Page 10 & 11
Yana zuwa yadaga hannu domin marintA har hamlat ta rufe ido tsabar tsoro. Amaan yaji jiri yafara dibansa kan ya ankara yafadi kasa. Karar fadiwarsa ce ta sa hamlat bude ido. Tana ganin amaan akasa ko numfashi babu ai tuni ta firgita tafara fadin"Amaaan Amaaan Ammaaan '. Kakara girgizShi sannan ta kuma cewa"Dan Allah karka mutu katashi wallahi inasonka inka mutu nima mutuwa zanyi pls katashi mana Amaaan dinah". Dataga Amaaan bai da niyar motsi tuni ta tashi tana kuka takira me gadi. Shikanshi maigadi sai da yaji mamakin ganin Hamlat tadamu akan Amaaan . Dasaury maigadi yataimaka mata akasa Amaan amota. Ba inda suka huce sai asibiti. Da hike daman nan Amaan yake zuwa aituni aka karbesu akabashi gado. Bayan hamlat ta dan samu kanta ne takira momynta ta fada mata. Momy tace"dafatan dai ba abinda kika masa kinsan halin dadynku akan wannan yaron nidama bakikaisaa asibityn ba dakinbarsa yakarasa". Hamlat tace"haba momy nifa wallahi inason Amaaan". Momy taja tsaki sannan tace"toh maiya ai sai kitasonshi Gamunan zuwa". Hamlat takashe wayar tana nishi. Momy taje wajen dady kamar mutuniyar aziki tasanar dashi . Aiko afusace dady yatashi yaji sahibinsa ba lafiya. Sai da momy tadanyi guntun tsaki. Dady yace"kidaukomin key din mota bari nama yayanah magana mutafi". Dady yaje yasanarda baban Amaan da mama duk suka fito domin tafiya asibiti. Dady tuki yake dagudu sose sai da baban Amaam yace"haba kayi ahankali mana kadaina sa damuwa aranka insha Allah jikin dasauki". Shidai dady kawai jinsa yke Aman zuciyarsa bugawa take. Suna isa suka nufi inda Amaan yake amman anhana shiga domin har yanzu bai farfado ba. Doctor yakira dady domin yamasa bayani annan ne yake fada masa cewa"Alhaji yakamata kuna lurah da danku sose domin da alama damuwa tamasa yawa sannan kuma zuciyarsa tana daf da bugawa dan haka aguji bacin ransa". Dady yafirgita sose hakan yasa zufa tafara keto masa sannan yace"yanzu ba yadda za ayi dashi". Likita yace"eh to akwai maganin da inya jury sha insha Allah za"asamu nasara". Dady yaji dadin jin hakan ahaka sukayi sallama da likita. Hamlat kuwa tunda taji ance ya farfado tayi tafiyarta tabar asibitin. Washe gari Ahlam tana gida yau ba makaranta. Baba na suyan kwosai awaje ita tazauna agun baba tayitayi da ita takoma gida taki domin tasan sai taja mata magana. AhakA tazauna sai ga wani me ruwa nan yazo siyan kwosai. Ahlam tace"dannan na nawa za"abaka?. Baba tayi karaf tace"ke baki da kunya ko". Ahlam tace"uhymmm baba ai nabar tukunyar agida ko naje na dauko?. Baba ta kalla mata harara sannan tace"mallam na nawa kakeso?. Yace"na hamsin. Baba tace"to kadan yi hakuri bari yakarasa". Ahlam takalli kafarsa tace"haba kawu mai ruwa baka wanka ne?. Mai ruwa yace",eh ". Ahlam takara cewa"Allah sarki jibi yarda kake wari kuma gashi har kafarka tafashe ". Mai ruwa dai sai kauda kai yake. Ahlam takuma cewa"tunda mamanka batasonka batama wanka to kazo gidanmu babata zatama kaga ni sai nashafa ma mai ko?.