Page 17
Ahlam tayi gaba abinta tazauna agurin zamanta. Amrah ma tabita suka zauna tare abin su. Uncle salim kuwa yafita yatafi office dinsa. Malam yacigaba da karutu tsit kakejin aji kowa yayi shiru. Abangaren su Amaaan kuwa. Amrin takammala gyara gidannan tsab kaman bashiba. Ita kanta matar gidan sai kallo take tana wani fadi kamar ita ta gyara. Amrin taje dakin Amaaan tace"bloodly br mai zan dafa neh?. Amaaan yayi murmushi sannan yace"ayya bloodly sis ni banason cin kome'. Amrin ta tabe baki tace"uhum wallahi sai kaci wani abu inba haka ba nafadawa dady". Amaaan yarike baki sannan yace"toh aunty bombolas zata hadani da dadyna". Amrin tayi dariya sannan tace"toh mezakaci yanzu". Amaaan yashagwabe fuska sannan yace"uhumm kawai kadamamin custard inaga ya isa". Amrin tayi murmushi tace"as u wish bloodly bara naje nadamama". Amaan yace",okey". Amrin nafita tashiga kichen batare da bata lokaci ba kuwa ta dama masa tasa madara sose domin tasan bloodly dinta bayason sugar sabida haka batasa masa ba. Tana zuwa tace"oya bloodly tashi inbaka". Amaan yayi murmushi yace"randa kikayi aure zanyi rashi bloodly". Amrin taji tausayi Amaan sose domin ita kadai tasan wahalar dayake sha agun hamlat. Idonta yaciciko amman haka ta dage tayi murmushi sannan tace"ai dole kasamanmin aunty kafin nabarka'. Amaan yayi murmushi azuciyarsa kuwa Ahlam ce tazo masa Amrin tace"umm kaga tashi kasha ". Amaan yatashi yana murmushi . Amrin nabasa suna yar hirarsu ta yan uwa. Sai dariya suke ita kuwa hamlat tanajin su duk zuciyarta ta jagule sai faman mita take. Ai tuni tanufa kofar dakiin amaaan Tabankade kofar tashiga. Amaan da Amrin suka dago suna kallon ikon Allah. Tafi minti biyu rike da kwankwsso suna kallon juna. Amrin taga abin nata bana wasa bane tacigaba da basa custard dinsa. Alokacin hamlat takuma tunzura tace"wai wannan irin rashin hankali ne zakazo kucikamin gida sannan kuma ina jiranki ki kawomin abincina shiru. Dasaury amrin tamike tare da cewa"wai ke wace irin dabbace? Sannan kuma ance miki ni yar aikin kice?. Hamlat tace"kutt alallai yar matsiyata ansamu waje". Amrin tace"hmm wallahi ni tausayima kike bani domin halinki zai kaiki ga halak amman bakome kicigaba". Sai alokacin Amaaan yayi magana yace"amrin kinga daukomin key din chan mufita". Amrin tace"ok bloodly". Hamlat tayi wata kara.