Page 12 & 13
shidai dan mai ruwa yayi zugum kawai kallon ahlam yake. Mama tayi sauri tasamasa kwosansa ai kuwa bai fi minti daya ba yabace awajen. Ahlam tace"baba yssn mai ruwan nan kazami nr wari fa yake shiyasa nace yazo kimasa wanka nikuma nashafa masa mai ga kafarsa duk faso kamar kafar saurayin *khadija Ahmad(princess deejerh)*". Baba tace"kai kaiiiiii ahlam nikam bansan yazan yi dake ba yanzu inba dan Allah yasa mai ruwan dan kirki bane ai da wani ne datuni yayi gudunbala dake". Ahlam tasheke da dariya sannan tace"aikuwa danasa uncle salim yamasa dukan tsiya". Baba tace"hmm Allah yakyauta dai". Ahlam tace"Ameen yar babata kyakkyawa mai fuskar cinçin".. Baba tayi murmushi sannan tace"wato kedai ko kinbatama mutum rai sai kinsashi dariya ko"?. Ahlam tasa dariya Ahaka yau suka gama suya duk wanda yazo sai ta tsokaneshi wasu ko dariyama take basu. Yawancin kostoman baba kawai dansuga ahlam da shirmenta suke zuwa siyan kwosai domin kuwa ahlam tanasa mutane nishadi fiye da yadda ake zato. Amaaan na farfadowa ba wadda yatuna sai Ahlam hakan yasa shi wani dogon murmushi wanda yasa bai kula da mutanan dake kansa ba. Sai abokinsa arfan yace"yadai yallabe daga farfadowa sai murmushi?". Sai alokacin Amaan yafahimci ma inda yake da wa inda suke tare. Dady yace"yadai son fatan lafiya? Amaan yakara murmushi sannan yaace"lafiyalau dady ina kwanan ku". Dukansu suka amsa cikin farinciki. Bayan nan Amaan yatashi yayi wanka yayi sallah sannan yasha tea. Bayan ya hutane arfan yake cewa"wai ya akayine ciwon nan ya riskeka lokaci guda?. Sai ga hamlat tashigo adai dai sanda arfan ke tambayar nan. Kowa yabada hankalinsa ga Amaaan.