PAGE:3&4
Daidai da shigowar Ammie parlourn ke nan ta ji maganar Big Dady, a tare suka hada ido suna kallon Juna da Mom cike da mamaki tare da ruɗewa Mom ta ce , "Aure! Aure kuma fa Alhaji taya aure zai kasance ga wa innan yaran da ke tsantsar ƘURUCIYA ga wata irin kiyayya mara son bayyanarwa."
Kallo ɗaya Big Daddy ya mata ta kau da kai tare da yin shiru domin kuwa tasan a yanke hukunci babu mai ja,magana ɗaya yake babu canji.
Jinjina lamarin ta ci gaba da yi a zuciya, Ammie kuwa ba ta ce komai ta zauna. Sai a lokacin Small Dady ya yi gyaran murya "Wannan shi ne mafita kawai ga rayuwar Rusul da Majeed su kadai garemu a wannan dangin kuma sai Allah ya jarabcesu da rashin jituwa,And ba za su zauna mana a gidan nan ba kamar yadda aka daura auren nan yau to yau zasu bar gidannan su je can su karata inma kashe kansu za su yi , suyi amman mu dai mun gama namu, ya rage naku ku sanar da su zuwa nan da yamma ko dare su shirya zasu tafi gidansu."
Daga Mom har Ammie sai kallon kallo suna so suyi magana amman ba dama mussaman Mom tafi Ammie karfin hali. Tashi Mom ta yi tana fita ta nufi bangaren Majeed kiransa tayi kan cewa ya zo ya sameta a dakinta.
Zaune yake daga shi sai gajeren wando tashi ya yi ya jura jallabiya kawai ya bi bayanta don ya san tunda Mom ta kirasa da kanta babu shakka Rusul ta haɗa masa gwarama. Kwafa ya yi a zahiri yana fadin, "Wannan yarinyar ba,I will deal with her as soon as possible yadda ko name dina zatana gudun ji bare kuma tunanin taɓoni Allah sa ba Big Daddy bane yasa Momy ta kirani."
Da sallamarsa ya shiga Ciki yana, "Mom gani." Kallonsa tai ta ce " Ka saurareni da kyau, Dadynku sun yanke hukunci Haɗaku aure kai da 'Yar uwar ka Rusul."
"Mom,Aure! ni ? Ni kuma da waccer mahaukaciyar yarinyar? Ta ya ? Ta ina ma hakan zai yiwu Never! Karaf Rusul ta ce, "Ban gane ba,wace ce mahaukaciyar ma wai? And Wallahi ka fi kowa sanin ko da kudi aka bani kai bana so inda zai kasance ma na yi mafarkinka babu shakka a lokacin zan farka inyi sadaka na gwammace Idanuna su kame ba tare da rufewa ba har karshen numfashi maimakon in kwanta na yi gamo da mummunar fuskarka, da ko a aura mun kai na gwammace a kashe ni kowacce irin kisace kuwa." Wani zazzafan mari Majeed ya sake wa Rusul a fuska yana huci tare da fadin, "Mom kina gani ko? Ki fadawa Big Daddy ka da su aikata Babban kuskuren da zasu yi nadama." Daga hannu ita ma ta yi tana shirin marinsa. Da sauri Mom ta rike mata hannu tana, "Ahir dinki Rusul shi ne gaba da ke ba ke ce gaba da shi ba,kar ki kuskura." Cikin muryar kuka ta ce, "Don ya bani tazarar shekara uku sai yana mulkata? Meye marabar 15 da 18 wallahi ni dai ba zan bari amun in kyale ba batun aure kuwa sai dai wata ba dai ni ba,tir da wannan Bagidajen Black-Black din,ya zama mijina." Ta karasa maganar cikin sautin kuka tare da ficewa.
Mom ta dubi Majeed ta ce, "ka ga wannan zafin ran naka abu kadan duka shi ne babban matsalata da kai, Majeed kaine babba ya kamata ace kana hakuri tare da kai zuciya nesa, sannan kuma ka je ka shirya inji Dadynku zuwa dare ko yamma zaku tare a gidanku."
Wani irin ciwon kaine ya rufe Majeed cikin kankanin idanunsa suka kara fitowa waje tare da yin ja, gabadaya yanayinsa ya sauya,zuciyarsa zafi take masa kamar zata tsage, "At this Age? A mun aure? Kuma ma da wannan yarinyar? Me yasa Big Daddy zai mun haka?."
Haka ya tashi ya fita yana tafiya yana tangaɗi tamkar sabon makaho. Rusul kuwa gun Ammie ta je da gudu tana kuka, "Ammie kin ga Mom wai Majeed ne mijina? Ammie ni bana sonsa wallahi na tsanesa bana son zama da shi,ni ba shi nake so ba,Almustapha nake so ku aura mun shi, har chocolate yake siyamun kuma ya ce in munyi aure zai siya mun waya babba nima,uhumm umm."
Janta jiki Ammie tayi tana shafa mata baya a hankali tana fadin, "Stop crying wai kin manta cewa yanzu ke big gurl Daughter ce? And big never cry , kin ga wannan hukunci ne daga Big Daddy ba mu da damar hanawa ko bijirewa,So yanzu kin san me nake so da ke? Ki karbi wannan hukuncin da hannu bibbiyu kuma ka da ki taɓa karaya ko ki ce zaki yi kuka kan hakan duk wanda yama iyayen sa biyayya watarana zai ga ribar hakan."
Cuno baki ta yi tana share hawaye ta ce, "umm nama daina kuka akan wannan Black-black din bama zan kara yi ba,kuma ni ba matar shi ce ba."
Murmushi Ammie ta yi ta ce, "Yawwa Big gurl Daughter yanzu ki tafi Part dinki ki huta kiyi barci zanje gun Mom muyi wani aiki."
Ta shi tayi cikin shagwaba , "Ok byebye Ammie, Luv U."
"Byee,Luv U too,Take care." Ammie ta fada ita ma tana daga mata hannu.
Rusul na zuwa daki ta ci gaba da sabgarta ta manta ma da wani batun aure,shi kuwa Majeed na nan hankali tashe ya kasa samun sukuni.
Ammie da Mom ne suka hadu don tattaunawa yadda zasu tsara abubuwan tafiyan su Majeed don sun san ba tantama yadda mazan nasu suka tsara komai haka zai kasance su dai duka tausayin yaran suke da tsantsar ƘURUCIYA ke dawainiya da su,basu gama sanin kansu bama bare kuma rayuwar gidan aure.
Karfe 5:30pm sai ga small dady ya shigo cikin sauri yana fadin, "Ina Rusul din take? Maza ta fito yanzu zamu tafi."
Ammie ta tashi, "aiko tana barci baza abari su ci abincin dare ba kawai sai mu raka su duka?"
"Aa ki taso ta kawai, yanzu yanzu zamu tafi ba sai kunje ba,in kuna son ganinsu daga baya kwa je abinci kuwa akwai masu girki acen sa girka masu."
Haka kuwa Ammie ta taso Rusul kayan barci ne a jikinta barcin ma bai gama warwareta ba,ga dukkan alamu lokacin ya fara yi mata dadi.
Hijabi da takalmi Ammie ta mika mata ta karba tasa sannan ta rike mata hannu suka fita wajen Parking space.
Glasses din fuskarta ta gyara fuska fal mamaki cikin yanayin shagwaba ta ce, "Ammie ina za muje da su Small Dady da big Dady?"
"Gidanku za mu kaiku ke da Mijinki." Big Daddy ya fada fuska ba alamar wasa bare dariya. Majeed kuwa na tsaye ido a kade tamkar wani bugagge.
"Na ce to kayyakinsu fa ba za asa a motar bane?"Mom ta fada. Small Dady ya ce "Ba matsala an tanadar masu komai a wancen gidan, inma suna bukatar wasu abubuwan akai masu daga baya."
Kuka mai tsuma zuciya Rusul ta fara ta ma rasa meke yi mata dadi kamar a mafarki wai za kaita wani gidan abar gidan su kuma ma daga ita sai wancen Black-black din.
Haka suka shiga bayan mota duka su biyun ba yadda suka iya Small Dady ya na driving big Daddy na gefensa. Daidai wani tankararren gida suka tsaya wanda kana gani kasan ya ci kuɗin da bai bukatar furtawa a baki a bayyane yake.
Agefen jikin get din gidan ga alama nan mai tabbatar da cewa gidan mallakinsu ne wanda aka rubuta BEER'S FAMILY Mai gadine yazo ya bude masu da mamaki gidan ta ko ina ma'aikata sai shawagi suke, tamkar sun jima suna aiki ciki.
Securities ta ko ina don hatta mai gadin Uniform ne sanye jikinsa. Motar na tsayawa cikin sauri suka tawo suka tsaya tare yi masu maraba.
Big Daddy ya ce, "Wannan gidankune wanda za ku ci gaba da rayuwa ciki,akwai komai da zaku bukata inma ya kasance babu to akwai wanda zaina tambayar ku abubuwan da kukeso da zaran kun fada zai kawo, in kunso ku zauna lafiya ko kaunaci juna in kun ga dama kuma ku ci gaba da rayuwar da kuka saba yi a gabanmu wannan kuma ya rage naku."
Da haka su Dady suka tafi suka barsu a gidan ba yadda suka iya haka suka shige ciki,har cikin ransu ji suke tamkar su shaƙo junansu. "Mtsss, Allah sawake in zauna in haifi baƙaƙe masu baƙin hali."
Da sauri Majeed ya dago yana kare mata kallo. "Am i Your mate? Ko kin ga na kulaki ko na shiga harkarki? Dagani sai ke ai a cikin gidan nan ko wallahi sai in babbalaki yanzu nan."
Kara cuno baki tai tana share hawaye , "e na fada nidai wallahi God Forbid in zauna in haifi black black, dan yaro ma da kai me zan yi da kai tab wallahi ka mun yaro a mijin aure."
Saukar mari kawai ta fara ji ta hagu da dama cikin fushi ta kallesa ta juya da gudu fara leƙe leƙe tayi tana leƙa wani gu ta ga store shigewa ciki tayi tana neman abun da zata dauka aikuwa sai ga doya irin manya manyan nan. Daya ta dauka a hankali tana nishi ta fito cikin sanda
Majeed ya sunkuyar da kai kawai ya ji saukan abu a wuyansa,cikin firgici ya waigo yadda wuyan ya sara masa tamkar zai balle. Gwalo Rusul ta masa tana gudu tare da shigewa wani daki tana, "Mugu azzalumi na rama nima,ai wallahi ba za ka ci banza ba."
Sosai wuyansa ya kama yi masa ciwo ba shiri shima ya nemi daki ya shige ya yi alwala daidai sallar magrib ya yi da kyar sannan ya kwanta.
Rusul ma da taga lokacin sallah ya yi alwala ta dauro tayi ,ganin tarin teddies a dakin ya tabbatar mata da cewa nata ne bayan ta idar da sallah ta dauka tana ta wasa da su, a hankali dare ya fara tsalawa barci ya fara zuwa mata nan hankali ya fara tashi ta tuna bata iya barci ita kadai daman ta saba Ammie ce ke zuwa ta kwanta da ita har sai tayi nisa kafin ta tafi ga shi wannan gidan daga ita sai wancen mugun da bata son gani ma.
Ita kadai ta fara sambatunta , "zan rufe idona, in rungume Teddy na har barci ya daukeni ai nima zan iya." Aiko tana rufe ido sai ta razana ta farka cikin tsoro. Ta tashi ta zauna ga barci na kara shigarta dare ya yi sosai ciki. Ta rasa ya zata yi kawai ta fashe da kuka.
Barci take ji Sosai har idonta na rufewa amman babu dama ta kasa. Tana kuka Teddy rungume a hannu ta fito tana leken neman Majeed.
Wani daki ta hango yana kallon nata ta tura kofar a hankali Majeed ne kwance ya yi ruf da ciki daga shi sai gajeren wando don baya iya barci da kaya a jikinsa koda wasa.
Bude kofar da yaji anyi yasa shi gaggawan juyowa daman rufe ido kawai ya yi amman ya kasa barcin.
Jajayen kwalakwalan idanunsa ya zuba mata cikin dagon murya ya ce, "You.......
Ga masu bukatar COMPLETE DOCUMENT 500 ne kacal,just chat me up *** [25/07, 9:41 am] Xayyeesherthul-humaerath🍂: ♥️ *ƘURUCIYA* ♥️
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
Aisha Sani Abdullahi *(Xayyeesherthul-humaerath)*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim