Page 8 & 9
Ahlam na ganin haka ta dauki katon mangoro acikin mangororin dasuka zuba sannan ta kara zurawa da gudu. Sai mutanen wajen ne suka taimakawa me mangoron nan yatashi sannan aka kwashe . Shiko me mangaro baya ma ta sauran mangoron sai ta wanda tadauka dominn kuwa duk aciki shine babba kuma me kyau. Yaso yabita amman ina ahlam tafi karfinsa domin acikin minti daya har yadai nah hangota. Ahlam kuwa kafa me naci ban baki ba . Amaaan ya iso kofar gidansu ahlam kawai jira yake yaga da me yau tadawo. Aiko sai gashi ta yanko kwana da shegen guda hanu rake da mangoro. Amaan yakasa magana bai san lokacin daya sake baki ba yana kallon ikon Allah. Tana zuwa taje wajen da ake sai da ruwa tace su sanmata ta wanke mangoro. Aikuwa dayike sun san halin ahlam yar rikice ce haka suka bata batare da bin layiba. Tana wankewa ta watsama me ruwan nasauran hannunta. Shiko kawai dariya yake domin yasan halin ta . Tasamu waje tazauna tana ta shan mangoronta. Sai ga wani yaron makwotansu nan. Yace"ahlam dan sammin". Ahlam tace"tab sai inka yarda zaka rakani mu tsinko danyen mangoro". Aliyu yace"bayan inmunje guduwa kike kibarni". Ahlam tace"toh ysssn yau bazan gudu ba " Aliyu yace"toh sammin nasha tukun muje kumama yau gidan baba kadan bala'i zamu kinsan natasunfi girma. Ahlam tace"ehmana ai nata kaman wannan suke kasan danye yafi dadi barin ma inmukasa gishiri . Aliyu yace"eh mana yawo na tsinkewa yana nidai bani nafara shan wannan". Ahlam tasa hakory ta gutsiro masa dan kadan duk yabaci da yawo sannan tace"gashi. Aliyu yace"haba dan wannan me zanyi dashi nikam". Ahlam tace"kambala'iiiiiiiiii ! Lallaima wato ka raina ko? Toh shikenan bara nashan ye kayana Ai Aliyu najin hakan yakarba da sauri domin yasan zata iya hanasama gaba daya". Shiko Amaan yanan anbarsa da sakakken baki sai dayaga yadda take fincikar mangoronma yadauko waya yanata mata hoto. Ita kuwa shan abunta take batama san yana wajenba. Ahlam tashanye tana neman ruwan wanke hannu sai ga wata yarinya da ruwa akanta tana tafiya. Ahlam tace"ke yar nan me majina zoki sammin ruwa na wanke hanuna". Yarinyar ta galla mata harara sannan tace"bazan bayar ba din". Ahlam tace"kuttt" Sannan tacire hijabinta tadaura akugu . Ta chikumo yarinyar ruwan yazuba sannan tafara dukanta tana ina ke baki da kunya ko? Kina yar karama dake har kin iya rashin kunya to yau sai nakoya miki kunya awajennan. Yarinya sai ihu take Anrasa me kwatarta ahannun ahlam kowa tsoro yake ji kar tadawo kansa. Sai da Amaan yaga abin yakici yaki karewa yaje yarabasu. Dakyar suka rabu Yana rabasu sai ga baba nan ta fito aliyu yaje ya fada mata Ahlam tana ganin Amaan tasa dariya sannan ta galla masa harara da gwalo. Tana cewa"nadai dana". Baba nazuwa tace"ohh ni ahlam wai bazaki girma bane". Ahlam tuni tashagwabe harda kakulo kuka tana"uhumm baba rashin kunya fa tamin kuma na girme ta ". Baba tace"eh lallai kam tunda ke bakya ma nagaba dake ba". Baba tajata dasu shige gida. Tajuyo taga amaan ta daga masa gira. Amaan yamata murmushi sannan shima yahau motarsa yanufi gida. Yana cikin tuki daya tuna hamlat zaije yatarar agida har ransa ya jagule. Yana isa yatarar maamah kawar hamlat na gidan yayi sallamAh basu kulashi ba hakan yasa yahuce shashinsa Yana tafiya maamah tace"ah lallai kin sakema mutumin nan ko geshemu fa bai yi ba. Hamlat taja numfashi tace"oh indai wannnan ai karki damu bari kitafi dama da haushinsa nadawo daga office domin duk meeting dinnan daya shirya akai na ne. Kuma yau zan basa mamaki. Maaamah tayi guda sannan sukayi shewa . Maaamah takara dacewa"shiyasa nake jidake yau banaso ayi barci agidannan". Hamlat tace"aiko baki fada bama dan yau natanadi buhun rashin mutunci. Maaamah tadubi agogo tace kinga kar dare yamin anan bara natafi". Hamlat tace"toh ina zuwa bara nJe nadauko miki abin". Tana tafiya maamah ta gallama mata harara sannan tace ballagaza kawai. Tana ganin hamlat tadawo tafara cewa"kawa ta gari kenan tana murmushun gulmah.". Hamlat tace"hmm gashi bayawq dubu darine kya fara rage abubuwa kafin naciro wasu" Maamah ta washe baki sannan tace"bakome ai sai munyi waya". Hamlat tace"owk byeee. Maaamah natafiya hamlat tanufi shashin Amaaan. Tana zuwa ta bankada kofa.