Page 6 & 7
*ASALIN LABARIN*
*SHIN AMAAN DA HAMLAT SU WAYE*? *SANNAN KUMA WACECE AHLAM*? *SHIN AMAAN DA HAMLAT SU WAYE*?
Amaan dane ga mallam sani tare da mahai fiyarsa baba nafi. Su biyune kadai awajen iyayensu daga Amaan sai kanwarsa Amrin Asalin sunan Amaan Ahamed ita kuwa Amrin Amina. Baban Amaan shine babba a familynsu daga shi sai kaninsa Alhaji sulaiman Asalinsu yan garin kanone Amman kasuwanci yadawo dasu garin jos. Alhaji sulaiman me arzikine na gaske domin kuwa ya ninka yayansa adukiya. Yanada kampani dayawa wa inda yasa ake lura masa dasu . Sanadiyar hakan shiyake daukan dawainiyar yayan yayansa . Alhaji sulaiman shine mahaifin Hamlat wadda asalin sunnanta halima itace ya daya tak awajensa. Tare da mahaifiyarta hajiya salma. Alhaji sulaiman yana matukar son Amaan sabida kyawawan halayensa. Akan hakan yabasa kamfani guda. Itakuwa hajiya salma sam bata kaunar Amaan sabida tana ganin Alhaji sulaiman yafi nunawa Amaan so akan hamlat. Tare Amaan da Hamlat suka taso duk da ya girmeta amman kome nasu tare alhaji yke musu. Karatuma tare sukayi har suka gama. Kwatakwata Amaan bayason hamlat sabida halinta na nunawa talakawa suba mutane bane sannan ga nuna isa ga kowa. Amman ita ahakan tadaurawa kanta son sa duk da bata nuna masa hAkan. Tasamu hajiya salma tasanar mata ita kuwa hajiya salma taji dadin hakan domin atunaninta hanyar da zasu ceto dukiyar Alhaji daga hannun Amaan kenan. Da aka sanarwa da Alhaji yaji dadi sose dan hka yaje yasanarwa da yayansa shima yanuna amincewarsa duk da kuwa yana jiyewa dan sa mugun hali irin na hamlat. Da aka sanar da Amaan ya girgiza sose Amman dan biyayya haka ya hakura akasa biki batare da bata lokaci ba. Alhaji sulaiman shi yadau nauyin kome domin acewarsa shine uban ango . Ankashe nera kamar ba asan zafinta ba. Bayan aure Amaan yaso adaukan musu yar aiki sabida yasan tsabar kazantar hamlat amman taki. Wai ita adole me kishi tana matukar kishin Amaan amman bata taba nuna mai soyayya ba koda kuwa ta minti daya sai zagi da cin mutunci. Ahaka Amaan yake juran zama da hamlat sai dai inshi yaso yagyara gidan ko kuma yakira Amrin ta gyara. Kuma ita intazo ta tsiya suke ravuwa da hamlat domin Amrin bata barin takwana anamata abu take ramawa. Hamlat bata taba neman Amaan sai bukatar ta tashi tukunnah. Koda Amaan yayi niyar wulakantata inya tuna da maihinsa da nata sai yafasa. Wannan shine takaitacen tarihin Amaan da hamlat.
*WACECE AHLAM*? Ahlam ya'ce ga mAllam Rabi"u da baba maryam. Asalin sunan Ahlam Aisha wadda akamata lakabi da Ahlam. Mallam Rabi"u talakane fitik dan haka inkaje gidansu ma kazata awata karkara kake domin kuwa gidan lakane sannan kuma dan karami. Baba kuwa suyan kosai take kwofar gidansu Asalinsu yan niger ne cirani yakawo mallam jos hakan yasa yatawo da matarsa. Mallam nakoyar da manyan mutane addini tahaka ne yakesamu damar biyawa Ahlam makaranta da bukatunta. Ita kuw baba intayi suyanta tasamu riba anan take musu cefanan abin da zasuci. Ahlam takasance ya me rikice da shagwaba ga tsokanar mutane. Mutane dayawa suna sonta domin tana gwarjini awajen mutane ko ina taje anasonta. Duk ranar ba ba school kuma ba madarasa sai ankawo karar fin sau goma. Inko aka hanata fita tata kuka kenan ko kuma tazauna ta ta tsokanar baba. Da mallam. Intaso tata jama baba kumatu tana cewa"babata yar kyakkyawa me kumatun cincin". Tun baba na dariya har sai tagaji tacewa"ahlam taje wasa". Kadan daga cikin tarihin Ahlam kennam.