KURUCIYA

PAGE:1&2

by @xayyeesherthulhumaerath

Babbar makarantar ce, wacce kallo guda za kayi mata kasan cewa duk wani ɗalinbi dake cikin makarantar,to iyayensa masu hannu da shuni ne. Tsarin Makarantar irin tsarin makarantun turai ɗin nan ne, akwai ajujuwa da abun sanyaya jiki a ciki, da kuma Library haɗi da staff rooms, ga office na principal dana director. Dukkan wani abun ƙawa da ɗaukan idanu akwai shi musamman kurayen flowers na ƙarawa students ƙarfin gani. Kana ganin yanayin yadda ɗaliban suke farin ciki tare da rungume juna zaka gane cewa they have been so long kafin su haɗu,The school holidays are over.

Uniform na su black and white ne, mata ƙaramin skirt da riga sai white baby hijabi wanda aka zagaye fuskar da adon black, maza black ɗin wando da white ɗin riga sai black nicktie. 10:30 ya yi daidai da fitowar students ɗin daga cikin class ɗin su. Cikin nutsuwa yake tafiya yana bada faɗin, he's young yet handsome, easy on the eyes. Sumar kan shi har wuya he has a dark skin har sheƙi fatarshi take saboda baƙi. Kamar daga sama ya ji saukar muryar a kunnenshi an ce.

"Fool" "What fool?" Ya maimaita a zuciyarsa was abinda ya ji a kunnenshi, sai kawai ya share tare da yin gaba yana son ya ƙarasa wajan breakfast. Yana shiga cikin ɗan ƙaramin hall ɗin da aka tana da domin cin abincin students ya na jin kalmar “Fool" na yawo sama-sama a kunnenshi.

Yana shiga aka kwashe da dariya, ya ɗan ware manyan idanunsa like what wrong with them suke abu kamar mahaukata. Wata budurwa ta ce "hi fooled young man" Majeed ya dubeta ya ce "Who?" Budurwar ta ce "You, Majeed Abdul-Alim Beer" still kallonta ya ke ta sanya hannu a bayansa ta ciro wata small paper ta nuna masa ta ce "Jeed ka ce call me fool" da tsoro mamaki, al'ajabi ya kalli paper da aka rubuta.

“Call me fool" ma'ana kirani wawa ko shashasha. Nan da nan ƙwayar idanunsa ta sauya tare da kaɗawa tayi jaa ya juya da sauri ya ce.

"Fouk You, where's Rusul? Ina Rusul" Majeed Abdul-Alim Beer ya faɗa idanunsa har ruwa ne ke kwanciya a cikinsu sbd tsabar yadda ransa ya ɓaci, baya ƙaunar duk abinda zai taɓa masa daraja da ƙima duk da kasancewar shi ƙaramin yaro mai tashen ƙuruciya he's 18 yrs old gabaɗaya amma zafin zuciya gare shi, wannan dalilin ya sanya baya shiga sabgar kowa. "bana jin Rusul tana cikin nan fa class mate" cewar Sona wacce suke class ɗaya cikin makarantar. "Ban fiya gane haushi ba sometimes, musamman idan haushin ya yi kama dana karnuka" kyakkyawar yarinyar dake zaune tana breakfast ta faɗa Idanunta akan plate ɗin chips. A wani irin zafin nama Majeed ya juya kai tsaye kuma ya nufi inda take, kafin ya ƙarasa ta miƙe tsaye hannunta riƙe da spoon mai yatsu.

"Ni ke kaiwa haka? Am i your mate?" Majeed asked yana fiddo idanu waje. Rusul ta watsa hannunta baya irin shi ya sani ɗin nan ya ce "Hee black" Black sunan da take kiransa kenan ta ce. "Ai na faɗa maka ba zaka taɓa cin galaba akai na ba, sai dai muyi 50%, ko a gida sbd Big Dady nake saurara maka, wallahi na tsaneka kamar yadda na tsani mutuwata, ka sanya na fara tsanar sunan familynmu na BEER sbd kasancewar ka ɗaya daga cikin familyn" yadda take magana tana fito da manyan idanunta wanda suke iri ɗaya sak dana Majeed zai sanya ka ɗauka ita ɗin babbar mace bayan ko rufe 15yrs ba tayi ba.

Majeed yama kasa cewa komai sbd ta gama kunyata shi a cikin jama'a. Kamar ƙwayar idanunsa zata fito waje ya ce. "You!" Yama kasa magana sai kawai ya nufeta zata juya ta gudu ya sanya ƙafa ya kwarfeta kafin ta je ƙasa ya sa hannu ya ɗaga ta sama tare da yin waje da ita da hannu. Babu wanda bai san zafin zuciyar Majeed ba hakan yasa ba wanda ya bi bayansa. Sona ranta fes domin daman haushin Rusul take ji yadda take wa Majeed rashin kunya tamakar ba ƴan uwa ba abin ya ɓaci, babban dalili kuma wani irin mahaukacin so ta kewa Jeed ɗin irin son nan na ƘURUCIYA. "Wai kuma ƴan uwa ne haka? Ina mamakin wannan ƙiyayyar da suke wa juna, idanun Rusul har kusan makancewa ya yi sbd dukan da Majeed ya yi mata, sai da aka fitar da ita waje and the end ta ƙare sanya medical Glasses a Idanunta, wannan hauka da Shirman ya yi yawa" Khariyya ta faɗa tana kai bottle water bakinta. Tsaki Sona tayi ta ce "Mtwss yama kasheta mana, mene problem naki Khariyya? Taya zai zauna yarinyar ƴar mitsitsiyya tana raina shi she's just jss 2 banda ma tsayin ƙafa" Khariyya ta ce "Ke ai sbd kina son Jeed ya sa baki son Rusul, shi ma ɗin ai yaro ne duk ƙuruciya ke damunsu ina yanzu ya shiga Shekara 18 daidai sanda zamu je ss1?" Cikin sauri Farouk ya miƙe ya ce "heee ya isa akwai jarida fa, kuma wallahi mai zafi ce" Sona ta ƙarasa wajan Farouk tana dokan shoulder nasa ta ce "Haba big man, faɗa mana Please ka shaho kan Shaheederh ne?" Farouk ya juya Idanu ya ce "Ke dilla mu duk kwailar muka gani muna so dole ta kware mana, me akayi akai Shaheederh ko balaga ba tayi ba fa" gabaɗaya suka kwashe da wata mahaukaciyar dariya banda Musty da yake danna Wayarsa fuskarsa a haɗe.

"Ina wannan kwailar yarinyar Rusul?" Attention nasu ya koma kan Farouk daman Students da son jin gulma, bare kuma prvt shcl da kowa sha'aninsa yake babu mai ƙwaba. Cewa za kayi "African Queen, Rusul ta fi kowa kyau a shcl ɗin nan" In ji Noha.

Farouk ya watsa hannu ya ce "What ever, to wallahi Musty mugun son yarinyar nan yake, ga dai babies nan everywhere a makarantar nan amma ya maƙale sai Rusul, bana jin yarinyar nan ko period ta fara" Musty ya miƙe yana jan tsaki ya ce

"Sometimes ku mahaukata ne, bakwa gane soyayyar ƘURUCIYA data zahiri, soyayyar da na kewa Rusul true love nake mata, aurenta na ke son yi" suka kalli Musty da mamaki.

Majeed tunda ya ɗauki Rusul bai ajjiyeta ko'ina ba sai wajan garden na makarantar kai tsaye wajan wata bishiya ya nufa ya direta, Rusul ta murguɗa baki tare da riƙe ƙaramin ƙugunta ta ce "Mtwsss aikin banza kawai mutum yadda yake baƙi haka zuciyarsa take baƙi, haka zaka auri baƙar mace da ƴa ƴa baƙaƙe kuje can kuci kanku" ya buɗe Manyan idanunsa akanta tana ƙoƙarin magana taci ya buɗe rigarta tare da zura mata wani abu. Wani kalar ihu ta kurma tayi kansa ya ja da baya da sauri yana taɓe bakinsa wani ihu take tana ƙara nufarsa tare da cewa "Lizard, lizard Mom, Big Dady small Dad wayyo zai shige mini cikin wando na shiga uku" numfashinta ya fara yin sama idan akwai abinda ke firgitar da ita bai shige ƙadangare ba. Yaƙi cire mata ƙadangaren ya juya zai fita suka ci karo da Musty.

"Rusul" Musty ya kirata ganinta tayi baya tare da zubewa a ƙasa babu numfashi a jikinta. Yana ƙoƙarin taɓa ta Majeed ya ce "You guy, stop interrupt she's my biological sister" Musty ya ce

"And so what Majeed Abdul-Alim Beer? Idan sister naka ce mai yasa ka ke mata haka, banda kai ma lusari ne ka rasa dawa za kayi rigima sai da ƴar uwarka, mahaifinta yayan Dady naka ne uwa ɗaya Uba ɗaya" Jeed ya ja tsaki ya ce "ba kuma wanda na tsana a duniya sama da ita, da zan samu dama kasheta zan yi" yana faɗin haka ya yi gaba abinsa. Cikin sauri Almustapha ya ƙarasa wajan Rusul tare da ɗagota ya ɗan ɗaga rigarta sai ga ƙaton Jangwala gwada ya fasa kai yana ta huci, cikin fushi Musty ya yi cilli da Lizard ɗin tare da ɗaukan Rusul zuwa compound na makarantar time ɗin Jeed na zaune saman kujera wasu class mate ɗinsa mata suna tayi masa iyayi ba wacce ke gabansa Wayarsa yake dannawa. A bakin wani taf ya sanya fuskarta ta sauke ajjiyar zuciya tana kwaɓe fuska tare da sanya kukan shagwaɓa. Sai lokacin Musty ya sake ta ya ce

"Are you okay?" Ta buɗe ido sai ta ɗauke kanta Musty ya sassauta murya cikin rarrashi ya ce "Sorry, daina kukan Kinji beauty" ta ce "Uhm, to ka daina kallona" ya yi murmushi yana shafa suma tare da girgiza kansa ya ce. "Oh what kind of shagwaɓa" ta ɗauke ya zaro chocolate a jaka ya ce "Take this Rusul, na siyo miki" murmushi tayi tana girgiza kai ta ce "No thanks, Yaa Musty" ya buɗe Idanu was abinda ta ce "Me ya sa baki amsar gift idan na baki"

"Ina da komai, Big Dady yana siya mini komai, jiya ma Small Daddy ya kawo mini teddy ƙato" ya ce "Wannan ai ƙaramin abu ne" ta ce "Ni waya nake so" ya gwalo idanu ya ce "No please, gabaɗaya nawa kike? Kawai don kin ganki a secondary school? Ki bari zan baki waya da kaina amma idan kin zama babbar mace" yau ta ɗan yi hira da shi sama-sama. Ana tashi daga makarantar drivern su na zuwa, daman tuni An kira Big Dady director ya shaida masa everything daya faru tsakanin Rusul da Majeed.

A gajiye Majeed ya shige ƙaton part ɗinsa, idanunsa lumshe kansa na juyawa tsanar Rusul na ƙara yawa a zuciyarsa gabaɗaya duniyar tayi masa zafi. Rusul na zuwa ta lafke jikin Small Daddy mahaifin Majeed kenan ta dinga kuka tana gaya masa ƙarya da gaskiya ransa ya ɓaci sosai ya kira Big Dady mahaifin Rusul ya shaida masa komai. Washegari ya kama weekend ne Misalin 11 na safe Big Dady da Small Daddy suka shigo main parlour suna zabga ƙamshi lokacin Rusul na part ɗinta tayi kaca-kaca da parlourn tana wasan teddy bakinta duk abin chocolate, Majeed kuma yana can yana kallon Match. Big Dady ya kalli Mom ya ce "Riƙe kuɗin nan" ta amsa ta ce "Wannan kuɗin na mene?" Kai tsaye fuska a ɗaure ya ce "Sadakin ƴarki Rusul ne, an ɗaura mata aure yanzu, tare da ɗan uwanta daga yau Majeed matsayin miji yake a gareta, ko a yau zai ɗauki matarsa su bar mini gida.....

*** Urs Xayyeesherthuo [25/07, 9:41 am] Xayyeesherthul-humaerath🍂: *NOBLE WRITERS ASSOCIATION*

Aisha Sani Abdullahi *(Xayyeesherthul-humaerath)*

Bismillahir-Rahmanir-Rahim

اللَّهُمَّ أَنْتَ رَبِّي لاَ إِلَهَ إِلَّا أَنْتَ، خَلَقْتَنِي وَأَنَا عَبْدُكَ، وَأَنَا عَلَى عَهْدِكَ وَوَعْدِكَ مَا اسْتَطَعْتُ، أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ مَا صَنَعْتُ، أَبُوءُ لَكَ بِنِعْمَتِكَ عَلَيَّ، وَأَبُوءُ بِذَنْبِي فَاغْفِرْ لِي، فَإِنَّهُ لاَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ إِلَّا أَنْتَ.

Allâhumma anta rabbî, lâ ilâha illâ anta. Khalaqtanî wa anâ ’abduka, wa anâ ’alâ ’ahdika wa wa’dika mâ stata'tu. A’ûdhu bika min sharri mâ sana'tu. Abû'u laka bi-ni’matika ’alayya wa abû'u bi-dhanbî. Fa-ghfir lî fa-innahu lâ yaghfiru dh-dhunûba illâ ant. ★

*I'm Back Oh oh😻 zaman jira ya kare,ban dawo da wasa ba ku gyara zama,ku kara gyarawa domin tafiyar ta dabance kuma ta musamman ce,ka da ku bari a baku labari,Luv U Oll Fisabilillah♥️*