.
"Amma kema kince kina sonsa ko?." Suhaima ta tambayeta.
"Haba mana gurls, atleast ai ya kamata naja Class ko yane."
"Eyh.. Amma kija a hankali." Jannah ta fada, sai kuma tace. "Dr Haisam fa?." Dariya Bhatool tayi sannan tace. "Wasa zanyi dashi, zance mai na aminci, amma ya jira mugama 100lvl mushiga 200. Sai ayi engagement da munje 300 sai ayi auren. Nasan shi wanan bazai fi six months ba, za'ayi komai a gama."
"Har bikin!?." Cewar Suhaima cike da mamaki.
"To mai zanjira Allah yakawo mun miji."
Dariya sukayi baki daya, daga nan suka shiga class.
*Senate*
07:45 yaƙaraso ƙofar gidan Yaya Karima, sai dai mai gadi yace mai tun 07 Ta fita. Komawa gida yayi rai babu dadi kwata-kwata. Har yanzu bai samu amsa daga wajenta ba, sannan yanaso yaji jiya akan wa take magana. Domin kasa bacci yayi gaba ɗaya, da tunanin maganar ya kwana. Bai san yana da kishi har haka ba.
"Good morning Momy nah." ya faɗa bayan ya shigo falon.
"Morning, angon Bhatool." Murmushi yayi sannan yace. "Momi har da ke."
"Ni dai yanzu zo ka zauna anan." zuwa yayi ya zauna, Momi ta kalleshi.
"Yanzu zuwa yaushe kakeso, a saka bikin nan. Sabida nima na matsu, duk ƙawayena sun fara aurar da yaransu. Har da masu jikoki."
Dariya Senate yayi, sannan yace."Momi nima bansani ba."
"Zan fara zuwa nayi magana da yayarta, sai asamu iyayenta."
*Bhatool*
"Haba Abdul, tunda nace kazo ina son ganinka ai kasan ganinka nakesonyi. Nifa yayarka ce." bhatool dake waya ta faɗa, shiru tayi Sannan ta ƙara cewa. "Idan kuɗi ne zance sai kazo, ai fada maka zanyi, ni yanzu turumun account number dinka na sama ko 10k ce dan kasan ni yanzu kuɗi basu bane matsala ta."
"Shikenan sai kazo." daga haka ta kashe wayar ta juyo ta kalli su Suhima tace. "Shi kadai ne Hope dina, sanan bani da wani wanda zai tsayamun daya wuce shi."
"Hakane Bhatool, sanan zai baki mafita sosai. Domin tabbas Dr Haisam ba karamin makirin mutum bane."
"Nasani wallahi Suhaima, kinaji yadda mukaji 'yan accounting dazu suna magana, kamar damu suke."
"Wallahi kiga dai yace zaki aureshi, to itama ƙawarsu yace zata aureshi. Mai hakan ke nufi." Jannah kuma ta faɗa.
"Alllah ya tsare mu baki daya, ni Abdul din ma idan yazo tare zamu tafi."
"Gwanda ki bishi Bhatool, wallahi banason ganinki a makarantar nan."
"Ke kuma da tsoro kike Jannah."
Ba'afi minti goma ba Abdul yazo makatantar, kiranta yayi a waya ya sanar da ita yazo. "jirani bakin gate." ta fada tare da kashe wayar. "Ladies yazo, sai munyi waya."
."Wait baki amshi cards dinki ba, banjin zan sake shigowa school." Suhaima ta fada tana bude jakarta.
"Ɗibi." ta fada tana miƙamata jakar. "Kala nawa ne." ta tambayeta. "Dinner, kamu, mothers eve. Su kadaine masu card, bridal babu, henna ma babu card."
"Okay, kowanne ban biyar, zanbawa senate da abokinsa, nabawa Yaya karima da mijinta sai abdul."
"Okay." Suhaima ta fada tana lissafa mata."Ga six nan ma ko zaki kara wani, ku nawa-nawa zan baku." ta tambayesu Jannah.
Bhatool dai amsa taita huce, sauri-sauri ta karasa bakim gate. Motar Abdul ta gani da sauri ta nufi motar tare da budewa ta shige a kan idon Senate da zuwansa kenan zai shiga Makarantar.
Ji yayi zuciyarsa ta harba da karfi, da sauri ya fara karanto addu'a yana Astagfirullah a zuciyarsa, yana gani ta shiga motar tana murmushi, gashi baya ganin ko waye ne dan tinted glass ne.
Numfashi ya sauke ganin motar ya bar gurin kafin a fili ya furta. " Bhatool!!." Yana dafe saitin zuciyarsa dake masa zafi.
Ta da motan yayi ya bar gurin a 360 ransa a bace, yana isowa get din unguwarsu yaga motar tana fita alamun ya ajiye ta ta shiga gidan Yaya Karima.
Har zai tare shi sai kuma ya fasa ya wuce ya nufi get din su, horn ya danna mai gadi ya bud'e masa, ya cinna hancin motar ciki yana parking, ya dade a ciki kafin ya furzar da iska yana fitowa ya nufi dakinsa direct.
~~~~~~~~
Ko da Abdul ya ajiye ta a kofar gidan Yaya Karima sai ta ce. " Abdul ga card na event din Suhaima, na Dinner, Kamu, nasan baza kazo Mothers eve ba."
" Abun naku har da mu ne?." Ya tambaya yana amsa tare da ajiyewa.
Hararansa tayi tana cewa. " Kai ka sani kuma, sannan idan zaka zo Hilis ka shigo da kudi na kari."
" Uhm naji fita zan koma kasuwa." Ya fada yana yiwa motar key.
Tabe baki tayi ta fita daga motan ta shiga gidan Yaya Karima shi kuma yaja motarsa ya wuce.
Da sallama ta shiga falon, Yaya Karima na amsawa dan tun dazu zaman jiranta take ta dawo taji ya suka kare da Lecturer din.
" Yaya Karima ya gida?." Bhatool ta fada zata wuce d'aki.
" Ke, tun dazu fa ke nake jira amma kinzo zaki wuce." Cewan Yaya Karima tana jin kamar ta kai mata duka.
Reverse tayi tana cewa. " Sorry Yayata ta kaina, me ya faru? Me kike jira?."
Hararanta tayi tare da fadin. " Ya kuka kare da Lecturer din naku?."
Dariya tayi tana fadin. " Ohh wai Dr Hashim? Ai wasan buya muka tayi dashi har na fito, nace zan same shi a office anjima shine na kira Abdul nace yazo ya dawo dani."
Ajiyar zuciya Yaya Karima ta sauke ta ce. " Alhamdulillah!!! Yanzu ina Abdul din?."
" Ya koma kasuwa abin shi."
" Baku da kirki dukan ku, tunda yazo har get ina laifin ya shigo mu gaisa yaci abinci." Ta fada ranta a bace.
Tabe baki Bhatool tayi ta nufi daki tana cewa. " To ki kirasa ki masa fada mana, amma kin wani sakani a gaba kinamin fada da rungumeman cikin naki...
Legends pen ***✍🏼