KADDARAR SOYAYYA

32

by @sheolly

💫KADDARAR SOYAYYA 💫
      
     By sheolly.
 


Da asubahin fari, bayan sun idar da sallar Asuba, Miemi da Khadija suka zauna a kan darduma suna karanta addu'o'in safiya. Shiru ya mamaye bedroom din, sai ƙarar tsuntsaye da ke tashi daga bishiyoyin cikin gidan.
Miemi ta sauke ajiyar zuciya, ta kalli Khadija da idanunta cike da damuwa.
"Yaya Khadija..." ta kira a hankali.
Khadija ta É—ago kai tana kallonta. "Na'am Miemi, me yake damunki?"
Miemi ta É—an yi shiru kafin ta ce, "Wallahi tun jiya dare zuciyata ba ta kwanta ba. Ina jin kamar akwai wani babban abu da zai faru. Ban san meye ba, amma zuciyata ta kasa samun nutsuwa."
Khadija ta matsa kusa da ita, ta kamo hannunta cikin tausayi.
"Miemi, ki daina sa wa ranki tunanin banza. Ki tuna cewa komai yana hannun Allah. Idan alheri ne, Allah Ya sauƙaƙa. Idan kuma jarabawa ce, Shi ne zai ba mu ƙarfin jurewa."
Miemi ta girgiza kai a hankali.
"Na sani Yaya, amma wannan karon abin ya bambanta. Kamar zuciyata tana sanar da ni cewa rayuwata za ta sauya."
Khadija ta yi murmushi mai cike da kwantar da hankali, sannan ta shafa kanta.
"Ki yawaita istigfari da addu'a. Kada ki bari shaiɗan ya saka miki tsoro. Allah ba Ya ƙaddara wa bawansa sai abin da yake alheri a gare shi."
Miemi ta yi murmushi kaÉ—an, duk da cewa har yanzu damuwar da ke cikin zuciyarta ba ta gushe gaba É—aya ba. Ta É—aga hannu suka yi addu'a tare,Bayan Khadija ta kwantar wa Miemi hankali, sai suka fita suka ci gaba da ayyukan gida kamar yadda suka saba. Kowacce tana gudanar da abin da ya rataya a kanta cikin nutsuwa.

Bayan sun gama, Khadija ta koma É—akinta domin yin shiri. Ta duba agogo, sai ta ga lokaci ya kusa.

"Oh no, I'm getting late for my lecture."

Ta yi sauri ta shirya, ta É—auki jakarta da kayan karatu.Miemi, I'm leaving now. My lecture starts by 8:30. I don't want to be late."

Miemi ta yi murmushi.

"Okay Yaya Khadija, have a nice day."

"Thank you, Miemi. khadija tafita zuwa harabar gidan, inda driver ya bude mata mota. suka nufi jami'a.

Bayan tafiyar Khadija, Miemi ta nufi ɗakin ƙaninsu Sadiq.

"Sadiq, wake up. It's time for school."Sadiq ya lulluɓe kansa da bargo.

"Please Aunty Miemi... five more minutes."

Miemi ta yi dariya.

"No way. Tashi yanzu, ko Daddy ya zo ya tashe ka."

Nan take Sadiq ya miƙe zaune.

"Okay... okay... I'm awake."

Miemi ta taimaka masa ya shirya cikin uniform ɗinsa, sannan suka sauko ƙasa.A lokacin ne Alhaji Umar Farouk da Hajiya suka riga suka zauna a dining table suna jiran yaran.

Bayan kowa ya zauna, aka fara cin abinci cikin annashiwa.Bayan kowa ya zauna, aka fara cin abinci cikin annashuwa.

Alhaji Umar ya É—an share makogwaronsa.Alhaji Umar ya kalli Sadiq.

"Sadiq, make sure you are ready. We will visit Alhaji Bashir's house soon."

"Okay Daddy."

"Abba, ni ma zan iya zuwa tare da ku mana."

Alhaji Umar Farouk ya kalle ta, amma kafin ya yi magana sai Hajiya ta ce da É—an tsawa,

"Miemi! Kin san kina da lessons É—inki. Ba za ki bar karatunki saboda tafiya ba."

Miemi ta yi shiru, ta sunkuyar da kanta.

"Okay Ammi."Ta amince da maganar mahaifiyarta, duk da cewa a zuciyarta tana son ta kasance tare da su.Bayan sun kammala breakfast, Abba ya kalli Sadiq yana murmushi.

"Sadiq, ka jira ni. Tunda mun gama tare, driver dina zai sauke ka a school kafin mu wuce office."

Da jin haka, sai Sadiq ya yi tsalle cikin farin ciki.

"Yawwa Daddy! Kai ne za ka je school dinmu yau?"

Ya faÉ—a cikin murna, yana kallon mahaifinsa da idanu cike da farin ciki.

Abba ya yi murmushi ya girgiza kai.

"Eh, zan raka ka yau."Bayan Abba ya shirya domin tafiya office, ya fito cikin kyakkyawan suit ɗinsa wanda ya ƙara masa kwarjini da kima.

Ammi ta matso kusa da shi, ta gyara masa zaman suit É—in cikin kulawa, kamar yadda ta saba yi.

"Allah Ya tsare ka, Ya dawo da kai lafiya. Allah Ya sanya albarka a duk abin da za ka yi."

Ta yi masa addu'a cikin soyayya.Miemi ma ta matso tana murmushi.

"Allah Ya kiyaye ka Abba."

Abba ya yi musu murmushi cikin farin ciki.

Sai ya kama hannun Sadiq, suka fita daga falon tare. Sadiq yana tafiya cikin farin ciki saboda yau mahaifinsa ne zai kai shi makaranta.