KUCHAKAR KISHIYA

Page 5

by @xayyeesherthulhumaerath

Sai ga amrah nan tazo tana fadin"toh yar matsiyata wato ke skul dinma sai kinnuna halin talakawan ko?. Ke kuma hanan kina yar babban gida amman kina bin yar me kwosai gidan laka?. Alokacin ahalam ta razana ta miki zumbur Tare da chukumo amrah tana fadin"ke wai ni sa ar wasan kice?. Wato ke yar masu kudi ko. Idon Amrah yaciko tayi zuru zuru. Ahalam takara dacewa"toh inaga ma kudin uban naki nasata neh kum wlh inkika kara cemin matsiyaciya sai naci miki mutunci. Hanan tayani mulakada banza. Aiko hanan da ahalam suka hadu suka dunga xabgawa amrah duka tun tana kuka har tayi shiru sai nishi. Duk sun kumbura mata fuska anfasa baki. Students sun hadu sai murna suke yau amrah ta hadu da wadda tafita masifa. Sai ga wata malama nan dakyar tasamu tarabasu sannan tasasu nildown . Aka kira uncle salim domin musu hukunci dan kuwa yafi kowa iya duka amakarantar dan hka ma in dalibai sukayi laifi shike dukan su amman sabida bala"i na ahalam shi gudun laifinta yake dan yasan tsagwarar rigima gareta . Yana zuwa yaga ahalam aikuwa sai da gabansa yafadi ganinta da yayi awajen. Yace"ahalam yadai lafiya dai ko? Keda baki lafiya meyakawo ki nan?. Aituni ahalam ta shagwabe sannan tace"uhumm ba wannan yarinyar bace take zagina. Shine fa nafasa mata baki". Amrah tace",kut ni zakima shari?. Uncle salim yama amrah tsawa me girgiza mutum dukansu sai da suka razana. Sannan yace"nasan halinki sarai amrah bakyajin magana kece baki da gaskiya domin nasan ahalam batada lafiya barata taba shiga harkar ki ba . Dan haka maza kitashi kibar wajen nan'. Amrah ta tashi tana tafiya dakyar. Shiko uncle salim yace"pls sister kidai na dukan mutune haka kinga fa watarana inbana nan sai an rama musu abin da kike musu". Ahalam tace"kuttt wallahi inta karamin sai na fasa mata hanci". Hanan dai tanajin su tayi shiru tna ganin ikon Allah dan tasan uncle da ahalam sai Allah. Uncle salim yace"to naji nidai tashi kikoma aji kinga tun dazu akakoma". Ahalam tace"wallahi bazani ajinba gida zanje abuna inci kwosai". Uncle salim dakyar yashawo hankalin ahalam sannan ta yarda sai antashi. Lokacin tashi yayi daidai da lokacin tashi daga office din Amaan da hamlat. Ahalam tana tafi tana tsokanar mutane. Dreban su hanan yazo amman taki yarda tabisu domin tafiso tana tafiya tana tsokanar mutane. Aiko tana cikin tafiya taga wasu mutane na fada. Da alama ma mata da mijine. Mijin yana cewa"ke baki da hankali ko akan titinma sai kin nuna halinki . Kafin matar takara magana yafara dukanta. Ahalam tana hangosu tazura da gudu tana zuwa tadau katon dutse ta dane bayan mijin tana buga masa dutsen aiko kuwa tuni ta fasa masa goshi. Tana fadin mugu kawai saketa. Yanajin zafi kuwa yasake matar itakuma ahalam ta dirka abayansa. Matar tana dagowa taga jini agoshin mijinta tafara kuka tana ke miye hka wayace kifasa masa goshi tafara goge masa jinin. Ita kuwa ahalam sai dariya take tana cewa"wayace kadaketa aigashi narama mata". matar ta biyo ahalam dagudu. Aikuwa ahalam kafa menaci banbaka tana gudun amman tana cew"wawiya kawai ta tsaya wani garde nadukanta narama mata amman tanajin haushi. Har matar tagaji da gudun ta tsaya amman ahalam bata tsaya ba . Ahalam tajuyo tana mata gwalo aiko sai gashi karaf tabige me mangoro. Me mangoro akasa mangoro ma akasa.