KUCHAKAR KISHIYA

PAGE* 1

by @xayyeesherthulhumaerath

------------------------------------------------------------------------

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM INA ROKAN ALLAH YASA NA KAMMALA LITTAFINNAN LAFIYA KAMAR YARDA NAFARA KUMA YASA YA ANNFANAR DA MUTANE KAMAR YADDA NA TSARA*

Amman ne yashigo tare da sallamarsa Kayan takaici abin da yasaba gani amman har yanzu baya juran ganin hakan. Hamlat ce kwance akan kujera tana ta zabga uban barci ga daki kacha kacha kamar anyi dambe da alamu ma dakin yafi wata ba agyarashi ba. Ran Amaan yayi matukar baci hakan yasa ya dibo ruwan sanyi yamakawa hamlat afuska. Afusace ta farka tare da fadin kan ubancen wani dan iskan ne ya watsamin ru....... Ganin Amaan tsaye agabanta ne yasa takasa karasawa . Sai da taja dogon numfashi sannan tace"toh uban yan tsurfa andawo kenan nikuma banda sukuni". Shikuma Amaan tsaye yake agabanta tsabar bacin rai ko magana ma yakasa kawai kallonta yake. Sai da takara da cewa dallah malam ka matsamin akai ko? Amaan yayi murmushi sannan yace"kingama? Ina ke bakisan darajar kanki ba bare na mijinki?. Da duk kan alamu tunda nabar gidannan ba agyarashi ba kusan wata kennan fa. Kuma wai da sunan mijin ki yadawo daga tafiya ko ajikinki. Sai rashin mutuncin dakika tanada kika fara zubamin. Yana maganganun nan hamlat na hararasa tare buga kafa akasa. Bata bari ya kammal abinda zai fada ba tace"dakata dan matsiyata nifa ba bai warka bace karka kuskura kanemi batamin rai . Bawai dankaga ina dan ragama yanzu ba to wallahi zan dawo yafi nadama domin bana daukar raini kai kafi kowa sani". Amaan yace"wai ina mijinki kike fadamin maganganun nan toh wallahi daga yau inzakiyi rashin kunyarki ta tsaya akaina batare da kin hada da iyayena ba". Hamlat taja dogon tsaki tare da fadin"su iyayen naka suwaye ai bansan su ba bare nasan da zamansu domin kasan bana harka d matsiyata kaima dai lalurace tasa nake zaune dakai domin kasan inba haka ba da tuni na dade ba barinka.". Tana kaiwa karshe tayi tsaki tare da bangaje shi tukun tashiga daki. Amaan binta yake kawai da kallo bamusan me yke aiyanawa azuciyarsa ba . Yafi minti talatin yana tsaye ba abinda yake illa tunani . Daga karshe kuma yace"Allah yakyauta". Alokacin yafara gyaran falon nan yafi awa sannan falon yafara kyan gani kuma duk da hka ba bai gyaruba yadai rage neh