Page 22
amaaan yace"to fa antabo me jiran kadan kinga ni kam muje insanar da dady domin,nasan inta riga fada toh da matsala", amrin tace"owk hakane fa muje", suka nufi hanyar gida, hamlat taji ana buga kwofa dahike tasan kawartace dasaurin ta tafito aiko taga falo wayam azuciyarta tace"lallai mah gayannan wato tafiyarsu ma sukayi", tayi kwafa taje ta bude kwofar, maaamah naganinta tace"kut yanaga har kin rame wai meke faruwa neh haka?, hamlat tace"hmm muje muzauna tukun, dai", maamah tace"owk ", hamlat tace"kiga dan rainin hankalin nan wai aure yakeson yi fah ko,ince zai ma yi", maamah ta tashi afirgice tace"kanbala'iiiiii aiki wallahi bai isa ba yamasan ko mu suwaye kuwa?, hamlat tace"hmm ni duk ba wannan ba kifadamin mafita", maamah tace"kinsan gidan su yarinyar neh? toh ma wai yar wani hamshakin ce da zasu kara damu", hamlat tace"wallahi bansan yar waye ba? maamah tace"owk yakamata musan yar waye amman kafin,nan zamuje gun wani hatsabibin boka wanda asanda mukaje zai mana aiki", hamlat takama bqki sannan tace"boka fa kikace?, kinsan duk abuna banason shirka ko?, maaamah tace"toh shikennan zauna amiki kishiyar ninayi gaba sai munzo shan biki da suna dama gashi ke ba haihuwa kike ba", tuni hamlat ta fara kuka tana rukwo maaamah"dan allah kitsaya ni muje ma ko gun waye wallahi zani indai za afasa auren nan", maamah tayi murmushi tace"ko kefa aminiyar", azuciyarta kuwa cewa take"banza ballagaza kuchakar da batasan metake ba sai na hallakar dake insha allah tunda dai ke son duniya kikasa agaba ai abinda nake nema kenan muzama daya", hamlat ta taba maaamah tace"baran dauko gyale da jaka mutafi ", maaamah tayi murmushi tace"toh kiyi sauri muyi muje dai kam", amaan da amrin suna shiga gida sukayi shashin mumy na ganinsu tafara harare2 suko suka gesheta suka nufi dakin dady, suna zuwa suka sami dady azaune yana karanta jarida dahike yau weekend ne , dady naganinsu yafara murmushi atake suka durkusa suka geshesa ya amsa cike da farinciki, dady yace"son meke tafe dakune tare da yar auta tah", amaan yafara murmushi yana sosa kyeya , dady yace"toh fa ke yar auta fadamin", amrin tayi murmushi tana wasa da yan yatsunta tace"uhymm,dady yayane yakeson yakara aure", dady yace"masha allah amman gaskiya naji dadin wannan maganar son allah yama albarka ,yar waye kuma a ina suke,?, amaan yace"babanta ba kowA bane alayin zana ma suke da zama", dady yace"owk to nasan dai baku fadawa babban yaya ba ,amman karku damu zan masa magana sai muje gidansu yarinyar ayi bincike,