Page 26
mumy na gama magana da ahlam tayi waje , inda ta tadda dady,afalo alamar dai yanzu tashigo ko kulasa batayi ba tayi,waje inda ta,nufi bangarensu amrin, tana zuwa ko sallama babu, baba da mama kawai ganinta suka agabansu kaman anjefo ta da hike hakan ba sabo bane agaresu ko damuwa basu yi ba, mama ce tace"sannu hajiya", mumy ta galla mata harara sannan tace"aiki kikaga inayi da zakimin sannu?, wato,ku kuna nan kuna hutunku dan son zuciya kunsa danku yakara aure,wai ma dukiyar da kuke kwashewan bai isa haka bane?, iyeee?, wato sai kun gama kwashe kome,ko ?, baba yace"ke salma kinsan dai dagani har mata ta ba sa,o,inki bane ko?, ba wai kinga muna miki kawaici akan duk abinda kike mana yasa zaki samu damar ci mana mutunci ba,kuma maganar dukiya dakike ta dan uwana ce dan haka nafi ki mulki da ita", mumy,tace"ohhh matsiyata ansamu waje,har ansamu bakin magana", mama tace"kiyi hakuri kibar mana daki,kuma aure ne insha allah sai dan mu yayi domin samun kwanciyar hankalinsa data mu", mumy tayi wata kara sannan tace"wallahi baku isa ba indai kudi na aiki dan ku bai isa yakarawa yata,kishiya ba gwara ya mutu kowa ya huta", baba yace"ta allah ba taki ba salma bakisa ki kashe mana da ba in kwanan sa bai kare ba dan haka barmin daki kije chan ki karata", mumy tayi wata dariyar mugunta tace"toh me tawakkali,mu zuba mugani", sannan ta fita tana cigaba da dariyar mugunta, ,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,,, hamlat sungama kintsa muguntarsu ita da maamah , sannan ta nufi office, tana zuwa ta tarar da amaan nasauri zai fita, ta kallesa ta gallah masa harara sannan tace"to za,aje gun matsiyata yan uwan matsiyata kenan", amaan ya kalleta yayi murmushi yace"hakane fa yar masu dukiya kuma uwar gida agun matsiyaci angon matsiyata,", ya kalleta ya kara da murmushi sannan yaci gaba da tafiyarsa, agurin hamlat ta kame domin tunda take arayuwarta,amaan bai taba fada mata magana irin haka ba duk tsiya tasan yana hakuri da ita, domin kome zata mesa sai dai ya kalleta ya mata murmushi kawai yayi gaba amman wai yau har amaan yafara mai da martani,,,, azuciyar ta tace"kut lallai matsiyatan nan sun gama da amaan amman bakome zasu sha mamaki, tashiga office dinta. amaaan kuwa yatafi yana farin ciki domin zai je yadauko masoyiyarsa amakaranta