PAGE:7&8
Wani irin takaici takara yana shigarta ga kumburarran baki ga Jeed yasata agaba sai dariya tamkar ya ga mahaukaciya.
"Ni ba mahaukaciya ce ba ka daina mun dariya kuma ba zan kyale ba kasani Dan karamin yaro kawai Mummuna baki da kai kamar na a kuya."
Cikin dariya ya kara kallonta yana, "Au da kumburarran bakin ma ba za ki iya yin shiru ba ko? Ga fatar bakin nan tana shirin tsagewa ai,inya rabe duka mu ga bakin tsiwa Kwailar kwailo."
Yana cewa bakinta ya kusa rabewa ta kara firgita tana kuka, "bakina ba zai rabe ba sai dai naka mugu kawai mai kama da jaɓa."
Murmushin mugunta ya yi kawai ya fice daga falon, ita kuwa tana kuka haka tayi sallah ko abinci ba ta iya ci ba sai tea ta sha ta je dakinsa ta kwanta.
Sai da ya tabbatar tayi barci ya dawo yana dariyar mugunta dauke da jaɓa a kwali ,cirowa ya yi, a daidai kan fuskarta ya ajiye mata,kamar a mafarki ta ji abu a fuska sa hannun da za ta yi kawai ta damƙo katotuwar jaɓa.
"Thi....sss." ta furta muryarta na rawa kawai ta tsala ihu tana tsalle jaɓar ta sauka kan gadon.
Jeed ko a jikinsa daukan jaɓar ya yi yana kokarin maida mata jikinta ya janyota yana jan gabar rigarta zai sa,"ba ni kike cewa jaɓa ba,gata nan ai na kawo miki ita." , tsabar rikicewa agun Rusul ta sake fitsarin wahala ga zufa ta ko ina keto mata yake, "Ammie, Small Daddy Majeed zai kasheni zai kasheni ,na shiga uku zan mutu."
Ita kanta jabar da ta ji wahala neman hanyar gudu take, yana tusa kanta jikin Rigar Rusul ta yi tsalle ta fada kasa, da gudu ta fice adakin.
"God Save You amman da yau sai kin kwana da jabar nan karshen rashin kunyarki kenan, kazamiya kawai ki fitar mun da kayan fitsarin nan adaki ."
A jiyar zuciya Rusul ta yi tana murguda baki , "Ni dai ba kazamiya bace,kuma Allah ai ba azzalumin bawansa bane , Message back to sender."
Wandon jikinta kawai ta cire ta wurga ta window ,don tsoron fita take kada ta ci karo da jabar,tana murgawa ta koma kan gadon ta kwanta. Wata irin tsawa Majeed ya mata yana, "ke wai ba zaki fitanmun adaki bane? Ko sai na jakine,"
"Ba zan fita ba anan zan kwana nace."
Fara ja mata kafa ya yi,ta rike jikin gadon gam tana, "koma me zaka yi sai dai kawai."
Duk yadda Majeed ya so korar Rusul a dakin nan sai da ya gaji ya hakura haka suka kwana tare.
Da asuba ita ta fara tashi tana jin ana masu Nocking ta nufi dakinta shi ma ya tashi.
Duka sun shirya kan lokaci kamar kullum Rusul kumburan baki ya ragu amman har yanzu da Saura hakan yasa ta dauki facemask ta maka gudun kar aga bakinta a mata dariya a school.
Suna haɗa ido ya cije gefen bakinsa ta yi tsaki ta kau da kai shi ma ya kautar.
Yau ma gaba ta zauna shi yana baya ba wanda ya ce ko ƙala har suka isa School din.
Sai da Majeed ya bari an taru kowa da kowa ana assembly tun kun ya tsira duba Yan matan da sukai Makeup yana cikin Masu Despiline amman bai taba duban komai ba sai ranar don kawai yasan akwai abun da ya taka.
Rusul ya fara kira gaban assembly yana, "Remove this." Yana nuna mata facemask din dake fuskarta da hannu.
Cikin tsiwa ta ce, "I can't , ni ban yi kwalliya ba kuma ai da na yi kwalliya za aga alamar a fuskata ba sai na cire ba."
Cikin tsawa ya kara fada, "I said You should remove it."
Almustapha ne ya karaso cikin zafin rai, "wai ke me yake damunka ne? Takurarka ga yarinyar nan ya yi yawa fa don ka ga kawai ana kyaleka? And ka fi kowa sanin cewa Ko Lipstick Rusul bata sawa bare ya kai ga Makeup."
Nuna masa hannu ya yi alamar dakatarwa, "sau nawa zan ce ma ka bar shiga harkata ,ka da ka kuskura ba ruwanka dani sannan kuma facemask dole ta ciresa gaban kowa anan wajen."
Janyota ya yi ya fisge facemask din da karfi.
Ban da hawaye ba abun da ke zuba a idanun Rusul sunkuyar da kanta kasa ta yi ba tare da ta dago ba. Shi ko yana cire mata ya ja tsaki yana huci kamar saniya ya bar wajen. Rike mata hannu Al-Mustapha ya yi mussaman da ya lura student sun fara kanun maganganu akan bakinta.
Suna ja gefe ta rungumesa tana kuka , "Sai na rama,ba zan kyale ba sai na rama ." Kuka take sosai har tana shidewa.
Dagota Al-Mustapha ya yi ya ce, "Sorry Dear, Stop crying please! Ko kina so nima na yi ne?" Girgiza kai tayi alamar Aa ta kara da cewa, "Shi fa ya fasa mun baki kuma ya bude mun gaban kowa aka gani ana mun dariya,nima sai na rama abun da ya mun kuma sai ya yi kuka kamar yadda na yi."
"Alright yanzu ki yi shiru dai zan baki wani facemask din kuma na miki promise zan rama miki da kaina kinji?" Ya karasa fada yana goge mata hawayen.
Rusul ta ce, "da gaske?"
"Yep da gaske nake zaki gani yanzu kiyi murmushi kin san in kika bata rai kyanki raguwa yake kuma ni fa bakinki ma kyau yamun yanzu ba muni ba,kyan ki na nan a ko ina kikaje zaki amsa sunan African Queen ." Musty ya fada.
Murmushi ta yi wanda ya bayyanar da jin dadinta a zahiri.
Sai da ya rakata har Wajen class dinsu yana rarrashinta sannan ya ce "Byee byee, take care Luv U."
Ita ma daga hannu ta yi tana, "Byee Luv U Too." Cikin kunya sannan ta shige aji.
Tana shiga Nisher ta mika mata wata Roba ta ce, "Oya take it,ki boye a jaka ai jiya ina zuwa na tarar Anty Hameeda ta zo,na ji tana cewa Mom wannan ma yafi wancen kyau da aiki, za dai mu gwada mu gani,za kina shafawa da safe da kuma dare kan ki kwanta,ai dauke mana daya nayi na diban miki na boye sauran kin ga daga yanzu ba mai kara ce miki kwaila."
Washa baki Rusul ta yi ta ce, "Yawwa Thank You So Much Nisher sai na bawa Majeed mamaki zai ga bambamci tsakanin kirjinsa da nawa,ke in suka fito ko daina kananun kaya kawai zan dunga sawa a gida ina yawo da su yana gani wallahi ke har gabansa zanna zuwa girgiza masa su yasan cewa am better than kwaila sai na fi duk matan nan da suke binsa mussaman wannan Sonan ita fa har tafiya take tana girgiza kirji gasu kananu kamar cokali."
Dariya Nisher ta yi,"ke dai bari kawai ni har irin kayan da Mom ke sawa nake sawa nima yanzu a gida,ke na manta ban fada miki ba fa na ji suna maganar wani abu wai da yake sa cikowar gaba,ban dai gama fahimta ba amman inna gane zan dauko mana shi ma mu gwada."
Rusul ta ce, "Yes kice muma zamu zama manyan mata." Tafawa suka yi duka suna dariya.
Gyaran muryan da suka ji ana yi yasa su saurin gyara zama tare da ankarewq ashe har teacher ya shigo basu sani ba.
★★★ Mom da Ammie zaune a falo suna hutawa kowacce dauke da waya a hannunta.
Ammie ce ta fara dagowa ta ce, "gidan ba dadi wallahi i so Much miss my rigima daughter."
Ajiyar numfashi Mom ta yi ta ce, "hmm ni babbar matsalata ma kada yaran nan suje su illata kansu duk da ance akwai enaugh securities amman sam hankali na bai kwanta da zaman su su kadai ba,ga shi jiya na yi magana kan muje mu gansu ya ce aa nikam dai zan kira Majeed inji ya suke ko hankalina zai kwanta."
Ammie ta ce, "Sun fi mu tunani sun fi sanin me suka hanga muta hakuri kawai muna bin Yaran nan da addu'a Allah hada kansu ya kauda kiyayya kuma ya dasa masu kaunar juna a zuciya shine fatanmu kawai."
"Hakane kam Allah ya tabbatar da Alkairi amman zan kira Majeed gobe tunda na san basa da School in sha Allah inji ya zamansun yake." Mom ta fada.
★★★Weekend ne ba School Don haka Rusul na sallah kafin Majeed ya dawo daga Masallaci ta kara shemewa kan gado bilhakki tana barci cikin jin dadi gabadaya gashin kanta ya rufe mata fuska sai sheƙi yake.
Rigar shi ya dauka ya jefa mata tsam ta mike a tsoroce tana, "Wayyo Allahna na shiga uku."
Sai da ta sa glass ta gane ashe riga ya jefa mata yana dariya. Tsaki tayi ta na, "ban shiga harkar wani ba ni ka barni in kwanta."
Majeed ya ce, "baki isa ki kuma mun wani barci adaki ba sai dai ki koma naki in kika ki kuwa saidai kuyi barcin ke da jaɓa cikin jikinki."
Tashi tayi tana cuno baki. "An fita din an fita ka cinye dakin Black-black kawai, ban san ya zan furta ma adadi da kimanta yadda na tsaneka na tsani ganinka ba a rayuwata."
Bin bayanta ya yi ya cafkota tare da rike mata fuska daidai wajen baki da hannunsa ya ce, "What? Wai ke har yanzu tunanin ki ya kasa bayyanar miki da gaskiyar cewa na tsaneki fiye da tunaninki ne? My hate for you is undying,and it will never Pause,When i says i hate you,I really mean it. I regret every single moment i spent with you,ke kima sa aranki watarana ni zan zama ajalinki."
Ya sake ta cikin fushi yana kokarin shigewa daki.
Cikin tsiwa ita ma ta ce, "sai dai mu zama ajalin juna,ni ci gaba ganinka ma kadai zai iya sawa zuciyata ta buga wallahi i hate you with all my life babban takaicin ma da ka kasance daya cikin Dangina, Tir."
Dakinta ta shige tayi wanka tana fitowa kafin tasa komai breast enlargement cream ta fara daukowa ta cire towel tana shafawa tana fadin, "sai na bawa wannan yaron mamaki ya kasa gane ni wace ce ko? Indai kirjini yaro Nono zai fito kuma za ka gani ganin idonka daga nan na ga bakin kara ce mun kwaila da har zaka hada kirjina da naga kana nan da wani fadadden kirji a kwance kamar katafa Yaro kawai."
Haka ta dunga sambatunta har ta gama shafawa sannan tasa kaya Teddynta guda daya ta dauka ta goya sannan ta rike ɗaya a hannu ta fita parlour don yin breakfast.
Ganinsa da tayi a dining area ne yasa ta ja tsaki a zahiri tana, "Mutum sai shegen kallon jaraba."
Ko kallonta bai yi ba amman tsabar shirme atunaninta daga sa mai har kirji ya fara fitowa shiyasa ta fada haka don ya dago ya kalleta shi kuwa ko gezau cin abincinsa yake tamkar bai ma san da ita ba. Kitchen ta nufa tana mita. "Ni azuba mun wani abincin don tunda wancen bakin yaje ya fara cin wancen na koshi."
Haka kuwq tasa aka zuba mata wani,ta fito parlourn tare da daura kafa daya kan daya tana ci.
Wayar Majeed ce ta fara kara yana dubawa kuwa ya ga number Mom. Da sauri ya amsa, "Morning Mom Wai Don Allah Big Daddy ba zai ce in dawo gida bane ni na gaji da zaman nan kamar prison duk rashin sona da ake ai ba sai an hadani da waccer yarinyar ba."
"Har yanzu dai wato baku bar halin ba anan ma ba? Ni ka mun shiru ma na kira inji ko kuna lafiya fatan ba komai dai ko?"
Rai bace Majeed ya ce, "Ina lafiya."
"Rusul fa? Ta na nan tana ma rashin kunyar nan ko?"
Shiru ya yi kawai Mom ta kara da , "Alright bani ita mu yi magana."
A jiye wayar ya yi kawai kan dining din ba tare da ya ko dago ba.
"Rusul, Rusul kina jina?"
Tana daga zaune can cikin dagon murya ta ce, "Yes Mom ina lafiya ni bazan taba wayar wancen bakin ba nima in zama bakar fata,ki fadawa Small Dady ya zo ya daukeni kuma ya siyomun breziya kirjina ya fara girma zanna tarewa."
Sai a lokacin Majeed ya dago ya kalleta yana sakin wata gigitacciyar dariyar mugunta.
Ita kanta Mom sai da abun ya bata dariya ajiyar zuciya ta yi kawai ta ce, "Allah ya shiryaku dai."
Majeed ya ce, "Wata kam ai saidai ta ga Nono a kirjin wasu ba dai nata ba, ina aka ga surar ma da miji zai so? Duk wanda za aba wannan ai an kashesa gwanda wani namijin ma da ke."
Ganin shirmen na shirin yin yawa yasa Mom katse wayar kawai tana kara maimaita, "Yaran nan dai ba za su girma ba."
Cuno bakin nan tayi ta aje plate din abinci gefe tana rike karamin Kwankwasonta, "nan gani nan bari takalmin kaza wallahi kuma ka tsaya ka ga yadda kirjina zai cika nan da wani lokaci sai dai ana leƙe daga nesa." Ta ƙarasa maganar tana cire ribom din da ke kanta gashin ta ya zazzago har kafaɗa. Ta kara juyawa , Ruwan kyau,farar fata ,bakin gashi So Ma Sha Allah Beauty is all around me?
Tashi Majeed ya yi yana ƙoƙarin damkota.
Aikuwa da gudu ta fice waje.
Kitchen ya nufa ya dauko scissors sannan ya bi bayanta.
COMPLETE DOCUMENT 500 *** [26/07, 1:36 pm] Xayyeesherthul-humaerath🍂: ♥️ *ƘURUCIYA* ♥️
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
Aisha Sani Abdullahi *(Xayyeesherthul-humaerath)*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim