KUCHAKAR KISHIYA

Page 18

by @xayyeesherthulhumaerath

Sai da Amaan ya firgita tare da Amrin afirgice suka mike. Hamlat takama kugu tare da fadin"wallau ba inda zakuje ku barni agidannan ai ba me gadi bace nj". Amrin tayi dogon tsaki sannan tabangaje hamlat taja hannun Amaaan suka fita. Agurin hamlat ta tsaya tanata zabga uban masifa. Suko suna fita Amrin tace"ina zamu bloodly?. Sai da Amaaan yayi murmushi sannan yace"layin zana". Amrin tace"bloodly? Me ya hadamu da layin zana kuma? Amaaan yakara murmushi sannan yace"kedai muje kyaganema idonki". Amrin ce me tuka motar sai sakye-sakye take azuciyarta ko ina dasu oho. Sunzo daidai wani gida me kama dana laka gashi kuntu sai kuwa Amaan yace"tsaya anan bloodly". Amrin da mamakinta tanemi waje tayi paking. Adai-dai lokacin sai ga ahlam ta bullo da uniform ajikin ta tana dan tsalle-tsalle . Amaan yabada hankalinsa ga ahlam hakan yasa itama Amrin ta bada nata. Aikuwa ahlam nadan tsalle-tsallenta sai ta hango me rake. Tanufi gunsa tace",me rake abani naa biyar". Me rake yace"babu na biyar yar nan". Ahlam tace"kut gashi ina gani fa". Me rake yamata shiru . Aikuwa tuni tafara waka. Tana cewa" *me rake, inba rake, mutuwa tazo, ta tafi dakai*". Dahike me raken tsohune ai tuni ya firgita yace"haba yar nan aai akwai rake kyauta ma zan baki ba sai kin ban biyar ba amman fa karki kara cewa mutuwa tazo ta tafi dani". Ahlam tayi dariya sannan tace"to baba me jiran duniya bani intafi zanje islamiya". Sai da merake yasamo lukyekyen ciki dan dari biyu yace"gashi toh". Ahlam nakarba tazura da gudu tana cewa"wallahi sai kamutu baba ai kowa ma zai mutu hhhhh wallahi zaka mutu ". Aituni baba me rake yasoma kuka shi adole bayason mutuwa. Hawaye nabin hawaye. Ahlam data juyo taga yana kuka sai yabata tausayi. Tazo tashare masa hawaye tace"sory baba bazaka mutu ba to daman fa wasaa nakema". Me rake yayi murmushi . Ahlam tace"to kasamin albarka" Me rake yace"Allah yamiki albarka yar nan". Ahlam tayi murmushi sannan tace"amin tacigaba d tafiyarta". Amrin sai dariya take haka kawai sai taji yarinyar tashige mata rai. Amaan yace"amrin wallahi inason yar nan fiye da yadda nakeson kaai nah". Amrin tace"nima inasonta wallahi yayana". Suna cikin maganar nab ahlam har tazo zata shige gida kawai sai ta hango su amaaan na lekyenta. Ta tawo da gudu