Page 15
Baba tace"ke ko ai da mun huta da rigimarki ahlam dan inaga ba mai iya jure halinki inko ansameshi to na musamman neh". Ahlam ta kurma ihu sannan tace"mallam baba kaganta ko?. Baba yace"naganta mamana kiyi hakuri bazamu siya mata chocolate ba". Ahlam tace"yAuwa babAna kai kam zan siyama mota itakuma baba mai fuskar cincin ysin bazan siyamata ba uncle dakai kawai zan siyama". Baba tace"kwadai ji dashi". MAllam baba yace"yauwa yar albarka tashi muje insiya miki chocolate din sai in anjiyeki askul ko" Ahlam tace"yes my sweet dad "sannab ta kalli baba tace kekuma biscuit mom ce wallahi". BabA da mallam baba sai da sukayi dariya iya son ransu. Har ahlam tafara jin haushi tace"to ma nafasa". Mallam yace"a"a muje yar albarka". Ahlam tayi murmushi sannan takama kumatun baba tace"bAbata mai kumAtun cincin na yafe miki kuma harda ke zan siyawa gida'. Ta shgwabe fuska sannan tace"kimin addu"ah babata". *daman wannan dabi"ar ahlam ce tasaba tun tana karama kullum inzata fita sai iyayenta sun mata addu'ah sAnnan ita kwata-kwata bata da rikwo arayuwarta kana bata mata rai intayi masifarta alokacin to anjima ma zata kulaka* Baba ma tayi murmushi sannan tace"toh mamanah yar albarka Allah yakiyaye hanya yatsaremin ke yasa kuma kiyi abinda kikaje yi haka kuma arage tsokanar nan dai". Ahlam ta tashi ta zura da gudu sai da taji bakin kwofa tace"Ameeen mai fuskar cincin dina". Baba tayi murmushi mallam ma yabita suka tafi. Suna fita kuwa Allah yasa suka samu mota batare da bata lokaci ba. Karfe 7:30 dai-dai suka isa aiko da ahlam taga batayi latti ba sai murna take yau zasu tare masu latti ita da uncle. Sai da baba yashigar da ita sannan yabata naira 20 tayi break tamasa godiya sose sannan tashiga ciki. Tana shiga ta hango uncle salim da gudu takarasa gunsa tana cewa"oyo yo uncle". Uncle yace"welcome sweetyn" Ahlam tace"good morning uncle". Ashagwabe take magana Shima uncle yashagwabe domin shagwabar ahlam kashe masa jiki take Yace"morning sweetyn". Ahlam tace"uhumm uncle kaga yau banyi latti ba ko?. Yace"yes my sweetyn ya akayi hakan ne kokin fara samun sauki ne?. Ahlam tayi dariya sannan tace"yasin kasan dama lafiyata lau yau su babane suka hanani zama agun kwosai" Uncle yace"aiko sun min dai-dai domin ina bukatar ganin sweetyn akusa". Ahlam tashagwabe snnan tace"aiko yau ni zanyi dukan latti". Uncle ya rike hannun ahlam yace"yes sweetyn muje" .