PAGE:11&12
Dagowa ya yi zuru yana kallonsu wani irin gigitaccen mari Small Dady ya sake masa a fuska sai da shatan hannu ya fito Ammie ta janye Rusul cikin sauri ta kwantar kan gado.
Dr Habeeb ne ya shigo cikin sauri,Shine Family Dr din BEER'S FAMILY gabadaya mussaman Rusul da ta saba samun matsaloli agun Majeed.
Duka Small Dady ya fara yiwa Majeed tamkar dan karamin yaro , cikin zafin rai Big Daddy ya ce, "miye haka? Ka bari Abdul-Alim na ce ka bari mene ne amfanin hakan? Kamar wanda ya rasa hankalinsa?"
Kara dukan Majeed yake ta ko ina har jikinsa ya fara ruɗu-ruɗu idon nan ya kara ja sosai kamar zai faɗi ƙasa.
Mom da Ammie kuwa suna kan Rusul Dr Habeeb nata kokarin bata taimakon gaggawa.
Tsawa Big Daddy ya wa Small Dady yana ficike Majeed,"In ka kuskura ka kara taɓasa sai na mugun ɓata maka rai."
"Haba Yaya Don Allah kenan haka zamu zuba masa ido yana cutar da ita, wannan wace irin bakar zuciyace da bata kaunar jininta, ba ita ya kamata ya nunawa tsana ba mu ya kamata ya fito ya bayyana mana cewa bamu cancanci haihuwarsa cikin Ahalinmu ba, duk kiyayya aka yi aure ai ya ci a sarara amman shi na lura kamat kara tunzura shi ake ni gaskiya ba zan jure ba." Cewar small Dady.
Big Daddy ya ce, "In dai na isa da kai kar in kara jin ka kuma fadin wata magana bare kokarin aikata wani....
Dr Habeeb ne ya katse Big Dady da fadin, "Condition din Rusul ya yi tsanani ba zan iya komai anan ba akwai bukatar mu tafi asibiti , in ba haka ba nan da wasu awanni numfashinta da ya yi saura zai iya tsayawa cak wanda hakan na nufin rai zai iya bita a jikinta in ba asamu mafita cikin gaggawa ba."
Dukaninsu firgici ya bayyana a fuskarsu mussaman small dady, Ammie da Mom da kuma uban gayya Majeed.
Big Daddy ne kawai bai nuna komai a zahiri ba duk da cewa a rayuwarsa kaf ta duniya ba wacce yake kauna sama da Rusul,zuciyarsa ta fasa take tamkar zata buga amman ban da addua ba abun da yake yi.
Small Dady ne ya dauketa suka nufi mota , Big Daddy yaja hannun Majeed suma suka fita tare suka bi bayansu.
Dukka manyan likitocin Asibitin sai da suka taru kan Rusul tun karfe 8 sai karfe goma Dr Habeeb ya fito yana zufa.
Cikin sauri Small Dady ya tare sa da fadin, "ta farfado? Don Allah kada ka ce mun wani abu ya samu Rusul muddin Rusul ta rasa ranta sanadin Majeed babu tantama shi ma sai nayi ajalinsa."
Murmushi Dr Habeeb ya yi ya ce, "Alhmdu Lillah ta farfado an ci sa'a da kyar sai dai muyi godiya ga Ubangiji domin ba don shi ba Rusul kam sai dai ayi wani labarin ba wannan ba."
Hamdala Mom da Ammie suka yi a tare. Big Daddy kuwa ajiyar zuciya ya yi na fadin , "Alhmdu Lillah, yanzu za mu iya shiga mu dubata?"
Dr Habeeb ya ce, "Eh inda hali abarta ta dan sha iska ko na 10minute ne sannan kuma ko zamu dan je office ina so inyi dan bayani."
"Alright muje to." Big Daddy ya fada suka bi bayan da Small Dady.
Dr Habeeb ya ce, " Alhaji gaskiya zan fada maku an fara zuwa gaba mai haɗari sosai ga rayuwar Rusul zata iya rasa ranta kamar yadda na fada a farko, ta tsorata Sosai wanda hakan ya taɓa mata bugun zuciya,irin hakan ya kara faruwa ko makamancinsa babu mafitar da za a iya bi don ceto rayuwarta zai fi kyau a tsaya domin kareta da kara fadawa irin hakan duk da ba a fata dai amman akwai bukatar kiyayewa don a yanzu haka akwai magungunan da zamu daurata akai."
Numfasawa Big Daddy ya yi ya ce, "ba matsala mun gode sosai Dr Allah ya bar zumunci,yanzu dai zamu iya tafiya da ita ko?"
"Eh Alhaji za ku iya zan hado magungunan yanzu in rubuta takardar sallama sai ku wuce kawai Allah ya kara sauki."
★★ Suna fita a office din Dr Habeeb suka nufi dakin da Rusul take ta farfado ban da shagwaɓa ba abun da take yiwa Ammie da Mom.
Su big Daddy na shiga ta taɓe baki kamar zata yi kuka ta ce, "Big Daddy,Small Dady Ina gida zamu koma? Don Allah karku maidani wancen gidan Black-black din cen kasheni yake son yi."
Ta fada tana nuna Majeed.
Small Dady ya ce, "Eh Daughter gida zamu tafi In Sha Allah ba zaki kara zama inda yake ba sai dai bakin halinsa ya kashesa ba dai shi ya kashe ki ba."
Big Daddy ya kalli Majeed yana dafasa, "ga shi har yaji ma ciwo akai muje a wanke a ma treating wajen kafin su gama hada sallamar mu tafi."
Rike masa hannu ya yi suka fita ciwon da Small Dady ya ji masa aka wanke masa sannan aka rufe gun kuma akayi masa allurar kariya.
Dukansu sun fito zasu tafi Small Dady ne ya dauki Rusul yasa ta cikin mota Big Daddy ya, "ba gida zamu ba gidansu zamu je yanzu."
"Yaah? Gidan su kuma me zamu....
Ya dakatar da shi, "ayi abun da nace kawai bana bukatar wata magana."
Small Dady ji yake kamar ya fice a motar tsabar zafin da zuciyarsa ke masa amman ba yadda ya iya haka ya zauna har suka je gidan main parlour suka zauna dukansu. Big Daddy ya yi gyaran murya, "zan yi magana kuma bana son kowa ya tanka har sai na gama fadin duk abun da zan fada, Majeed kana kiyaye irin abun da zaka yi don hukunci wa Yar Uwarka gudun kara samun matsala irin hakan,sannan kema ki kiyaye Yayanki ne jininki kuma mijinki a kasansa kike a komai na rayuwarki a yanzu, Don ba da ban securities sun fahimci cewa akwai matsala sun kirani ba ya kake tunanin abun zai kasance? Sai dai kuta zama a haka karshe numfashinta ya dauke? Ku sani bawa bama sonku yasa muka aura maku juna ba,muna kaunarku fiye da tunaninku kasancewarku tare shine farincikinmu kawai. Sannan kuma ina kara tabbatar maku da cewa ba inda zaku ba za ku koma gida ba anan zaku ci gaba da rayuwa in kun so ku gyara in kunki kuma ku ci gaba da rayuwa son ranku."
Tun Mom na jurewa har ta gagara fashewa da kuka tayi, Rusul ma ta fara.
"Yanzu Don Allah 'Yartawa daya tilo ake son rabani da ita gabadaya a duniya? Ba zan jure ba wallahi ba zan iya rayuwa babu Rusul ba sai dai in zauna da ita ko abani abata mu tafi, tunda kai baka sonta ni ina sonta ina kaunarta ba zan zauna a kasheta a idanuna ba."
Small Dady ya ce, "Gaskiya ne abun da take fada Yaya In da hali ma Ni nafi so araba auren nan ka dai ji abun da Dr Habeeb ya fada zata iya rasa ranta a irin wannan shashashancin da Majeed yake kada hakan ya janyo mana matsala tsakaninmu tun abu na ga yara kuma kar ya koma garemu manya Don Allah kayi hakuri a warware wannan auren tunda dai yadda muke zato bai kasance ba har yanzu."
Gyara zama Big Daddy ya yi ya ce, " Indai dukkanku na isa da ku to babu mai raba yaran nan, na ce babu mai rabasu haka zasu rayu, Allah ne mai karewa kuma shi zai kare in Rusul ta rasu kwananta ne ya kare saidai wani ya zam sanadi amman bawai ya zam mai daukan ranta ba." Yana fada ya tashi ya fice abunsa cikin bacin rai.
Small Dady ya mikawa Rusul magunguna ya ce, "Kiyi hakuri Daughter ki daina kuka, zan siyo miki sabuwar teddy har chocolate wa innan magungunan kine akwai wacce zata dunga zuwa tana baki."
Ya juya yayiwa Majeed wani mummunan kallo sannan ya yi kwafa shi ma ya fice.
Ammie da ta zama yar kallo bin bayansa tayi kawai ita ma. Mom ba yadda ta iya itama haka ta tashi ta fice tana kuka Rusul na kuka itama kamar zata hadiye zuciya har da shiɗewa.
Suna fita Majeed ya kalleta tare da wurga mata harara, "Mayyar banza da wofi da ma kin mutu kowa ya huta, tunda nake Small Dady bai taɓa dukana ba amman yau kin zama sanadi, to wallahi yanzu aka fara yanzu na fara tsanarki sai dai duk abun da zai faru ya faru karshe dai ace za a kasheni nima kuma don an kasheni akan ki ba komai bane."
Share hawaye ta yi tana, "Nice zan fada maka yanzu na fara tsanarka kuma yanzu na dau damarar yin duk wani abu da zai cutar da kai kamar yadda kake kokarin salwantar mun da rayuwa na kara fada ma saidai mu salwantar dana juna."
Tashi ya yi ya bar mata parlourn ya fice waje.
Ita ma ta tashi jiki ba kwari haka ta rarrafa ta tafi dakinta ta kwanta, mai lura da ita ne Mira ta zo ta kawo mata abinci tana, "Madam Ur food is ready in kin gama ga maganin da zaki sha." Ta fada tana ajiyewa.
Shagwabewa ta yi tana, "ni bana wani son magani lafiyata kalau ma fa."
Da kyar Mira ta lallabata ta sha maganin bayan ta dan cakali abincin nan take barci ya kwasheta agun.
Sai can Yamma ta farka,Mira ta taimaka mata tayi wanka ta baza teddies dinta tana wasa,ita kadai kawai ta fara sheƙe dariya tana, "na tuna wallahi na tuna yadda ake a wannan Film din yau zan bawa wancen yaron mamaki."
Ta shi tayi ta birkita wadrope dinta ta dauko wata farar alkyalba mai hade da hula a jiki fara ce tas ko ado babu ko kadan tasa, ta dau farar hoda ta shafe fuskarta da shi,gashinta ma gabadaya ta zazzaga farar hodar a jiki ya yi kamar kan tsohuwar da furfura ya cika.
Ita da kanta da ta ga kanta a madubi sai da ta razana.
Tana daidaita lokacin fitar sa masallaci ta shige dakin ta kashe haske sai na window da ke shigowa kadan kadan ba a gani sosai.
Tana jin motsinsa taje daidai bakin kofa ta tsaya shigowar sa ta fara, "Dakata, na ce dakata." Ta fada cikin wata irin murya wacce take kokarin banbantata da na Bil-Adama.
Tsaki Majeed ya yi cikin zafin rai ya ce, "kin San Allah in baki matsa mun kin fice mun adaki ba zaki sha mamaki yau sai dai ki mutu kuma inna sa miki Tsaka a baki."
"Bil-Adama kuna da tsaurin ido." Ta fada cikin jan maganar.
Kokarin sa hannu ya yi a aljihu zai ciro waya ya haska sai a lokacin ya tuna ashe ya bari adakin.
Dagowan da zaiyi kawai ya fara jin saukan mari a fuskarsa ta kowanni bangare .
Jikinsa ne ya fara rawa da idanunsa suka fara yi masa tozali da fararen kaya daga sama har kasa ga shi babu fuska sai wata doguwar hula.
Kafa masa sanda tayi a kafada tana fadin, "MAN RABBUKA."
Nan fa Majeed ya kara tsure wa ,cikin rawar murya yake fadin, "Na shiga uku mala'ikan mutuwa a duniya muke Don Allah kar ka dauki raina na na naaaa....
Yama gagara karasa maganar nan ciki ya fara kara yana kuka zufa na keto masa har diga take, guduwa ta fara sauka daga wando zuwa kafafu ,ya kasa tsaya da kafafunsa yana kokarin faduwa ga gudawa kara yawa take tsabar tsoro.
Kasa rike dariyarta ta yi kawai ta sake tana kunna wutar dakin.......
*KURUCIYA PAID BOOK ne ga duk mai bukata har karshe zata biya 500 via 1453215759 Aisha Abdullahi Sani Access Bank, Evidence of payment to *** free pages na daf da karewa* [26/07, 1:41 pm] Xayyeesherthul-humaerath🍂: : ♥️ *ƘURUCIYA* ♥️
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION*
Aisha Sani Abdullahi *(Xayyeesherthul-humaerath)*
Bismillahir-Rahmanir-Rahim