PAGE:5&6
What brings you here?"
"Barci na ke ji kuma ba zan iya yi ni ɗaya ba."
Wani irin kallo Majeed ya watsa mata yana, "You Mean anan za ki kwanta wai? Ina tunanin hankalin kanki ya ɓace,common get out tun kafin in ballaki into pieces."
"Wallahi ni ba zan tafi ba anan zan kwanta barci nake ji na fada ma." Ta karasa maganar tana kokarin kwanciya akan gadon. Cikin zafin rai ya tashi. Cak ya dauketa tana wutsitsil, "Hey You Black-black ka barni inje inyi barci in ba haka ba... Ta karasa maganar tana gantsara masa cizo a wuya. Ajiyeta ya yi kofan dakin yana, "ke ga kwailanci ga mayyta to wallahi namana yafi karfinki Stupid sai ki kwana anan ai, Allah kawo lizard ma ya shige jikinki."
Dakin ya shige tare da sawa kofar key ya kwanta. Azabure Rusul ta tashi tana kuka fuska duk ta baci da hawaye tana bubbuga masa kofa ya bude,shi kuwa Earpiece ma yasa a kunnensa yana sauraren waka ya kwanta.
Zagayawa tayi ta baya gun window irin mai glass dinnan da ake iya dagawa ga shi da girma yanayin manyan gidaje dagawa tayi ta sakala kanta ciki ta dira sai ji ya yi kawai an haye kan gadon.
"Oh My God wai ke baki san ba abun da inanuna suka gudun gani ba fiye da ke?"Majeed ya fada.
Rusul ta ce, "nima ai ba son ganinka nake ba kafi kowa ma sanin hakan kaddara ce ta kawoni nan dakin kuma ka barni nayi barci in ba haka ba wallahi zansa a kira mun Small Dady in fada masa."
Tsaki ya ja ya rufe fuskarsa da filo ba yadda ya iya don yasan ta fadawa Dadynsa zai iya zuwa ya dakesa mussaman inta kitsa abun da akayi da wanda ba ayi ba.
Ita ma rufe kanta da filon tayi,kowanni na gefe kanta na karshen gado shi kuma kansa na farko haka har barci ya daukesu duka.
Nocking aka fara yi masu lokacin sallar asuba ya yi,Jeed na farkawa yaga jikinsu haɗe da juna. "Mtsss See this ugly girl." Bigeta ya yi har sai da ta faɗi daga kan gadon. Tana motsa ido doguwan da zatai ta gansa tsaye yana sa kaya.
"Aikin banza koma waye ya yarda ni kasa wallahi sai na rama,mugunta kawai, kuma Allah zai saka mun."
Ficewa ya yi ko a jikinsa ya nufi, ita ma dakinta ta koma tayi alwala tayi sallah sannan ta yi wanka, Uniform dinta ta gani an ajiye mata kan gado da komai da take bukata na tafiya school,shi ma Jeed kan ya dawo daga Masallaci ya tarar da komai hatta coffen da suka saba sha kafin su tafi ,shi kawai suke sha sai sunje School suke breakfast 10 na safe, sun gama shiryawa duka a tare suka fito parlourn sai ga wata ta shigo ita ma sanye da Uniform wanda yake tabbatar da cewa daya ce daga cikin ma'aikatan da aka ajiye a gidan.
Durkusawa tayi ta gaishe su tare da tambayar ko da abun da suke da bukata. Rusul ce kawai ta iya amsa mata da Nop shi ko Majeed wayar da ke hannun sa yake dannawa hankali kwance cikin kasaita.
Rusul ta kallesa tana taɓe baki, "Mutum yaro da shi sai girman kan jaraba mai girman kai dai kam wuta zai shiga anji kunya."
Ya dago kenan sai ga wani Namiji ya shigo wanda duka sun san shi daman drivern da ke kaisu school ne. Ba tare da magana ba kawai suka bi bayansa. Majeed ya fara budewa kofa ya shiga sannan Rusul a tare duka suka yi tsaki suna kau da idanu wajen kallon juna.
Majeed ya ce, "Eheen Let me Warn You first, kar ki kuskura inji wata magana mai kama da aure na yawo cikin School in kuma hakan ya kasance kin fi kowa sanin me zai faru."
Da sauri ta juyo tana masa kallo irin na takaici mai bayyanar da kiyayya ta ce, "Allah sutura in ce an aura mun kai,ni ko maza sun kara a duniyar nan na gwammace in rayu ba mijin auren ma da ka zama mijina,inje in haifi yara bakake ga bakin fata ga bakin hali in sun fita ana gudun su Allah tsare gatari da saran shuka."
Kallonta ya yi sama da kasa yana
"Ni Jeed, me zan yi da kwaila? Dubi ƙirji bashi da mara ba da nawa, ko a haka ake haihuwa ni wallahi an gama cutar da rayuwa ta, how am going to life da wannan mitsilar."
Sai da yasa ta kalli kirjinta ta cuno baki irin like abun ya taɓa mata zuciya sosai anci mata mutunci a kan kirji.
Kwafa tayi kawai a zuciyarta tana saƙa yadda zata rama ita ma.
Har driver ya sauke su a school ba wanda ya kara magana a motar kowa sauri yake kawai ya bar motar.
Majeed Abdul-Alim Beer tafiya yake tamkar bai so taka kasa har ya isa cikin Class dinsu.
Rusul kuwa fuskar nan babu walwala sam kallo ɗaya zaka mata ka fahimci cewa ranta a ɓace yake.
Ba wanda ta kula har ta shiga class ta zauna sai can Nisher ta kalleta ta ce "Rusul What's Wrong with you tunda kika zo kin ki kula kowa kuma ranki a ɓaci fuskar ma na nuwa like u want to cry."
Zuciya a fusace kamar za ta yi kuka ta ce "Nisher wai ni Majeed ke tsokana kwaila ban da Nono a kirji? Wai har yana ce mun kirjina bai da Maraba da na shi? I can't take this." Ta karasa tana daga glass din fuskar ta tare da goge hawayen da ke shirin zubo mata.
Dariya Nisher tayi ta ce, "Common har kin bani kunya , kalli kirjina ko matan Ss3 basu isa su nuna mun ba, ke ma in kina so naki zai zama haka kila ma har ya fi nawa."
Da sauri Rusul ta dafeta , "Are You Serious Nisher? Ina bukata da gaske fa ina so in nunawa Jeed bambanci tsakanin kirjina da na shi."
"Eheen akwai wani cream da Mom dina take shafawa,shi nake diba nima in shafa bata sani ba,Anty Hameeda ce ke kawo mata kuma jiya ma na ji suna waya yau zata zo gidanmu." Nisher ta fada.
Ajiyar zuciya Rusul ta yi ta ce, "ki taimaka ki samo mun nima Please Nisher."
Nisher ta ce, "kar ki damu bara na koma gida dai."
Sai a lokacin Rusul ta dan sake. Lokacin breakfast na yi suka nufi hall suna zuwa sai da ta daidaici inda ta san Jeed ya saba zama ta canja kujerar da wata wacce ta karye ba tare da ta bari an ganta ba, sannan ta koma ta zauna suka fara breakfast da Nisher.
Kowa ya shigo hall din tsit ka ke ji ban da sautin plate da spons ba abun da ke tashi. Kamar kullum sai a lokacin Majeed ya shigo hall din. Sona ce ta fara magana, "Good Morning Jeed."
Ba tare da ya dago ba bare ya kalleta ya amsa ciki ciki , "Morning."
Dariya Noha da su khairy suka fara suna, "That's Good maganin mai naci irinki kenan."
Sona ta ce, "Mtss ku ya dama tunda dai ya amsa ai shikenan."
Yana zuwa zaman da zaiyi kawai sai jinsa sukai a kasa tim idon kowa ya dawo kansa.
Tsabar takaici da kunya kasa motsawa ya yi na kusan Minti guda,tuni idanun nan sunyi ja yanayinsa ya canja.
Dariya suke suna kunshe baki, Rusul kuwa karaf ta ce, "Ah Big Boy anji kasa ,So sai a tattara taburmar kunya a tashi ko?"
Ta karasa maganar tana dariya tare da ficewa a hall din.
Da karfin Hali Sona ta karasa garasa tana mika masa hannu, "Sorry Class Mate,ina ga ba a lura da karyewan chair din bane."
Tashi ya yi kawai a fusace ya fice har yana shirin bangajeta. Yana fita kuwa hall ya dau sautin dariya.
Breakfast din da baiyi ba kenan.
Zuciyarsa har suya take masa domin ya tabbatar da ba mai yi masa wannan aikin sai Rusul yanzu kullum sai ta yi abun da zai disgasa a cikin makaranta, "ba zai yu ba,i most teach her a lesson wannan kwailar yarinyar na tsaneta na tsaneta wallahi." Shi kadai yake magana tamkar zautacce.
Zaune take a garden tana shan iska ban da dariya ba abun da take kyalkyalawa hankalinta ya kwanta ta rama abun da Ya mata. Ji tayi an rufe mata idanu ta baya cikin shagwaba ta ce, "Nisher Stop this i don't like it at all?"
Gyaran Murya Al-Mustapha ya yi ba tare da ya ce komai ba. Murmushi ne ya bayyana a fuskarta ta ce, " umm ummm Al-Mustapha."
Sai a lokacin ya cire hannayensa ya zauna daf da ita yana , "wato baki ganni a breakfast hall ba kuma ba za ki neme ni ba? Anya kuwa kina tausayina Rusul?"
Cikin shagwaba ta ce, "Umm to ni na manta ne kuma ina tausayinka ai."
"Really?" Almustapha said
Girgiza masa kai ta yi cikin sigar shagwaba alamun eh.
"Alright, Take this saura yau ma kice kin ƙoshi shawarma ne ba chocolate ba."
Rusul ta ce, "To nidai saidai ka bani a baki." Ta karasa magana tana cuno bakin.
Dariya ya yi, "to shikenan bude bakin." Bude bakin ta yi yana bata suna hira har ta cinye tas.
Zasu koma Class har ta tafi ya kwalla mata kira , "My African Queen can't say Anything?"
Rufe fuska tayi da hannu a cikin shagwaba ta ce, "I love you." Tana fada ta tafi class da gudu.
Wani irin sanyi Musty ya ji har cikin ransa a zahiri ya furta , "I so Much Luv this girl And kuma sai na mallaketa In Sha Allah."
Farouk ne ya zo yana dafa kafadarsa, "kai dalla an shiga class kana nan kana wani shirmen Murmushi mene ne haka ko dai ka fara zaucewa ne."
"Ina nan ina gina soyayyata ne kai wallahi ina son yarinyar nan Over ."
Tsaki Farouk ya yi yana, "Daman akan waccer kwailar ka zauna anan Lallai ka fara zaucewa ni kazo mu tafi."
"What Ever ni dai ina son abata kaima haushin rashine kawai kuma karka kara ce mata kwaila call her name Rusul ko kuma ka yi shiru."
Dariya Farouk ya yi yana, "Allah sawake in so wannan yarinyar babu cikakken gaba bare baya wannan ma me zan samu a jikinta da har zan ji dadi? Asalin kwaila ce wallahi sai dai tsayi da saurin girma kawai amman ba kayan aiki,wannan ni ko kiss ta mun bazan ji komai ba ai."
Tuni Ran Musty ya baci,cikin Fushi ya ce, "Kai bana son wannan iskancin kuma ya isa haka ai gwanda ma ta zauna haka da irin ku Mayun mata suna kalle mata sura."
Dariya kawai Farouk ya yi ganin yadda kicin-kicin Musty yake nuna bacin rai don an taɓa Rusul.
Majeed kuwa yana class rai ɓace ana karatu amman wayarsa yake dannawa.
Lokacin tashi nayi driver yazo daukansu da sauri Rusul ta shige gaba don ta san ta shiga baya yadda idanun Jeed sukai tsaf zai iya yi mata komai.
Kwafa ya yi kawai ita ko sai dariya take tana waƙokinta.
Suna isa gida ma ita ta fara barin motar da gudu zata shige ciki daidai bakin kofa ji tayi an hamɓareta kawai ta bige sai da bakinta ya fashe.
Kuka ta fara ganin yadda jini ya biyo hannunta ta shige da gudu, ɗaya daga cikin ma'aikatan gidanne tazo da sauri ta taimaka mata ta wanke.
Shi kuwa sai a lokacin zuciyar sa tayi sanyi ya yi wani irin murmushin takaici sannan ya shige ɗakinsa.
Ana gama wanke mata don azaba take tayi barci agun ko sallah ba tayi ba bare ta ci abinci.
★★★
Nisher na komawa gida tayi wanka sannan tai sallah, abinci ta dauko sannan ta dawo parlourn momynta ta zauna ai kuwa ta tarar da Anty Hameeda ta zo sunata hira.
Ta gaishe su sannan ta zauna ta ci gaba da cin abincinta.
Hameeda ta ce, 'kin ga wannan Great Curves din ya fi wancen breast enlargement cream din aiki wannan kankant ne ba iya kara girman breat din yake ba hatta kyau da fidda masa shap yana yi ki zama tamkar sabuwar budurwa ke tsaya ma am Telling you sai kin fi wata budurwar ina da 💯 sure akan wannan ke dai ki gwada kawai za ki ga yadda abu zasu kara bayyana su tsaya su firfito Sister sai kin rasa gane kan Dadyn Nisher."
Mika mata hannu tayi suka tafa Momyn Nisher ta ce, "kin ga shiyasa nake ji dake over komai na karuwa da kin samu sai kin nemeni yanzu ki mun bayani ya ake amfani da shi ko kamar wancen ne dai?"
Hameeda ta ce, "kin san wannan fa takanas nayi mana Ordern sa guda hudu kowa bibbiyu , za ana shafawa da safe da kuma dare in za a kwanta barci,amman kuma ki tabbatar kin wanke breast ba wani datti kafin ki shafa za asha mamaki kawata."
Shewa suka kara yi suna tafawa,ita kuwa Nisher tsuru tana binsu da ido tare da kallon bakin duk mai magana cikin su tana recording komai.
Mika mata kwali biyun Momynta tayi ta ce, "Oya Nisher take this,ki ajiye mun cikin warddrope na gefe da nake ajiya."
Karfa tayi taje ta ajiye mata ɗaya aciki ɗayan kuma ta koma dakinta tasa a jakarta na School sannan ta dawo ta zauna cikin su tana jin dukkanin abubuwan da suke tattaunawa kai duk dai wani abu da ya shafi kari na rayuwar mace,harda maganin cikowar gaba,ko a jikinsu da tunanin cewa wai tana gun.
★★★ Kamar a mafarki taji bakinta na yi mata nauyi ga kiran sallah dake shiga kunnenta.
A hankali ta bude ido ta mika hannunta kan bedside ta dauko glass tasa sannan ta tashi a hankali.
Karasawa tai gaban mirror don yadda take jin nauyi a fuskarta. Abun da ta gani yasata wata gigitacciyar kara tana kuka.
Bakinta ne ya kumbura suntum tamkar Balloon kamanninta ya sauya gabadaya tayi wani irin muni.
Cikin sauri ma'aikatan gidan suka nufa dakin. Jeed kuwa na zaune a falo ko ajikinsa tamkar ma bai san meke faruwa ba.
Suna yi mata magana ta share su ta fito tana kuka.
"Wallahi sai na fadawa small Daddy da big Daddy, Ammie da Mom ji yadda ka maida mun baki? Mugu azzalumi mai kama da agwagwa."
Sai a lokacin Jeed ya dago ya na kallonta.
Me zaiyi ban da dariya. Rike ciki ya yi har yana kokarin tuntsirewa.
Rusul kuwa....
COMPLETE DOCUMENT 500
*** Urs Xayyeesherthuo [25/07, 9:41 am] Xayyeesherthul-humaerath🍂: ♥️ *ƘURUCIYA* ♥️
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
Aisha Sani Abdullahi *(Xayyeesherthul-humaerath)*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim