KUCHAKAR KISHIYA

Page 24

by @xayyeesherthulhumaerath

bayan baba yashiga gidane yasanar da baba abinda bakinsa suke bukata, baba tayi shiru domin ko kadan batason abinda zai rabasu da ahlam, baba yace"nafisa nasan me kike tunani domin ba abu me wasa bane rabuwar mu da ahlam toh amman,in hakan ne alkairy ya muka iya,", baba taja dogon,numfashi tace"toh allah yazabq mana mafi alkairi", baba yace"amin kinga yanzu sai insanar da yaya ko inzasu kara zuwa sai suyi magana dasu"-, baba tace"hakan ma yayi", suna cikin,maganar,sai,ga ahlam tashigo da gudu , baba yace"lafiya ?, ahlam tace"uhumm yau anbamu hutu neh fa kuma ninazo ta daya", baba tace"wow,masha allah yar albarka sannu", ahlam tace"baba kasan me nakeso ka siyomin?, baba yace"aa yata", ahlam tace"yar bebi nakeso", baba yace"laa ahakan kikeso anace miki aunty kina wasa da yar bebi ke kam dai bazaki girma ba ahlam ", ahlam tace"uhumm nifa babbace kuma manya ma nawasa ai ", baba yace"toh shikenan", ,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,, hamlat da maama suka nufi wajen boka , suka sanar dashi,abinda ke tafe dasu aiko boka yasanar dasu cewa wannan yar tafi karfinsu,kuma yar talakawace sose,amman ba abinda suka isa su mata sai,dai,subita hanyar muzguna musu", maamah tace,"bakome sun gode kuma sunada hanyoyi,kala-kala ", suna fita maamah tace"kinga talakawane inmukaje muka wulakantasu zasu ce,sun fasa", hamlat tace"yauwa dama ninafison hakan", maamah tace"amman kifara nemomana adress din gidansu tukun", hqmlat tace"wannan ba kome bane", ahaka suka rabu,

washe gari,

da safe amaan natashi bayan yayi wanka ko break bai yi domin dama basaba masa akayi ba inba amrjn ce tazo ba ,yanufi gidansu ahlam, ashe hamlat na biye dashi,abaya, yana zuwa dai-dai kwofar gidan yayi paking aiko sai ga ahlam tafito,zata tafi,skul, yana ganinta yace"morning auntynah", ahlam tayi murmushi sannan tace"morning kaninah", saj ga baba yafito yana ahlam,muyi sauri karki makara fa, amaan ya durkusa yageshe da baba sannan yace"baba kabari kawai zan kai ta", baba yace "toh shikenan allah yayi maka albarka", ahlam aka shiga gaban mota aka harde kafa, sunfara tafiya kowa dai yayi shiru , amaan yace"aunty ahlam kina sona?, ahlam tayi sauri ta rufe,fuska, sannan tace"tab kai fa kanina ne sai dai yayanka", amaan ya kyalkyale da dariya sannan yace"toh kinason yayan nawa?, ahlam tace"eh mana indai kamar ku daya, amaan yace"toh shikenan aunty matar yayanah,yanzu kullum zanna zuwa inkaiki skul kuma indauko ki", ahlam,tace"toh kanina nagode ka geshemin da yayanka", amaan yayi murmushi sannan yabude mata kwofa tafito, karaf a idon,uncle salim, ai tuni,zuciyarsa tafara bugawa,